Tarihin kamfanin Apple Inc.

Apple, kamfanin fasaha ne na kasar amurka wanda ya ke da hadaka da wasu kasashe, kuma cibiyarsa ta na zaune a Cupertino, da ke jahar California. Apple dai kamfani ne wanda ya ke ginawa tare da tsara kayan lantarki, da na'urorin zamani, da manhajojin computer, da na wayoyin hannu, da sauran aiyuka a yanar-gizo (online services).

Sanannun na'urorin kamfanin Apple

Kamfanin Apple ya kera na'urorin da ake iya gani kuma a tabasu (hardware) wanda su ka hada da babbar wayar iPhone, da na'urar iPad tablet, da na'ura mai kwakwalwa ta Mac, da na'urar iPod portable media player, da agogon hannu na Apple wato Apple smartwatch, da talabijin din Apple wato Apple TV, da AirPods wireless (earpiece mara waya), da sifikar girke wanda aka fi sani da HomePod smart da sauransu.

Manhajojin Apple (software) sun hada da macOS, da iOS, iPadOS, da watchOS, da kuma tvOS operating systems, da iTunes media player, da manhajar shiga internet wato Safari web browser, da fingerprint wanda ake kira Shazam acoustic fingerprint utility, da kuma su iLife, da iWork kirkira da aiki, tare da shahararrun manhajoji kaman Xcode, da Final Cut Pro, da kuma Logic Pro.

Aiyukansu na online (wato online service) kuma sun hada da rumbun kade-kade na iTunes, da rumbun manhajoji da wasanni iOS App Store, da rumbun manhajojin na'urar Mac wato Mac App Store, da rumbun kade-kade na Apple Music, da Apple TV+, tare da iMessage, da kuma iCloud, sauran su ne Genius Bar, da Apple Card, da AppleCare, da Apple Pay, da Apple Pay Cash, da kuma Apple Store da sauransu.

Yaushe aka kafa kamfanin Apple?

Steve Jobs, da Steve Wozniak, da Ronald Wayne su ne su ka kafa Apple a watan Afrilu na shekarar 1976 (April 1976) domin ginawa da siyar da na'urar Wozniak's Apple I personal computer, ko da ya ke Ronald Wayne ya siyar da kasonsa a kwanaki 12 daga baya. Kamfanin ya samu hadakar zama a matsayin kamfanin na'ura wato Apple Computer Inc. a watan Janeru na shekarar 1977 (January 1977), sannan ya siyar da na'urorinsa masu kwakwalwa wanda su ka hada da Apple II. Bayan habakar kamfanin Apple a cikin shekaru kadan, Steve Jobs da Wozniak sun dakko hayan kwararrun ma'aikatan na'ura mai kwakwalwa wadanda su ka kware a fagen kerawa da tsara na'ura mai kwakwalwa domin su tayasu aiki.

Kamfanin Apple ya shiga jama'a a shekarar 1980 domin nasarar samun kudi da ya cimma. Bayan wasu shekaru kadan Apple ya matsa gaba ta hanyar kirkiro sabbin na'urori masu kwakwalwa (computers), kaman Macintosh a shekarar 1984, da tallace tallacen hajojin da ya karba wadanda su ka yadu a gurare da dama.

A yau kamfanin Apple Inc. ya zama gagara gasa duba yanda ya samu habaka, sannan kuma hajojinsa sun samu aminci da karbuwa a wajen al'ummar duniya. Domin shine kamfanin da wayoyinsa tare da na'urorinsa masu kwakwalwa su ka fi na kowane kamfani tsada.

Shin ko ka san bambancin da ke tsakanin wayar iPhone (iOS) da Android (OS)?

Wayoyin kamfanin Apple su na da tsada fiye da wayoyin sauran kamfanonin. Saboda haka ake cewa wayoyin iPhone da iPad sai 'yan boko ne su ke iya rikesu ko amfani da su. Za mu dakata a nan, sai kuma mun hadu a wani darasin fasaha a gaba.

Mu na fatan a na amfanuwa da darusan fasaha da ake karantawa a shafin nan. Sannan ku na iya rarraba wannan bayanan ga abokanku a shafukan sada zumunta da muhawara na internet.

Sannan duk wanda ya ke da tambaya, sai ya yi kasa wajen comment, ya rubuta, zai samu amsa insha Allahu. Mu na godiya akan ziyarar da kuke kawowa shafin nan, da fatan za mu sake ganinku, a huta lafiya. Mun samo wadannan bayanan daga shafin Wikipedia.

1 comment:

  1. Kamfanin apple sun taba qera mutum-mutumi, sannan suna qera drone?

    Tnks

    ReplyDelete

Powered by Blogger.