Yanda Ake Install Na Application A Wayar Android

Android wayace wanda kamfanin Google suke gina asalin manhajarta wato OS. Wannan manhaja ita ce kanwa uwar gami wajen tafiyar da wayar Android. Shiyasa su kamfanin Google suka saka wata doka ko ka'ida wanda mutum sai ya bi sannan zai iya tafiyar da wayarsa a saukake.

A lokacin da wayar Android take sabuwa za ka samu cewa bata bude duk application din da ba a PlayStore aka dakkoshi ba. Wannan yana faruwane saboda su Google din basu bayarda lasisi ga wannan application din ba. A bisa tsari da doka duk wani application ko game da ka gani a PlayStore yana da lasisi, sannan kuma ba ya dauke da wata cutarwa ga waya. Domin kafin a daurashi a PlayStore sai an tantance shi cewa lafiya kalau yake.

Shin kasan yanda ake dawo da abubuwan da aka goge a wayar Android?

Dalilin da yasa suke haka watakila saboda dalilan kare fasahane, da kuma samun kudin shiga. Duk wanda zai daura application ko game sai ya biya kudi akalla dalar Amurka ashirin da biyar ($25) - kenan akwai dalilai na neman kudi, tare da kare fasaha da sauransu.

Saboda yawan application na Android, ana iya samun wasu application da suke da matsaloli da kuma cutarwa ga waya a PlayStore. Duk dacewa suna da illoli ga waya, amma an basu lasisin zama a cikin a PlayStore. Sai dai idan Google suka gano hakan sukan goge irin wadannan application din sannan su gargadi wanda ya daurasu, ko kuma su kulle masa account.

Bawai kowane application bane wanda baya cikin PlayStore yake da illa ga waya ba. Akwai shafuka masu yawa wadanda ake samun lafiyaiyun application wadanda ba su da matsala ko kada. Wadannan amintattun shafukan sune kaman Apkpure.com da makamantansu.

Yanzu dai bari muyi abun da yasa muka tsara tare da wallafa post din nan, wato nuna yanda ake install na application a wayar Android. Da farko, idan ka zo za ka yi install na application a wayarka, za ka ga wayar ta gargade ka cewa wannan application din zai iya zama illa ga wayarka, ko kuma zai iya yi wa wayarka illa. Alhali kuma application din bashi da wata matsala ko kadan.

Yana da kyau, ya kasance kana saukar da application a shafukan da suke amintattu kamansu Apkure, da Aptoide, da Uptodown da makamantansu. Wadannan shafukan da muka kawo an sansu a duniya wajen samun application da game amintattu kuma tsaftatattu na Android. Shiyasa suka samu aminci a wajen jama'a.

Shin ka iya canza background na hoto a wayar ka ta Android? Shin ba ka iya ba, kuma kana son ka koya? To yi sauri ka shiga nan domin ka koya.

Domin saukar da application ko game a PlayStore da wayar Android, dole sai mutum yana da Google mail, kuma yana amfani dashi akan wayarsa. Idan kuma mutum ba shi da Google mail ba zai iya samun daman shiga PlayStore ba, ballema ya saukar da wani abu acan. Hasalima wasu bangarori a wayar Android, kaman su PlayStore, basa aiki har sai mutun ya yi Log in na Google mail nashi a wayarsa. Sannan ya samu daman amfana da irin wadancan bangarorin. Yanzu dai ku yi kasa ku ci gaba da karatu kawai!

Ga Yanda Akeyi
1. Da farko, ka saukar da wani application a daya daga cikin website din da mu ka yi misali da su a sama. Amma banda PlayStore, ko kuma ka tura application din ta Xender ko Bluetooth. Idan ka tura ko ka saukar da application a wayarka, sai kaje wajen da application din yake, ka bude shi. Kana tabashi za ka ga an rubuta For your security, your phone is not allowed to install unknown app from this source. Sai ka sharesu, kawai ka shiga inda aka rubuta SETTINGS.


2. Kana shiga SETTINGS din za ka ga wajen Install unknown apps. Ka duba gaba da inda aka rubuta Allow from this, za ka ga wajen a rufe.


3. Wannan wajen da yake rufe, shi za ka bude. Domin bude sai ka taba wajen - kana taba wajen za ka ga ya bude.


4. Kana bude wajen, sai ka dawo baya, ka sake taba application din, za ka ga wayar ta rubuta maka Do you want to install this application? It does not require any special access. Sai ka taba inda aka rubuta INSTALL, yana daga kasa ta bangaren dama.


5 Kana yin haka wayar za ta fara install na application din, sai ka jira ta gama install na shi.


6. Wayar tana gama install na application din za ka ga ta rubuta maka App installed. Idan ka duba daga can kasa za ka ga an rubuta DONE da OPEN. Sai ka shiga OPEN domin bude application din, sai ka yi aikinka da shi. Idan kuma baza ka yi aiki dashi a yanzu ba, sai ka taba DONE.


Kana yin haka shikenan ka gama install na application a wayarka. Wannan hanya za ka bi idan za ka yi install na kowane irin application a wayarka ta Android. Idan kuma tsarin wayarka ba haka yake ba, sai kayi kasa ka duba daya matakin.

Kafin mu yi nisa a mataki na biyu, ka je wajen application din ka tabashi, kaman za ka yi install nashi. za ka ga wayar ta rubuta maka Install blocked, kuma ta rubuta cewa "For security, your phone is set to block installation of apps obtained from unknown sources".


Shi kana so ka koyi yanda zaka bude WhatsApp da kan ka a wayarka ta Android? Ko kuma dai WhatsApp naka ya yi expire, ya dena aiki, kuma kana so ka sabunta shi? Shiga nan, domin karanta bayanin da mu kayi akan yanda zakayi komai da kan ka cikin sauki.

Mataki Na Biyu
1. Da farko, ka je, ka shiga SETTINGS na wayarka. Sai kayi kasa wajen PERSONAL, ka shiga Security.


2. Kana shiga Security, sai ka yi kasa kadan za ka ga Device administration, kasa dashi kadan za ka ga inda aka rubuta Unknown sources, shidinma kasa dashi an rubuta "Allow installation of apps from sources other than the Playstore" kusa da rubutun kuma akwai wani dan karamin box, kawai sai kayi tick nashi.


3. Kana yin tick na wannan box din nan take zai nuna maka wasu bayanai, kawai sai ka taba Ok.


4. Daga nan kuma za ka ga wannan box din anyi tick nashi, shikenan an gama komai! ;)


5. Yanzu kuma, sai ka je ka gwada install na wani game ko application din da kake so - wanda ba a PlayStore ka dakko shi ba, za ka ga wayar ta fara install na application babu wata matsala.


Daman tsarin nan haka yake a duk wata wayar Android, kuma a haka take zuwa. Amma kana setawa kaman yanda muka nuna a wannan tutorial din shikenan ka magance matsalar.

Saukar da wasan game din Zuma Revenge kyauta a wayar ka ta Android.

Nan shine karshen wannan tutorial din sai kuma a gaba idan mun zo da wasu bayanan. Muna fatan wadannan darusan suna amfanarku ta hanyoyi daban daban.

Kuna iya tambayar duk abun da ku ka ga ba ku gane ba a wajen comment dake kasa, mun gode!

2 comments:

  1. Wow thats extremely wonderful I actually have detected a brand new app camsurf apk this app is nice and that i have started gazing it.Thanks for the assistance and suggesting the matter i'll travel with it.Keep publication and writing new article.

    ReplyDelete

Powered by Blogger.