Yanda ake seta theme da font a keyboard din wayar Android

A darasin da ya gabata mun nuna yanda ake seta keyboard a wayar Android - sannan kuma mun ce zamu ci gaba da sauran bayanan a darasi na gaba wato a darasin nan. A wannan darasin zamu yi kokarin cika wancan alkawarin da mu ka dauka, na yin bayani akan yanda ake seta su theme, da font, da sound, da kuma a jiye kalma a cikin dictionary.

Idan ka seta theme a keyboard din, za ka ga keyboard na wayarka ya kara yin kyau sosai. Idan kuma ka canza font za ka ga salon rubutu a jikin keyboard na wayarka ya canza, ya koma mai kyau. Idan kuma ka seta sound wanda kake so wannan ma zai kara kayarta da keyboard na wayartaka. Domin lokacin da kake amfani da shi za kana jin wani sauti kaman kana rubutu da typewriter ta gargajiya.

Idan kuma ka ajiye kalma a cikin dictionary, hakan zai rage maka wahala lokacin da kake rubutu. Misali, idan kalma tanada harufa masu yawa, inde ka ajiyeta a cikin dictionary, lokacin da kake rubutu kana saka kalmomi guda uku na farkon wannan kalmar za ka ga kalmar gaba dayanta ta baiyana. Kaga wannan ai zai rage maka wahala wajen rubutu.

Ga yanda ake seta theme

1. Kafin mu yi nisa a cikin tutorial din - ka da a manta a darasin baya mun nuna yanda ake saka keyboard a wayar Android cikin sauki. Kuma bayanin yayi nisa a wancan darasin, sai mu ka dakata - saboda haka za mu ci gaba da bayani daga inda muka tsaya. Bayan ka shigo cikin keyboard din za ka ga Theme, da Font, da kuma Sound daga sama ta bangaren hannunka na hagu. Sai ka shiga Theme.


2. Kana shiga Theme za ka ga keyboard din ya nuno maka theme na zuwan keyboard din. Theme din sune Default wato theme na zuwa wanda yake aiki a keyboard din, sai Concise, sai Brazil, sai Green, sai Gorgeous, sai Mars, sai Blue Sky, sannan sai Red daga karshe kuma akwai Spring. Kuma idan kun lura za ku ga an yi maki akan theme mai suna Default, wato shine yake aiki a keyboard din a lokacin.




3. Za mu canza Default theme, mu saka wani theme na daban. Za mu yi misali da theme mai suna Brazil. Idan ka shigo cikin Theme sai ka yi kasa ka je kan theme din da kake so ka seta a matsayin wanda za ka yi aiki da shi. Kana zuwa dai dai kan theme din sai ka taba shi. Kana taba shi za ka ga wani maki ya futo akansa. Idan kuma wadannan theme din da suke zuwa a cikin keyboard din ba su yi maka kyau ba, ka duba daga sama za ka ga inda aka rubuta Online. Sai ka shiga wajen ka saukar da wasu, idan kanada data. Ko kuma ka shiga Custom idan kana so kayi amfani da hotunan cikin wayarka a matsayin theme na keyboard din.


4. Kana taba kan theme din shikenan, ka seta theme a keyboard na wayarka. Za mu iya ganin yanda kalan theme din yake a hoton da ke kasa.


Sannan kuma keyboard din yana da Emoji ko Emoticons - wato wasu kananun hotuna ko alamu da ake amfani da su a cikin rubutu domin a nuna hali ko yanayin abun da akayi rubuta akansa yake ciki.


Bayan mun gama seta theme, aiki na gaba da za mu yi shine mu seta salon rubutu wato font. Ka yi kasa ka ci gaba da karatu domin ganin bayanin canza yanda ake ganin rubutu a jikin keyboard na Android.

Ga Yanda Ake Seta Font
1. Bayan ka gama seta Theme, sai ka dawo baya, ka shiga inda aka rubuta Font, wanda yake kasa da Theme.


2. Kana shiga Font za ka ga inda aka rubuta Local, daga gefensa kuma an rubuta Online. Idan font na zuwan keyboard din basu burgeka ba, ko kuma kana so ka saukar da wasu a internet, sai ka shiga Online, ka saukar da wasu. Idan kuma za ka yi amfani da na zuwan keyboard din sai ka dawo karkashin Local za ka ga wasu font guda hudu. Kuma sune Default, da CaviarDreams, da Pacifico, sai kuma Windsong.


3. Za mu canza font na zuwa mu saka wani daban. Za mu yi misali da font mai suna Pacifico. Kana shigowa cikin Font sai ka je, ka taba kan font din da kake so ka seta a matsayin font na keyboard naka. Kana taba kan keyboard din za ka ga wani maki ya futo akansa.


4. Kana yin haka za ka ga style na yanda keyboard din yake nuna rubutunsa ya canza. Bari mu ga yanda font din yake bayan an canzashi.


Font din da mu ka seta bawai system font mu ka canzawa ba. Iya salon rubutun cikin keyboard din ne kawai ya ke canzawa - wato ko da ka canza keyboard din, idan kayi rubutu za ka ga rubutun bai canza ba a cikin wayarka, a jikin keyboard dinne kawai yake canzawa. Aiki na gaba kuma shine seta sound wato sautin keyboard din lokacin da kake rubutu dashi - wato lokacin da kake rubutu dashi za ka ji wata kara kaman kana amfani da abun rubutu na gargajiya.

Ga Yanda Ake Seta Sound
1. Bayan ka gama seta keyboard din. Sai ka dawo baya ka shiga Sound, wanda yake kasa da Font.


2. Kana shiga cikin Sound - za ka ga sound kala kala kaman su Typewriter, da Gun, da Cup, da Piano, da Silencing shot, da Tuner, da Ring1, da Rubber duck, daga karshe kuma sai Ring2.




3. Yanda za ka seta karar da za ka ji lokacin da kake rubutu, kana shigowa cikin Sound, sai ka taba kan sound din da kake so. Za mu yi misali da sound mai suna Typewriter, wato sautin abun rubutu na gargajiya.


Bayan an gama seta sound, aiki na gaba kuma karshe da za mu yi, shine, mu saka wata kalma cikin a dictionary. Kana gama seta sound, ka duba daga can sama ka taba alaman gear ko settings da take can sama ta bangaren dama.

Ga Yanda Ake Saka Kalma A Cikin Keyboard
1. Bayan ka gama seta sound na keyboard din, sai ka duba daga can sama ka taba icon din gear. Kana tabashi za ka ga ya kawo ka cikin Settings na keyboard din. Ka lura daga can sama za ka ga an rubuta Emoji keyboard, a kasa kuma za ka ga Auto-capitalization, da Vibrate on keypress, da Sound on keypress su ukun duk anyi tick nasu.


2. Sai kayi kasa, ka shiga Personal dictionary.


3. Kana shiga Personal dictionary za ka samu wajen babu komai. Idan kuma ka taba ajiye wata kalma za ka sameta a wajen. Sai ka duba daga can kasa a tsakiya ka taba icon din nan mai kaman plus wato +.


4. Kana shiga wajen sai ka rubuta asalin kalmar gaba dayanta, misali ka rubuta gaisuwa. Sai ka shiga wajen shortcut ka rubuta harufa uku ko hudu na farkon kalmar. Misali na rubuta gaisuwa, harufa uku na farkonta sune gai. Kana rubuta kalmar da shortcut nata, sai ka taba inda keyboard din zai bace.


5. Kana taba wajen da keyboard din zai bace, nan take keyboard din zai bace. Yana bacewa ka duba daga kasa za ka ga alaman plus wato + sai ka tabata.


Kana yin haka shikenan ka ajiye kalma a cikin dictionary na keyboard din. Idan kazo yin rubutu, kana rubuta harufa uku na farkon wannan kalmar za ka ga gaba daya kalmar ta baiyana. Bayan ka gama ajiye kalmar sai ka dawo baya za ka ga kalmar da ka ajiye.


Kana yin haka shikenan, ka gama komai. Bari muga yanda abun yake aiki.


Haka za ka yi idan zaka seta keyboard a wayarka ta Android. Hanyoyin da muka nuna basu da wahala, suna da matukar sauki. Bayanin gaba daya mun yi shine a darusa biyu wato na farko da kuma wannan na biyun kuma na karshe.

Nan shine karshen darusa biyun. Da fatan ana amfanuwa da tutorial din da muke wallafawa. Idan kunada tambaya akan abun da baku gane ba, kuna iya shiga wajen comment ku rubuta mana tambayoyinku, ko kuma yin sharhi game da abun da mu ka rubuta.

Ku gaiyato mana abokanku domin suma su zo su karanta rubuce rubucen da mukeyi a shafin nan. Daga karshe kuma muna godiya akan ziyarar da kuke kawo mana a shafin nan - da fatan za mu sake ganin ku.

A huta lafiya, mun gode!

No comments

Powered by Blogger.