Yanda ake aiki da Linear Algebra

Ina dalibai musamman daliban lissafi da kimiyya ga wani application wanda zai taimaka wajen rage muku wahalar lissafi. Linear algebra application ne na lissafi, ba kaman photomath ya ke ba, cikinsa akwai zane da fomulaloli wadanda ake amfani da su wajen gano area, ko volume, ko perimeter. A cikin wannan application din akwai fomuloli wadanda aka tsarasu tare da calculator.

Saukar da Linear algebra
1. Linear algebra ga masu Android.
2. Linear algebra ga masu iPhone da iPad.

Ga yanda ake aiki da Linear algebra
1. Da farko, ka fara saukar da application din a link din da mu ka bayar a sama, sai ka yi install din sa. Bayan ka gama install din sa sai ka budeshi, ka na budeshi za ka ga Matrices, da Linear Equation, da Vector Space, da kuma Geometry a karshe.


2. Daga nan sai ka shiga wajen da ya ke da alaka da aikin lissafin da za ka yi, misali, ka shiga Metrices.


Ka na shiga za ka ga abubuwan da su ke cikinsa kaman haka:
Addition of Metrix
Subtraction of Metrix
Metrix Multiplication
Transpose of Metrix
Trace of Matrix
Determination of Matrix

3. Bayan ka gama ganinsu sai ka shiga wanda za ka yi aiki dashi. Idan ka gama, sai ka dawo baya, ka shiga Vector Space.


Ka na shiga za ka ga abubuwan da su ke cikinsa kaman haka:
Addition of Vector
Subtraction of Vector
Scalar Product
Projection
Vectorial Product
Angle Between the Scalar Product
Orthogonal

4. Bayan ka gama ganinsu sai ka shiga wanda za ka yi aiki dashi. Idan ka gama, sai ka dawo baya, ka shiga Linear Equation.


Ka na shiga za ka ga abubuwan da su ke cikinsa kaman haka:
Gaussian Jordan Method
Gaussian Elimination

5. Bayan ka gama ganinsu sai ka shiga wanda za ka yi aiki dashi. Idan ka gama, sai ka dawo baya, ka shiga Geometry.


Ka na shiga za ka ga abubuwan da su ke cikinsa kaman haka:
Cone
Cylinder
Isosceles Triangle
Square
Sphere
Rectangle
Rhombus
Parallelogram
Trapezoid

6. Za mu yi misali da Geometry. Geometry darasine wanda a cikinsa ake auna tsayi da kuma fadi sannan a gano area, ko volume ko perimeter na wannan siffa. Kaman yanda ake iya gani a hotunan da su ke kasa za mu lissafa area da perimeter din isosceles triangle, da square, da kuma rectangle. Kuma za mu yi amfani da santimita (centimetre) saboda abubuwan tsayinsu bai kai mita (metre) ba.

7. Ga hoton Isosceles triangle da tsayinsa tare da fadinsa, a zanen nan isosceles triangle din yana da tsayin santimita biyar (5cm) kuma fadinsa ta kasa (base) fadin santimita ukune (3cm).


Sai kuma Square wato zanen da yake da bangarori hudu da kusurwa hudu, sannan kuma duk tsayinsu daya. Dole fadinda da tsayinsa su zama daidai, idan tsayin abu ya fi fadinsa yawa to ba square bane, sai dai a kirashi rectangle. Anan square tanada tsayin santimita hudu (4cm).


Sannan na ukunsu wato Rectangle. Shi kuma rectangle yana kama da square sosai. Sai dai bambancinsu shine rectangle dolene tsayi ko fadi daya ya fi dayan. Yayin da a square dolene fadin da tsayin su zama daya. Anan rectangle din yana da tsayin santimita uku (3cm) da kuma fadin santimita biyar (5cm).


8. Ga hoton isosceles triangle tare da fomulolin da ake amfani da su a lissafa area da perimeter.


Ga nan hoton lissafin isosceles triangle din da na yi a littafina.


Ga kuma sakamakon lissafin a application din.


9. Ga hoton square tare da fomulolin da ake amfani da su a lissafa area da perimeter.


Ga nan hoton lissafin isosceles triangle din da na yi a littafina.


Ga kuma sakamakon lissafin a application din.


10. Ga hoton reactangle tare da fomulolin da ake amfani da su a lissafa area da perimeter.


Ga nan hoton lissafin reactangle din da na yi a littafina.


Ga kuma sakamakon lissafin a application din.


Wadannan matakan ake bi idan za a yi aiki da wannan application din. Wannan kadan kenan daga cikin aiyukan da application din ya ke yi. Linear algebra ya na aiki da sauri kuma calculaton cikinsa ya na bayar da amsa daidai.

Bayan haka kuma application din nan akwai calculator a cikinsa wanda zai taimaka wa dalibi a lokacin yin lissafi. Akwai wasu application masu yawa domin dalibai a kowane fanni na ilimi. Za ka samesu mafi yawa kyauta ake saukar da su ayi amfani da su duk a kyauta.

Idan za ka yi aiki da wannan application din ka tabbata ka rubuta tambayarka yanda kowai zai ganewa ya fahinci tambayar.

Za mu dakata a nan sai kuma wani darasin. Amma kafin sannan ya kamata a sani Photomath application ne wanda ake amfani da shi ayi lissafi ta hanyar daukan hoton rubutu akan littafi, kuma ya na zuwa da calculator dan yin lissafi da kanka. Mun gode da kawo ziyara wannan shafin a huta lafiya! ;)

No comments

Powered by Blogger.