Yanda ake update din Google play service a wayar Android
Shin wayarka ta Android ta taba nunama cewa ta na bukatar ka yi update din Google play service? Ko ka san menene shi da kuma amfaninsa a wayarka ta Android? Domin samun amsoshin wadannan tambayoyin sai ka yi kasa, ka cigaba da karanta bayanin.
Misali, idan ka na so ka shiga Play store a wayar Android, ka na taba Play store din Google play service ne yake bude shi ka yi amfaninka da shi. Hakama idan za ka shiga application din YouTube ka yi kallo, Google play service ne yake budema shi. Idan kuma ya tsufa ya dena aiki ba zai iya budema wadannan application din ba, balle ma ka yi aiki da su.
Ko ka karanta bayanin yanda ake install din application a Play store?
Google mail kuma adreshin e-mail na kamfanin Google. Hanyace ta sadarwa wanda duk wani application na kamfanin Google sai da shi ake iya more shi - da gmail za ka samu daman shiga Play store ka dakko duk application da ka ke so a wayarka.
YouTube kuma bangare ne na bidiyo mallakin Google. Akwai application na iPhone da kuma na Android da aka tsara wadanda ake shiga YouTube da su a yi kallo. Wannan application ya na saukakawa mutane wajen amfani da YouTube.
Google drive wani bangarene na Google da ya ke ba da dama a ajiye abubuwa a cikinsa. Bayan wani lokaci idan kuma idan a na bukata sai a saukar da su a yi amfani da su. Wannan bangare ya na da mahimmaci sosai, domin duk dadewar da files za su yi a cikinsa ba sa lalacewa - ga kuma backup na WhatsApp.
Shin ko ka san yanda ake aiki da Google drive?
Google maps bangarene na Google dake baka daman ganin taswirar inda kake da sauran yankunan duniya a cikin wayarka ta iPhone ko Android. Wannan application din ya na da amfani musamman wajen gano gurare daban-daban da inda wani yake ta cikin taswira.
Wadannan application din idan Google play service ba ya aiki a wayarka to kai ma ba ka da daman shiga daya daga cikinsu balle ka yi aiki da shi. Akwai wata matsala da masu hada application (developers) su ke kira bug. Kalmar ‘bug’ kalmace ta turanci, wacce take nufin sunan wani karamin kwaro. Abun da su ke nufi da wannan kalman shine misali idan ka ajiye kayan abinci kaman wake ko masara ko shinkafa ko dai makamantansu - wadannan abubuwan da ka ajiye idan su kayi watanni a ajjiye ba a aiki da su, za ka ga kwari (insects) sun fara yawo akansu.
Wadannan kwarin dake yawo akan abubuwan da ka ajiye ya na nuna cewa wannan abubuwan sun jima a wajen a ajjiye ba a duba su ba - shi ya sa kwarin suka hau kansu. Hakama application idan suka dauki wani lokaci za ka ga sun tsufa, sai ace kayi update din su, misali kaman WhatsApp dake expire. Duk lokacin da ka ga application ya na bukatar ayi update din to kamfanin da ys hadashi ya sabunta wasu bangarori a cikinsa, ko kuma ya yi kwaskwarima a wani bangarensa.
Wannan matsalarce ke samun Google play services shi ya sa yake tsayawa ya dena aiki har sai an sabuntashi. To da ikon Allah a tutorial din nan zamu nuna yanda ake sabunta Google play service a wayar Android.
Kafin mu fara bayani ka je apkpure.com idan wayarka ba ta shiga Play store ka saukar da Google play service.
2. Ka na tabashi za ka ga ya kowa cikin Play store din daidai kan Google play service. Ya na nuna ma application din sai ka sake taba UPDATE.
3. Ka na tabawa zai nuna ma wasu bayanan application din kaman yanda suke nuna bayanan sauran application a Playstore. Sai ka duba kasa da bayanan za ka ga wajen ACCEPT sai ka tabashi.
4. Ka na tabawa za ka ga Google play service din ya fara updating.
5. Wayar ta na fara update din Google play service din sai ka jira ta gama. Idan ta gama update dinsa za ka ga da kansa ya fara install sai ka jira ya gama.
6. Ya na gama install din shikenan ka gama komai! Daga nan za ka ga Playstore din ya nuna ma Google play service - ya nuna ma application din sai ka taba OPEN.
7. Daga nan za ka ga komai ya dawo ya na aiki kaman yanda ya kamata. Bari mu shiga Play store din mu gani.
Idan akabi wadannan matakan da muka nuna za a magance matsalar da mu ka yi bayani a sama. Ya-na-da-kyau a sani cewa duk bayan tsawon wani lokaci ana bukatar ka yi update din Google play service a wayarka.
Sannan ya-na-da-kyau a duk lokacin da aka nuna ma wayarka ta na bukatan update dinsa sai kayi update din kawai ka huta. Gaba daya nauyinsa baikai 40MB ba, amma watakila nan gaba nauyinsa ya wuce haka saboda duk lokacin da aka sabuntashi wasu bangarori da tsaruka aka karamasa.
Za mu dakata a nan sai mun zo da wasu darusan a gaba. Da fatan ana amfanuwa da tutorial din da muke wallafawa a shafin nan. Mu na godiya, sai mun sake ganinku, ahuta lafiya!
Menene Google play service?
Google play service application ne na kamfanin Google wanda ya ke sadar da mutum da sauran application din Google da su ke cikin wayarsa ta Android. Application kaman Play store, da Google maps, da Google mail, da Google drive a wayar Android babu dama a shige su idan babu Google play service.Misali, idan ka na so ka shiga Play store a wayar Android, ka na taba Play store din Google play service ne yake bude shi ka yi amfaninka da shi. Hakama idan za ka shiga application din YouTube ka yi kallo, Google play service ne yake budema shi. Idan kuma ya tsufa ya dena aiki ba zai iya budema wadannan application din ba, balle ma ka yi aiki da su.
Amfanonin Google play service
Play store application ne dake zuwa a cikin kowace wayar Android. Kuma amfaninsa a wayar shine duk application din da ka ke bukata a wayar sai ka shiga cikinsa ka saukar da shi. Play store rumbune dake samarwa kamfanin Google kudaden shiga ta hanyar application din da ake daurawa a cikinsa - saboda duk wanda zai daura application a cikinsa sai ya biya kudi akalla dala ashirin da biyar ta America ($25).Ko ka karanta bayanin yanda ake install din application a Play store?
Google mail kuma adreshin e-mail na kamfanin Google. Hanyace ta sadarwa wanda duk wani application na kamfanin Google sai da shi ake iya more shi - da gmail za ka samu daman shiga Play store ka dakko duk application da ka ke so a wayarka.
YouTube kuma bangare ne na bidiyo mallakin Google. Akwai application na iPhone da kuma na Android da aka tsara wadanda ake shiga YouTube da su a yi kallo. Wannan application ya na saukakawa mutane wajen amfani da YouTube.
Google drive wani bangarene na Google da ya ke ba da dama a ajiye abubuwa a cikinsa. Bayan wani lokaci idan kuma idan a na bukata sai a saukar da su a yi amfani da su. Wannan bangare ya na da mahimmaci sosai, domin duk dadewar da files za su yi a cikinsa ba sa lalacewa - ga kuma backup na WhatsApp.
Shin ko ka san yanda ake aiki da Google drive?
Google maps bangarene na Google dake baka daman ganin taswirar inda kake da sauran yankunan duniya a cikin wayarka ta iPhone ko Android. Wannan application din ya na da amfani musamman wajen gano gurare daban-daban da inda wani yake ta cikin taswira.
Wadannan application din idan Google play service ba ya aiki a wayarka to kai ma ba ka da daman shiga daya daga cikinsu balle ka yi aiki da shi. Akwai wata matsala da masu hada application (developers) su ke kira bug. Kalmar ‘bug’ kalmace ta turanci, wacce take nufin sunan wani karamin kwaro. Abun da su ke nufi da wannan kalman shine misali idan ka ajiye kayan abinci kaman wake ko masara ko shinkafa ko dai makamantansu - wadannan abubuwan da ka ajiye idan su kayi watanni a ajjiye ba a aiki da su, za ka ga kwari (insects) sun fara yawo akansu.
Wadannan kwarin dake yawo akan abubuwan da ka ajiye ya na nuna cewa wannan abubuwan sun jima a wajen a ajjiye ba a duba su ba - shi ya sa kwarin suka hau kansu. Hakama application idan suka dauki wani lokaci za ka ga sun tsufa, sai ace kayi update din su, misali kaman WhatsApp dake expire. Duk lokacin da ka ga application ya na bukatar ayi update din to kamfanin da ys hadashi ya sabunta wasu bangarori a cikinsa, ko kuma ya yi kwaskwarima a wani bangarensa.
Wannan matsalarce ke samun Google play services shi ya sa yake tsayawa ya dena aiki har sai an sabuntashi. To da ikon Allah a tutorial din nan zamu nuna yanda ake sabunta Google play service a wayar Android.
Saukar da Google play service
1. Google play servicesKafin mu fara bayani ka je apkpure.com idan wayarka ba ta shiga Play store ka saukar da Google play service.
Ga yanda ake yi
1. Da farko, ka je Play store, ka yi searching din 'Google play service'. Idan kuma wayar ba ta bari ka bude Play store, ka na taba Play store din za ta rubuta ma “Play store won't run unless you update Google play service” - ma'ana Play store ba zai yi aikiba, har sai ka sabunta Google play service a wayar. Ta na rubuta ma haka, sai ka duba kasa da rubutun, ka taba inda aka rubuta UPDATE.2. Ka na tabashi za ka ga ya kowa cikin Play store din daidai kan Google play service. Ya na nuna ma application din sai ka sake taba UPDATE.
3. Ka na tabawa zai nuna ma wasu bayanan application din kaman yanda suke nuna bayanan sauran application a Playstore. Sai ka duba kasa da bayanan za ka ga wajen ACCEPT sai ka tabashi.
4. Ka na tabawa za ka ga Google play service din ya fara updating.
5. Wayar ta na fara update din Google play service din sai ka jira ta gama. Idan ta gama update dinsa za ka ga da kansa ya fara install sai ka jira ya gama.
6. Ya na gama install din shikenan ka gama komai! Daga nan za ka ga Playstore din ya nuna ma Google play service - ya nuna ma application din sai ka taba OPEN.
7. Daga nan za ka ga komai ya dawo ya na aiki kaman yanda ya kamata. Bari mu shiga Play store din mu gani.
Idan akabi wadannan matakan da muka nuna za a magance matsalar da mu ka yi bayani a sama. Ya-na-da-kyau a sani cewa duk bayan tsawon wani lokaci ana bukatar ka yi update din Google play service a wayarka.
Sannan ya-na-da-kyau a duk lokacin da aka nuna ma wayarka ta na bukatan update dinsa sai kayi update din kawai ka huta. Gaba daya nauyinsa baikai 40MB ba, amma watakila nan gaba nauyinsa ya wuce haka saboda duk lokacin da aka sabuntashi wasu bangarori da tsaruka aka karamasa.
Za mu dakata a nan sai mun zo da wasu darusan a gaba. Da fatan ana amfanuwa da tutorial din da muke wallafawa a shafin nan. Mu na godiya, sai mun sake ganinku, ahuta lafiya!
Leave a Comment