Yanda ake install din application ko game a Play store a wayar Android
Wayar Android ta na da rumbun manhajoji wanda ake samun application da gyama gyamanta a cikinsa. Wadannan abubuwa da ake samu a cikin rumbun wasanni ko kuma Play Store masu kyau da inganci ne, kuma an tsaresu, sannan abubuwa wadanda su ke da lasisi a kamfanin Google. Bayan rumbun wasa wanda ya ke zuwa a kowace wayar Android, akwai shafuka kaman apkpure.com da aptoide.com wadanda ake samun application na Android kyauta, kuma su din ma masu ingacine.
Install din application ko game a PlayStore ba wani abu mai wahala bane wanda za a ce sai an koyawa mutum. Abu ne mai sauki inde ka daura Google mail a wayar. Ba tare da wani bata lokaci ba, sai a yi kasa a ci gaba da karatu.
Ga yanda ake yi
1. Da farko, ka tabbata ka daura Google mail naka a wayar. Bayan ka daura Google mail din naka a wayar, sai ka je, ka shiga PlayStore. Ka na shiga za ka ga application da gyama gyamai a jere, sannan kuma daga can sama, za ka ga wajen search, an rubuta Search for apps & games.
2. Sai ka shiga wajen Search for apps & games din, ka rubuta sunan application ko game din da ka ke bukatar yin install din sa a wayarka. Za mu yi misali da application mai suna google drive.
3. Kana gama rubuta sunan za ka ga application ko game din da ka rubuta sunansa ya baiyana. Sai ka taba application din, ko kuma ka taba inda aka rubuta Install.
4. Kana taba Install din, za su nuna maka needs acces to sai ka taba inda aka rubuta ACCEPT.
5. Kana taba ACCEPT din za su nuna maka waiting for download... Kuma za ka ga wajen rubutun yana loading, sai ka dan jira.
Kana cikin jira za ka ga waiting for download din ya canza, ya koma download application a nan ma sai ka jira.
Daga nan sai ka jira download din tun daga 0% har sai ya kai 100% - wato ka ci gaba da jiransa tun daga farko har sai ya gama saukar da application ko game din.
Download din yana kai 100% za ka ga application ko game din ya fara install da kanshi. Sai ka jira ya gama installing din da kansa.
Yana gama install din daga can saman screen din wayarka za ka sakon app installed completed, sannan za a nuna maka Uninstall da kuma Open a kusa da application din.
Idan kuma kana so, ka bude application din da ka saukar, sai ka shiga Open. Kana shiga Open din za ka ga nan take application din ya bude.
Kaman yanda ake iya gani a hoton da ke sama, mun saukar da application a PlayStore, kuma mun budeshi, cikin sauki, kuma a kankanin lokaci. Wannan hanya da mu ka nuna ita mafi sauki wajen saukewa tare da install din application ko game daga PlayStore a wayar Android.
Za mu tsaya a nan, sannan kuma duk mai tambaya zai iya rubuta mana ita a wajen comment da ke can kasa. Da fatan ana amfanuwa da tutorial din da muke rubutawa a shafin nan. Mun gode, sai mun sake ganinku, a huta lafiya✋

Leave a Comment