Bayanin kimiyya game da Sun (Rana)
Rana ita ce zuciya, kuma tauraron dake tsakiyar solar system din mu. Kewaye da ita akwai duniyoyi guda takwas, da kuma gwamman gajerun duniyoyi (dwarf planet). Sannan akwai watanni sama da guda dari da hamsin wadanda su ke kewaye duniyoyin cikin solar system. Rana ta na da siffar kwallo (sphere). Bayan nan kuma ta na haifar zafi na futar hankali wanda ya ke canza sinadaran da su ke cikinta zuwa plasma.
Rana ita ce abu mafi girma kuma mafi nauyi a cikin solar system. Domin ita ta ke dauke da kaso casa'in da tara da digo takwas (99.8%) na nauyin solar system gaba daya. Sauran duniyoyi, da watanni, da kananun abubuwa kaman comet, da asteroid, da sauran abubuwan, su suke dauke da kaso sifili da digo biyu (0.2%) na nauyin solar system. Rana ta na iya daukan gaba daya duniyoyi takwas da suke cikin solar system kusan sau dari takwas. Rana ta na da fadin da zai dauki duniyar da muke ciki wato Earth sau dari daya.
Shin ko ka san ya ya saurin haske ya ke?
A bangaren sinadarai (element) kuma rana ta na dauke da sinadarai na iska (gases) kamansu Hydrogen, da Helium, da sauran element masu nauyi kaman su Carbon, da Nitrogen, da Neon, da Oxygen, da kuma Iron. Haka kuma cikinta ya na dauke da kaso casa'in da daya (91%) na iskar Hydrogen, da kaso takwas da digo tara (8.9%) na iskar Helium, sai kaso sifili da digo daya (0.1%) na sinadaran Nitrogen, da Carbon, da Neon, da Oxygen, da Iron da sauransu. Sakamakon haduwar wadannan sinadaran da suke cikin rana muke samun wannan isashshen karfi mai yawa daga rana.
Rana ta na da yanayin wuta wuta (fiery nature) wanda haduwar kananun sinadaran iska (isotope) na Hydrogen guda biyu ta hanyar da ake kira Thermonuclear fusion ko kuma Fusion Reaction shi ya ke haifar da samuwar sinadarin iska na Helium. Haduwar kananun wadannan sinadaran na Hydrogen shine ya ke haifar da zafi a cikin rana, kuma ya kai mataki ko maki miliyon ashirin da bakwai (27, 000, 000°F) a ma'aunin zafi na Fahrenheit, daidai da maki miliyon goma sha biyar (15, 000, 000°C) a ma'aunin Degree celsius - wa'iya zubillah!
Shin ka karanta bayanin kimiyya game da duniyar mercury kuwa?
Rana tanada layer guda shida, kuma ga su nan kaman haka:
1. Corona
2. Chromosphere
3. Photosphere
4. Convective zone
5. Radiative zone
6. Core
Thermonuclear fusion, reaction ne wanda ya ke faruwa a can cikin rana a layer da ake kira core. Wannan reaction din shine ya ke haifar da zafi mai tsananin gaske. Reaction ya na nufin haduwar wasu sinadarai domin su haifar da wani sinadari ko kuma karfin da ake bukata. Reaction da ya ke faruwa a cikin rana, shine ya ke samar da isashshen karfi ga duniyoyin da suke cikin solar system. Thermonuclear fusion shine ya ke haifar da isasshen karfin electricity, da kuma radiation na hasken rana da muke samu daga rana.
Ko ka karanta bayanin ya ya saurin duniyar Earth ya ke?
Heliosphere wani kewayene na rana wanda ya ke kare duniyoyi daga cosmic rays. Sun spot wasu ramuka ne, ko huji (holes) a jikin rana wadanda ta cikinsu karfin maganadisu (magnet) ya ke futowa daga cikin rana zuwa sauran duniyoyin da su ke cikin solar system. Karfin magnet din ya na futowane daga rana ta bangaren arewa zuwa kudu. Sannan kuma rana ita ce take samar da karfin gravity a cikin solar system gaba daya.
Ko ka san tsaunin Mount Everest?
Rana ita ce take rike da duniyoyin cikin solar system ta hanyar karfin gravity mai matukar karfi dake jikinta. Daga cikin hasken rana akwai hasken da ido yake iya gani wato visible light, da kuma wadanda ido ba ya iya ganinsu. Haske yana daukan minti takwas da wani abun kafin ya iso duniya. Haske yana tafiyar mita miliyon dari uku duk second daya (300, 000, 000m/s) daidai da kilomita dubu dari uku duk second daya (300, 000km/s).
Za mu dakata anan da fatan ana amfanuwa da darusan kimiya da fasaha wadanda muke rubutawa a shafinan. Mun gode sai mun sake ganinku.

Leave a Comment