Menene noun?

Idan mutum zai koyi kowane irin yare a duniya, abu mai matukar mahimmaci a garesa shine sanin nahawun yaren. Wanda shine zai taimaka masa wajen fahimtar yaren da kuma sanin ka'idojin karatu da rubutun sa. Sanin ka'idojin rubutu da karatu na harshe sune suke bunkasar da fahimtar yaren a kwakwalwar mutum.

Noun kalma ce ta turanci wanda take nufin suna, ko kuma mu ce suna gaba daya. Suna yana nufin wani harafi ko wata kalma da aka bawa wani mutum, ko wani abu, ko wata dabba, wanda zai sa ana ambatar wannan harafi ko wannan kalma abun nan ko mutumin nan zai fahimci cewa dashi ake. Haka kuma mai sauraro ko mai karatu zai fahimci cewa ga wanda ake nufi da wannan harafi ko kalma da aka ambata.

Noun yana nufin suna gaba daya. Idan muka ce suna gaba daya, muna nufin sunan mutane (persons), da gurare (places), da dabbobi (animals), da kuma sunan abubuwa marasa rai (things). Wadannan sunayen muna iya cewa sun kunshi sunan komai. Ga wasu sunaye da misalansu nan a kasa.

Misalin sunan mutane (person) sune Nura, da Hassan, da Fatima, da Zainab, da Tahir, da Usman, da Ibrahim, da Sa'adiya, da Ahmad, da A'isha, da Saratu, da Balkisu, da Hassana, da Habiba, da Hafsa, da Khadija, da sauran su.

Misalin sunan dabbobi (animal) kuma sune Zaki (lion), da Damusa (tiger), da Mage (cat), da Jaki (donkey), da Doki (horse), da Giwa (elephant), da Alade (pig), da Kare (dog), da Kifi (fish), da Bauna (buffalo), da Kunkuru (tortoise), da Kadangare (lizard), da Talo talo (turkey), da Akuya (goat), da Tunkiya (sheep) da sauran su.

Misalin sunan gurare (place) sune Makaranta (school), da Masallaci (mosque), da Makabarta (graveyard), da Kasuwa (market), da Coci (church), da Gidan mai (filling station), da Kogi (river) da, Gida (house), da Shago (shop), da Asibiti (hospital), da Bariki (barrack), da Banki (bank), da Farm (gona), da sauran makamantan su.

Misalin sunan abubuwa marasa rai (thing) sune Kwallo (ball), da Mota (car), da Keke (bicycle), da Littafi (book), da Katifa (matress), da Kofa (door), da Takalma (shoes), da Kwali (box), da Gwangwani (Tin), da Allin rubutu (chalk), da Tawada ta rubutu (ink), da Kwalba (bottle), da Buta (kettle), da Kofi (cup), da Benci (bench), da Spoon (cokali), da sauran makamantan su.

Bayan mun gama bayarda misalan suna da bangarorin da suke ga misalan su a cikin jumlolin da suke zuwa a kasa.

Misalai:
1. Musa is playing with a ball.
Wato: Musa yana wasa da kwallo.

A misalin nan na sama Musa shine sunan mutum (person), kwallo kuma shine sunan abu mara rai (thing), wanda Musa yake wasa da ita.

2. Ibrahim reads books at library everyday.
Wato: Ibrahim yakan karanta littattafai a dakin karatu kullum.

A misalin nan kuma littattafai sune sunan abubuwa marasa rai (thing). Ibrahim kuma shine person wato sunan wanda yakan yi wannan aikin kullum. Sannan dakin karatu shine wajenda (place) Ibrahim yakan yi karatu.

3. Zainab sold her goat at market.
Wato: Zainab ta siyar da akuyar ta a kasuwa.

A misalin nan kuma Zainab shine sunan mutum (person), goat kuma sunan dabba (animal), kasuwa kuma ita ce place wato sunan wajen da aka siyar da akuyar.

4. The boy threw a stone to birds at zoo park.
Wato: Yaron ya jefa dutse ga tsuntsaye a gidan kallon namun daji.

A misalin nan Yaro shine mutumin (person) da ya jefa dutse. Sannan kuma dutse shine sunan abu mara rai (thing). Sai kuma zoo park wato gidan kallon namun daji shine sunan wajen da akayi wannan aikin (place).

5. The Car that carried Nura and his Bag is travelling from Maiduguri to Katsina.
Wato: Motar da ta dauki Nura da Jakarsa tana tafiya daga Maiduguri zuwa Katsina.

Anan Mota da Jaka sune sunan abubuwa marasa rai (things). Nura kuma shine sunan mutum (person). Maiduguri da Katsina kuma sune sunan gurare (places) a cikin jimlar.

6. Nura arrieved Katsina earlier in the morning.
Wato: Nura ya iso Katsina da sassafe.

Anan kuma Katsina shine place wato sunan wajen da Nura ya je. Nura kuma shine sunan mutum wato person.

Zamu dakata da misalan anan sai mun zo da darasi na gaba, wanda a cikin sa za mu ci gaba da bayani akan sassan magana - tare da misalansu. Amma kafin sannan bari mu barku da wasu tambayoyi guda hudu wadanda zaku amsa su domin mu tabbatar da cewa ana amfanuwa da darusan koyan turanci da ake karantawa a shafin nan.

Tambayoyin sune:
7. A Lion caught a Zebra in forest.
Wato: Zaki ya kama Dokin dawa a cikin dawa.

8. Fatima went Market to buy a pencil and books.
Wato: Fatima ta tafi Kasuwa ta siya fensiri da littattafai.

9. Ahmad drives his Car to Filling station.
Wato: Ahmad ya tuka Motar sa zuwa Gidan mai.

10. Hassana broke a bottle.
Wato: Hassana ta fasa kwalba.

Tambayoyin sune a cikin wadannan jimloli guda hudu da suke sama, daga tambaya ta bakwai (7) zuwa ta goma (10) - muna so ku ciro mana sunan mutum; ko sunan waje ko guri; ko sunan abu mara rai; ko sunan dabba. Sannan kuyi comment da su a wajen comment dake kasa.

Haka kuma zaku iya tambaya akan duk abun da babu gane ba, mu kuma zamu baku amsa, idan Allah yasa mun san amsar tambayarku. Sannan daga karshe kuma muna fatan zamu sake ganinku a shafin nan. Mun gode, ahuta lafiya!

No comments

Powered by Blogger.