Yanda ake scanning din Barcode a wayar Android
Barcode wani zanene ko hoto wanda ake a jiye wasu bayanai a cikinsa. Bayanan cikinsa mutum ba ya iya fahimta har sai yayi amfani da wata na'ura sannan zai iya ganin menene a kunshe a cikin wannan code din. Sau dayawa za mu ga barcode wanda ya ke dauke da wasu bayanai akan abubuwan da mu ka siya, musamman kayan na'ura - amma ba mu san menene amfaninsa ba, sai mu ketashi, ko kuma konashi.
Shin ko ka iya scanning din document a wayarka ta Android?
Katin zabe, ko katin dan kasa jikinsa akwai barcode wanda zai bayar da daman gano mai wannan katin ko da hoton jikin baifuto mai kyauba.
A kasar Saudi Arabia an yi amfani da barcode ta hanyar saka bayanan mutane cikinsa. Duk wanda ya shiga kasar za a saka bayanansa a cikin barcode, sannan sai a bawa mutun wani abu da zai daura a hannunsa kaman agogo. Wannan abun jikinsa akwai barcode, kuma barcode din ya na dauke da bayanan mutun, kaman sunanshi, da shekarunsa, da kuma asalin kasarsa.
Kayan aikin sune:
1. Barcode
2. QR & Barcode Scanner
Mu na bukatar barcode wanda za mu gwada karanta bayanan cikinsa ta hanyar application din nan. Ana samun barcode a jikin kwalin waya, da na magani. Kuma ana samunsa a jikin katin zabe, da katin dan kasa da sauransu.
Ga yanda ake scanning din
1. Da farko, ka je Play store, ka yi install din QR & Barcode Scanner. Kafin mu yi nisa a tutorial din zan yi scan din barcode guda uku daban daban. Na farkon barcode ne wanda ya ke dauke da PIN dina na BBM. Na biyun kuma barcode din jikin kwaline na wata waya ta kamfanin MTN. Sai na karshen kuma barcode din jikin takaddar jikin layin MTN ne. Ga nan hoton farkon wanda zan fara scan dinsa.
Kaman yanda ake gani a hoton da ke kasa, ga barcode din a jikin hoton da ke cikin wayar nan.
2. Bayan ka gama install na application din, sai ka bude shi. Ka na bude shi za ka ga camerar wayarka ta bude kaman za ka dauki hoto. Sai ka daidai camerar wayartaka akan barcode din kaman za ka dauke shi a hoton.
3. Ka na daidaita camerar wayar akan barcode din za ka ga application din ya fara karanta code din. Ya na gama karanta barcode din zai nuno maka bayanan cikin barcode din.
4. Idan ka yi haka shikenan, ka gama scanning na barcode din. Za mu kara misali ta hanyar karanta menene a cikin barcode din jikin wannan kwalin.
5. Sai ka daidaita camera wayarka akan barcode din jikin kwalin kaman za ka daukeshi a hoto - za ka ga application din ya fara scanning na code din. Ya na gama scan din zai nuna maka bayanan cikin barcode din jikin kwalin.
6. Zan kara misali daya, ga barcode a jikin takkadar gidan layi.
7. Sai ka bude application din sannan ka daidaita zanen barcode din jikin takkadar a tsakiyan screen din wayarka.
Za ka ga application din ya fara scanning din barcode din jikin takkadar. Ya na gama scan din zai nuna maka bayanan cikin barcode din. Wannan barcode din adreshin yanar gizone wanda za a saukar da application din MTN mai suna MyMTN App ne a cikinsa.
Wadannan matakan ake bi idan za a yi scanning din barcode a wayar Android cikin sauki. Da fatan ana amfanuwa da darusan da mu ke rubutawa a shafin nan.
Sannan duk wanda ya ke da tambaya kofa a bude ta ke, sai ya yi kasa wajen comment ya rubuta mana ita. Mu kuma za mu ba shi amsa, idan Allah ya sa mun sani.
Ku na iya tura wannan post din ga dandalin sada zumunta domin abokanku su karanta. Mun gode, sai mun sake ganinku, a huta lafiya.

Leave a Comment