Yanda Zaka Saukar Da Bidiyo A YouTube Da Opera
Shafin YouTube dai shine babban shafin bidiyo akan internet, wanda ake samun kowane irin bidiyo. Kallon bidiyo a shafin YouTube kyauta ne. Bidiyoyin da suke shafin YouTube kai tsaye ake kallon su wato streaming - kuma babu dama a saukar da su. Wannan yasa mutane dadama suke tambaya akan yanda ake saukar da bidiyo a YouTube.
A tutorial din da muka rubuta a baya munyi bayanin yanda ake saukar da bidiyo a YouTube ta Opera, kuma a wayar Symbian. A shafin nan mun nuna hanyoyi masu yawa da ake saukar da bidiyo a YouTube. Wasu hanyoyin ana amfani da application kaman KeepVid, da VidMate. Hanyoyin suna da sauki sosai, idan kabi daki daki kaman yanda mu kayi bayani.
Ba shafin YouTube kadai ba, har shafukan Facebook da Instagram munyi bayanin yanda ake saukar da bidiyoyi a cikin su. Shiga nan idan kana so ka koyi yanda ake hada intro YouTubea cikin wayar Android. Ko nan idan kana so kasan menene subcribe da amfanin sa a YouTube.
Kayan Aikin Sune
1. Opera Mini
Bayan ka saukar da Opera Mini, sai ka je kayi install nata. Idan ka gama install nata gaba daya - sai ka bude ta, kana bude ta, sai kayi kasa ka karanta yanda ake yi.
Ga Yanda Akeyi
1. Da farko, kaje ka shiga shafin YouTube. Tana bude maka shafin, sai ka je kan bidiyon da kake so ka saukar. Kana zuwa kan bidiyon da kake so ka saukar din sai ka taba kan shi. Zamuyi misali da wannan bidiyon mai suna How software is made.
2. Kana taba bidiyon zai bude maka bidiyon kaman zakafara kallo a online.
3. Idan yabude maka bidiyon sai kayi stop ko pause nashi, sai ka shiga wajen saka URL Address. Idan kashiga URL Address ka cire m. na gaba da https://m. sai kasa ss a wajensu. Kana saka ss din wajen daga https://m.youtube zai koma https://ssyoutube sai ka danna Go.
4. Kanayin haka zakaga takaika shafin savefrom.net sai kayi kasa kaje wajen da kaga hoton bidiyon kasa dashi zakaga Download sai ka tabashi.
5. Kana dannawa zakaga yakowa maka wasu zabuka guda biyu sun futo daga kasa. Sai ka zabi Download nan take zai fara downloading na bidiyon.
6. Kanayin haka zakaga tafara downloading na bidiyon. Sai ka jira tagama saukar maka da bidiyon. Idan tagama saukar maka da bidiyon, sai kaje folda mai suna Download zaka samu wannan bidiyon da ka saukar a shafin YouTube.
Wannan hanyar da muka nuna tana da sauki wajen saukar da bidiyo a shafin YouTube. Idan ka bi matakan nan kaman yanda muka nuna a sama, zaka iya yin komai a cikin kankanin lokacin.
Bari mu tsaya anan tun da gaba daya bayanin yakammala. Muna fatan ana amfanuwa da darusan da muke rubutawa a shafin nan. Sannan kuma kuna iya baiyana ra'ayoyin ku, ko kuma ajiye tambaya a wajen comment dake kasa.
Yana da kyau ka saukar da Mp4 na kusa da 720, saboda shine bidiyon da yake budewa daidai a wayar Android. Idan kuma ka saukar da wanda ba shi ba, wayar zata bude shi sai dai ba zai nuna maka mai kyau kaman 720 ba.
Daga karshe kuma muna godiya akan ziyara da kuke kawowa zuwa shafin nan. Sai mun sake ganin ku!
Leave a Comment