Hanya ma fi sauki ta saukar da bidiyo a YouTube

A shafin nan mun nuna hanyoyi masu yawa wadanda ake bi a saukar da bidiyoyi a shafin YouTube. Mafi yawa daga cikin hanyoyin nan masu sauki ne, kadan daga cikin su kuma akasin haka. Sai dai wannan hanyar da zamu nuna a yanzu tana da sauki sosai, wanda muna iya cewa kowa zai iya saukar da bidiyo a YouTube idan ya bi yanda mu ka yi bayani.
Ina ga ba sai mun tsaya mun bata lokaci akan jawabin gabatarwa ba. Saboda a baya mun yi bayanin yadda ake saukar da bidiyo a shafin YouTube cikin sauki. Sabanin hanyoyin da muka nuna a baya wannan hanya da application guda biyu za muyi aiki. Application na farko za mu shiga YouTube, mu nemo bidiyon dashi. Shi kuma application na biyun da shi za muyi amfani mu saukar da bidiyon da muka nemo.
Kaman yanda mu kace wannan hanyar duk ta fisu sauki, saboda babu wani copy da paste na url da ake yi. Sai dai kawai ayi share na url din bidiyon daga application din nan zuwa wancan application din. Misali share na bidiyo daga application na YouTube zuwa KeepVid - nasan hakan babu wahala ko kadan. Kawai kai dai ka cigaba da karatu domin koyan yanda abun yake.
Kayan aikin su ne:
1. KeepVid
2. YouTube
Ga yanda ake yi
1. Da farko, ku saukar da wadannan application din guda biyu da mu ka bada sunayen su a sama ta hanyar taba kan sunayen nasu. Bayan kun gama saukar dasu, sai kuyi install nasu - kuna gama install nasu, sai kuzo ku fara bude application na YouTube.
2. Ku na bude shi sai kuje kan bidiyon da zaku saukar. Kuna zuwa wajen bidiyon sai ku taba kan bidiyo. Bari muyi muku misali da bidiyon nan mai suna How does transistor work. Kuma haka za ku yi kuje ku taba kan bidiyon da kuke so ku saukar.
3. Ku na taba kan bidiyon za ku ga ya bude, wato zai fara nuna muku cikin bidiyon. Kawai sai ku tsayar da shi. Kuna tsayar da shi ku duba daga kasan bidiyon zakuga wajen Share sai ku taba shi.
4. Kuna taba Share din zai budo muku hanyoyin Share da suke wayar ku gaba daya - yana budo muku sai ku duba za ku ga tambarin KeepVid. Ku na ganin tambarin sai ku taba shi.
5. Ku na taba kan tambarin za ku ga ya kai ku cikin KeepVid, kuma ga wancan bidiyon da kuke son saukarwa. Sai ku taba wancan shudin arrown da yake kasan bidiyon ta bangaren hannun dama.
6. Kuna tabawa za ku ga ya fara analyzing - sai ku dan jira kadan. Yana gama analyzing din zai nuno muku Save video as: kawai sai ku taba kan 720p HD MP4. Kuna taba kan 720p HD MP4 zakuga sun nuna muku The task has been added successfully, wato wayar ta fara saukar da bidiyon.
Inaga wannan hanya ita ce hanya mafi sauki, da ake bi a saukar da bidiyo a shafin YouTube. Kafin wannan hanyar mun nuna wasu hanyoyin da ake bi a saukar da bidiyo a YouTube wadanda su din ma basu da wahala. Kuna iya shiga nan domin koyan yanda ake saukar da bidiyo a YouTube, da application mai suna VidMate.
Idan kuma kuna so ku koyi yanda ake saukar da bidiyo a shafin Facebook ne, sai ku shiga nan - masu son koyan yanda ake saukar da bidiyo a Instagram kuma su shiga nan.
Nan shine karshen tutorial din nan sai kuma mun zo da wani sabo. Fatan ana amfanuwa da rubuce rubucen mu. Zaku iya tambaya akan abun da baku gane ba, a wajen comment dake kasa.
Mun gode a huta lafiya!
Leave a Comment