Yanda Zaka Saukar Da Bidiyo A YouTube Ta Opera A Wayar Symbian



Shafin YouTube shafi ne na bidiyo, wanda muna iya cewa shine babban shafin yanar gizo wanda ake samun kowane irin bidiyo a cikin sa, sannan kuma a kallesu kyauta. Sai dai wasu masu amfani da shafin su kan so su saukar da bidiyo a shafin, amma basu san yanda akeyi ba.

A baya mun nuna yanda ake saukar da bidiyo a YouTube, da Facebook, da Instagram, amma ga masu aiki da Android. A yanzu kuma zamuyi wa masu amfani da Symbian da Nokia java bayanin yanda suma za su saukar da bidiyo a wayoyin su.

A tutorial din nan za muyi bayani ne a matakai guda biyu, wanda duk ana iya saukar da bidiyo a YouTube dasu. Sannan kuma da Opera Mini zamuyi aiki a duka matakan.

Ka tabbata kana da Opera a wayar ka, idan kuma baka da ita ka shiga nan, sai ka saukar da ita. Bayan ka gama saukar da ita, sai ka yi install nata. Kana gama install nata sai kayi kasa ka karanta yanda akeyi.

Ga Yanda Akeyi
1. Ka bude operar ka, sai ka shiga YouTube, idan kuma babu a operar ka, sai ka rubuta www.youtube.com sai kayi Ok.


2. Kana yin haka sai ka jira ta kai ka cikin shafin YouTube. Tana kawo ka shafin YouTube din, sai ka je kan bidiyon da zaka sauke. Za muyi misali da bidiyon nan mai suna How to Create a Free Website daga channel mai suna Tech Fire.


3. Kana shiga bidiyon sai ka danna Option ko Menu. Sai ka shiga wajen saka url address zakaga url address na bidiyon kaman haka https://m.youtube.com/watch?v=wlvQCJSO0xc sai ka cire m. din da yake gaba da https://, sai kasa ss a wajen sa sannan ka danna Ok.



4. Kana yin haka za su kai ka cikin shafin savefrom.net - kuma zakaga hoton bidiyon da zaka saukar a wajen, sai kayi kasa.


5. Suna kawo ka cikin shafin sai kayi kasa ka je wajen download. Kana zuwa wajen sai ka shiga Mp4 na biyun, wato Mp4 na kusa da 360.


6. Kana shiga zakaga bidiyon yafara zuwa sai ka jira yagama zuwa wayar taka.


7. Kana gama saukar da bidiyon sai kaje folda mai suna Video ko Video clips anan zaka samu duk bidiyon da ka saukar da opera.

8. Ka sani wajen saukar da bidiyo a shafin savefrom.net bawai 3GP - 240 ne kadai ba. Akwai wasu daban, sai dai shi 3GP - 240 shine yake budewa a Symbian da sauran kananun wayoyi. Idan ka saukar da wanda basu ba, to zakaga bidiyon yafi karfin wayarta ka. Wato gashi nan a cikin wayar ta bude shi amma bata nuna hoto, sai kaji sauti kadai. Daman shi 3GP - 240 shine daidai da irin wadannan wayoyin.

Ga Mataki Na Gaba
9. Ita kuma wannan hanyar yanda akeyi shine, idan ka shiga bidiyon da kake so ka saukar dashi. Su na kawo ka wajen bidiyon, sai ka bude wajen saka url address kasa pp a tsakanin sunan youtube din da .com - misali kaman daga https://youtube.com/watch?v=Ik4zE8lXWs8 sai ka canza shi zuwa https://youtubepp.com/watch?v=Ik4zE8lXWs8 sannan saii ka danna OK.

10. Kana yin haka za su kai ka cikin shafin y2mate.com, shima anan ana saukar da bidiyoyin YouTube a kyauta.



11. Su na kai ka cikin shafin y2mate.com din, sai ka yi kasa kadan zakaga hoton wannan bidiyon, nan din ma sai ka karayin kasa, zakaga wajen saukar da bidiyon. Sai ka shiga Download dake kusa da 360p. Zasu tambaye ka sai ka danna Save. Daga nan zakaga bidiyon ya fara zuwa, sai ka jira ya gama zuwa.



12. Ka sani wajen saukar da bidiyo a cikin shafin y2mate.com bawai Download 360p ne kadai ba. Akwai wasu daban sai dai shi 360p shine yake budewa a Symbian da sauran kananun wayoyi. Idan ka saukar da wanda ba shi ba, to zakaga bidiyon yafi karfin wayar ta ka.

Bayan saukar da bidiyon, a shafin ne ake converting na bidiyoyin YouTube zuwa audio. Wato daga bidiyo, zuwa sautin murya kadai.

Saukar da bidiyo a shafin YouTube babu wahala inde kana da isasshen datar shiga yanar gizo. Sannan kuma akwai yayin sadarwa mai karfi.

A manyan wayoyi kaman su Android, kai harda computer ma, ana iya amfani da wannan tutorial din domin sauke bidiyo a YouTube.

Idan da zamu lura application na YouTube da muke aiki dasu a wayoyin Symbian za muga cewa yanzu sun dena aiki kwata kwata. Amma idan mu kayi aiki da Opera mukan samu muga bidiyoyin YouTube tare da Real player. Sai dai bidiyoyin basa futowa mai kyau gwara kawai ka saukar dasu inaga zaifi.

Za mu tsaya nan da fatan ana amfana, idan kuna da tambayoyi akan abun da baku gane ba, kuna iya tambaya zaku samu amsa da zarar mun san amsar.

Mun gode da kawo ziyara shafin nan, muna fatan zamu sake ganin ku, a huta lafiya!

No comments

Powered by Blogger.