Yanda ake bude WhatsApp

WhatsApp dai mun riga mun yi bayaninsa, da amfanoninsa a tutorial mai taken menene WhatsApp wanda mu ka yi a baya. Saboda haka yanzu mun zo da bayanin yanda ake budeshi a waya cikin sauki.

Saukar da WhatsApp a nan
1. WhatsApp ga masu Android
2. WhatsApp ga masu iPhone da iPad

Ga yanda ake yi
1. Da farko ka shiga Play store, ko App store, ka yi install din WhatsApp a wayarka. Bayan ka gama install din sa sai ka budesa. Ka na budesa za ka ga daga can sama an rubuta maka Welcome to WhatsApp. Sai ka yi kasa ka shiga inda aka rubuta AGREE AND CONTINUE.


2. Ka na shiga za ka ga an kawoka wajen Verify your phone number. Wato wajen da za ka rubuta lambarka. Idan ka lura za ka ga country code din kasarka. Daga gaba shi kadan za ka ga wajen da aka rubuta phone number wato wajen da za ka rubuta lambar wayarka.


3. Sai ka shiga wajen rubuta lamba, ka rubuta lambar wayarka, sannan ka shiga NEXT. Misali, 08023456789, sai ka shiga NEXT.


4. Ka na shiga NEXT din za ka ga sun rubuta ma ka We will be verifying the phone number. Kuma a wajen za ka ga lambar da ka rubuta. Idan lambar da ka rubuta akwai kuskure a cikinta, kuma za ka canzata sai ka shiga EDIT, ka sake rubuta lambar. Idan kuma lambar ta yi daidai, sai ka shiga OK.


5. Ka na shiga OK watakila za su nuna maka To easily verify your number, WhatsApp can automatically detect your verification code if you allow WhatsApp to view SMS messages sai ka shiga CONTINUE.


6. Bayan ka shiga CONTINUE, za su sake tambayarka kaman haka Allow WhatsApp to send and view SMS message, sai ka taba ALLOW.


7. Daga nan za su nuna maka Waiting to automatically detect an SMS sent to +234 802 345 6789, sai ka je cikin inbox din wayarka za ka samu sako daga WhatsApp.


Sai ka kwafo code din da ka gani a cikin sakon, ka dawo cikin WhatsApp ka rubutasu a wajen da aka rubuta Enter 6-digit.

Amma hanya ma fi sauki ka bari WhatsApp din zai yi verifying din lambarka da kansa. Sai ka jira WhatsApp din da kansa zai gano code a cikin inbox din wayarka. Ya na gano code din zai rubuta ma ka verifying...


8. WhatsApp din ya na gama verifying zai tambayeka To find your backup on Google Drive, allow WhatsApp access to your contacts. Idan za ka yi backup na sakonninka sai ka shiga CONTINUE. Idan kuma ba za ka yi backup din ba sai ka shiga kawai ka shiga NOT NOW.


9. Ka na gamawa da matakin sama WhatsApp din zai tambayeka Allow WhatsApp to access your contacts? Sai taba ALLOW.


10. Daga za a nuna ma ka Profile info, sai ka taba wajen hoton camera na kusa da inda aka rubuta Type your name here.


11. Ka na taba wajen za ka ga an rubuta ma ka Profile info, kuma za ka ga Camera da Gallery. Sai ka shiga camera ka dauki hoton da za ka daura a profile na ka. Idan kuma hoton ya na cikin wayarka sai ka shiga Gallery ka zabo hoton, sannan ka yi OK a kansa.


12. Ka na zabo hoton za ka ga WhatsApp din ya rubuta ma ka Profile photo updated


13. Daga nan sai ka shiga wajen Type your name here, sai ka rubuta sunanka. Misali, Nura Mahdi Idris, sannan ka shiga NEXT.


14. Ka na yin haka za ka ga WhatsApp ya fara initializing... Sai ka jira ya gama.


15. WhatsApp din ya na gama initializing, zai nuno maka wajen CHAT, da STATUS, da kuma CALL. Idan za ka tura sako sai ka taba plus ➕ wanda ya ke can kasa.


16. Ka na taba plus din za ka ga wasu abubuwa sun baiyana sai ka shiga na can sama wato Chat.


17. Ka na shiga chat WhatsApp din zai kawoka cikin contact din wayarka. Ya na kawoka cikin contact din za ka ga hoton duk wanda ya ke WhatsApp a jikin lambarsa.


18. Sai ka shiga kan lambar wanda za ka tura ma sa sakon.


19. Ka na shiga kan lambar za ka ga wajen rubuta sako, sai ka shiga, ka rubuta sakonka sannan ka tura masa. Ka na tura masa sakon a take sakon zai tafi.


Bayan ka aika ma sa sakon idan ya gani shima zai yi ma ka reply. Za mu tsaya a nan a tutorial na gaba za mu nuna yanda yin status a WhatsApp.

Wannan shi ne yanda ake bude WhatsApp a saukake. Sannan kuma idan WhatsApp na ka ya yi expire ka na iya bin wadannan matakan domin sabuntashi.

Mu na fatan ana amfanuwa da tutorial din da mu ke rubutawa a shafin nan. Sannan duk wanda ya ke da tambaya ya na iya rubutawa a wajen comment da ya ke can kasa, zai samu amsa idan Allah ya sa mun sani.

Mu na fatan sake ganinku a shafin nan. Sannan ku na iya share na tutorial din nan a shafukan sadarwa domin wasu ma su amfana. Daga karshe mu na godiya akan ziyarar da ku ke kawowa shafin nan. Mu na fatan za ku huta lafiya.

No comments

Powered by Blogger.