Yanda ake seta dark mode a Twitter
A yanzu amfani da tsarin dark mode a wayoyin hannu shi ake ya yi, saboda tsarine mai matukar mahimmaci ga lafiyar idon mai aiki da waya. Domin ya kan rage yawan radiation (adadin haske) da ke futowa a screen din waya zuwa idon mutum. Wanda hakan ya na da mahimmaci wajen kula da lafiyar ido.
Kafin bullo da tsarin dark mode, ma su amfani da waya su kan yi amfani da tsarin eye care, wanda ya ke rage haske waya daidai yanda ake tsammanin ba zai cutar da lafiyar idon mutum ba.
Ko-da-ya-ke a yanzu ba wai a cikin application kadai ba, hatta tsarin launin cikin waya akwai na dark mode. A darasun da su ka gabata da jimawa a shafin nan mun yi bayanin yanda ake seta dark mode a WhatsApp, da Facebook, da Xender wannan ya sa a yanzu za mu ci gaba da bayani akan yanda ake seta dark mode a Twitter.
Masu amfani da Android, da iPhone duk matakai daya za su bi, domin seta dark mode a application din su na Twitter. Amma fa watakila a samu wasu 'yan banbance banbance kadan a matakan.
2. Twitter ga masu iPhone da iPad
Amma ya na da kyau a sani cewa tsofin version na application din Twitter ba a seta mu su dark mode, sai dai sabbin version kadai. Saboda haka idan ba ka da sabon version na application din Twitter a wayarka, sai ka yi kasa, ka saukar da shi a App store ko Play store ta hanyar link din da mu ka bayar.
2. Ka na taba kan hotonka za ka ga application din ya nunoma wasu zabuka, sai ka yi kasa, ka shiga Settings and policy.
3. Ka na shiga Settings and policy, sai ka yi kasa wajen General, ka shiga Display and sound.
4. Ka na shiga wajen Display and sound, sai ka zo wajen dark mode, za ka same shi a Off, wato a rufe.
5. Daga nan sai ka shiga wajen domin bude dark mode din. Ka na shiga wajen sai ka taba On.
6. Ka na taba kan On din za ka ga a take cikin application din ya yi duhu.
7. Application din ya na yin duhu sai ka dawo baya ka ci gaba da harkokinka a Twitter kaman yanda ka saba.
Wadannan su ne matakan da ake bi wajen seta dark mode a shafin Twitter ta hanyar official application din su. Sannan kuma idan ka na so ka cire dark mode din sai ka dawo ka rufe shi, wato ka canzashi daga On, zuwa Off ka na yin haka a take za ka ga cikin application din ya yi haske.
Ina ga za mu dakata a nan da fatan a na amfanuwa da tutorial din da ake karantawa a shafin nan. Sannan kuma duk mai tambaya ko neman karin bayani sai ya je kasa wajen comment ya rubuta. Zai samu amsa idan Allah ya sa mun sani.
Ku ci gaba da kasancewa da shafin Arewanote, domin samun tutorial, da darusan koyan turanci, da lissafi, da kuma bayanan kimiyya da fasaha a ko-da-yaushe. Sannan ku na iya ba da gudunmuwarku ta hanyar gaiyato abokanku su zo, su amfana da bayanan da mu ke wallafawa a shafin nan. Mun gode, a huta lafiya, sai mun sake ganinku.
Kafin bullo da tsarin dark mode, ma su amfani da waya su kan yi amfani da tsarin eye care, wanda ya ke rage haske waya daidai yanda ake tsammanin ba zai cutar da lafiyar idon mutum ba.
Ko-da-ya-ke a yanzu ba wai a cikin application kadai ba, hatta tsarin launin cikin waya akwai na dark mode. A darasun da su ka gabata da jimawa a shafin nan mun yi bayanin yanda ake seta dark mode a WhatsApp, da Facebook, da Xender wannan ya sa a yanzu za mu ci gaba da bayani akan yanda ake seta dark mode a Twitter.
Masu amfani da Android, da iPhone duk matakai daya za su bi, domin seta dark mode a application din su na Twitter. Amma fa watakila a samu wasu 'yan banbance banbance kadan a matakan.
Saukar da application din Twitter
1. Twitter ga masu Android2. Twitter ga masu iPhone da iPad
Amma ya na da kyau a sani cewa tsofin version na application din Twitter ba a seta mu su dark mode, sai dai sabbin version kadai. Saboda haka idan ba ka da sabon version na application din Twitter a wayarka, sai ka yi kasa, ka saukar da shi a App store ko Play store ta hanyar link din da mu ka bayar.
Ga yanda ake setawa
1. Da farko, ka shiga application din Twitter kaman yanda ka saba. Amma fa ka tabbata ka na aiki da sabon version din application na Twitter, kaman yanda mu ka yi bayani a sama. Ka na shiga Twitter sai ka je can sama ka taba kan hoton profile dinka, kaman za ka duba profile dinka.2. Ka na taba kan hotonka za ka ga application din ya nunoma wasu zabuka, sai ka yi kasa, ka shiga Settings and policy.
3. Ka na shiga Settings and policy, sai ka yi kasa wajen General, ka shiga Display and sound.
4. Ka na shiga wajen Display and sound, sai ka zo wajen dark mode, za ka same shi a Off, wato a rufe.
5. Daga nan sai ka shiga wajen domin bude dark mode din. Ka na shiga wajen sai ka taba On.
6. Ka na taba kan On din za ka ga a take cikin application din ya yi duhu.
7. Application din ya na yin duhu sai ka dawo baya ka ci gaba da harkokinka a Twitter kaman yanda ka saba.
Wadannan su ne matakan da ake bi wajen seta dark mode a shafin Twitter ta hanyar official application din su. Sannan kuma idan ka na so ka cire dark mode din sai ka dawo ka rufe shi, wato ka canzashi daga On, zuwa Off ka na yin haka a take za ka ga cikin application din ya yi haske.
Ina ga za mu dakata a nan da fatan a na amfanuwa da tutorial din da ake karantawa a shafin nan. Sannan kuma duk mai tambaya ko neman karin bayani sai ya je kasa wajen comment ya rubuta. Zai samu amsa idan Allah ya sa mun sani.
Ku ci gaba da kasancewa da shafin Arewanote, domin samun tutorial, da darusan koyan turanci, da lissafi, da kuma bayanan kimiyya da fasaha a ko-da-yaushe. Sannan ku na iya ba da gudunmuwarku ta hanyar gaiyato abokanku su zo, su amfana da bayanan da mu ke wallafawa a shafin nan. Mun gode, a huta lafiya, sai mun sake ganinku.
Leave a Comment