Yanda ake seta yaren turanci a China phone ko da ba a gane yaren wayar

Akwai wani lokaci da ka za ka ga cewa idan ka ajiye wayarka yara su na dauka su yi shige-shige a cikin wayar. Wani lokacin ma za ka samu sai su canzama yaren wayar daga turanci zuwa wani yare wanda ba ka fahimtarsa. Daga nan kai kuma sai ka rasa yanda za ka yi, saboda ba ka fahimtar yaren da aka seta wayar bisa kuskure.


Indai ka fuskanci wannan matsalar cikin sauki za ka maganceta, ba tare da wata wahala ba. Abun da za ka yi shine bayan an seta wani yare a wayar sai ka dakko wayar sai ka danna *#0000#.


Ka na gama dannasu, sai ka danna wajen kira, ka na danna wajen kira za ka ga wayar ta rubutama Language set to default.


Ka na yin haka shikenan, za ka ga yaren da wayar ta zo da shi wanda ya ke aiki a kanta ya dawo.

Amma ya na da kyau a sani cewa shi yaren waya ya na da alaka da yanki ko nahiya ko kasa. Wayar da aka kawo kasashen yammacin afurka kamansu Nigeria, da Ghana, da Gambia, da Liberia, da kuma Sierre Leone yarenta na zuwa shine turanci inglishi (English), saboda shine yaren da hukuma ta ke aiki da shi.

Haka kuma wayoyin da aka kawo kasashen yammacin afurka kaman su Niger, da Mali, da Benin republic, da Togo, da Senegal, da Ivory coast, da makamantansu yarensu na zuwa shine faransanci (French).

Wayoyin da aka kai su Mozambique su kuma yarensu na zuwa shine yaren kasar Portugal wato Portuguese. Domin kowane kamfanin kera wayar salula ya na la'akari da yaren da gwamnati ko hukumomin wannan kasar su ke aiki da shi wajen aikace-aikacensu. Sannan kuma akwai local language wato asalin yaren mazauna wannan yankin kaman arewacin Nigeria akwai yaren Hausa, kasar Kenya akwai Swahili.

Za mu dakata a nan da fatan a na amfanuwa da tutorial din da mu ke rubutawa a shafin nan. Sannan mu na fatan sake ganinku a shafin, mu na godiya bisa ziyartar shafin nan da ku ke yi. A huta lafiya.

No comments

Powered by Blogger.