Bayanin kimiyya game da duniyar Earth
Earth ita ce duniyar da mu ke rayuwa a cikinta, kuma duniya ta uku daga rana a cikin duniyoyin solar system. Hakama duniya ta uku a bangaren terrestrial. Duniyar Earth ita ce duniya ta biyar mafi girma a cikin solar system - kuma mafi girma a bangaren terrestrial. Earth ce duniya kadai wanda take da ruwa a cikinta. Saboda haka, ita kadaice za a iya rayuwa a cikinta.
Earth ta na dauke da sinadaran Nitrogen da Oxygen masu yawa. Wadannan sinadaran su na da matukar mahimmanci ga rayuwar dan Adam, da dabbobi, da kuma tsirrai. Sannan sinadarin Carbon dioxide ya na da matukar karanci a cikinta, wanda za a iya cewa kusan babu shi idan aka kwatanta yawansa da yawan sinadaran Oxygen da Nitrogen.
Daga rana zuwa Earth akwai nisan akalla kilomita miliyan dari da hamsin (150, 000, 000km). Duniyar Earth cikinta akwai dazuka, da tsaunuka, da dutwasu, da sauran gurare masu burgewa da kayatarwa da kuma ban sha'awa. Sannan duniyar Earth akwai manyan tekuna wadanda halittun ruwa kaman giwar ruwa (whale) da dorina da kada da kifaye su ke rayuwa a cikinsa.
Bayan teku duniyar Earth ana yin ruwan sama wanda ya ke taimakawa sirrai su rayu kuma dan Adam ya yi amfani da su. Haka kuma akwai dazuka masu cike da ciyawu kala-kala da kuma dabbobin jeji kaman barewa da dila. Akwai yankuna da ake samun sanyi mai tsananin wanda har ake samun duwatsun kankara (iceberg) inda dabbobi kaman bear da penguin su ke rayuwa.
Earth wata guda dayane ya ke kewayeta wato moon. Sannan ya na daukan kwanaki ashirin da tara (29 days) kafin ya kewayeta. Ita ma Earth takan dauki kwanaki dari uku da sittin da biyar (365 days) kafin ta zagaye rana. Wanda hakan shine shekara daya. Sannan a cikin shekara dayan nan wata yakan zagaye duniya sau sha biyu.
Duniyar Earth ta kan yi elliptical orbit, kaman yanda sauran duniyoyin su ke yi. Elliptical orbit ya na faruwane a lokacin da duniya ta yi nesa da rana sai ta fara juyawa a hankali, amma a lokacin da ta matso kusa da rana za ta ci gaba da juya da sauri. Wannan shiyasa cikin ikon Allah za ka ga rani ko damuna ko sanyi wani ya fi wani jimawa.

Leave a Comment