Bayanin kimiyya game da duniyar Mercury

Duniya mai suna Mercury ita ce duniya ta farko, sannan mafi kusa da rana, dayace daga cikin duniyoyin bangaren terrestrial a solar system. Kalmar Mercury ta samo asali daga sunan wani dan aiken ubangijin 'yan addinin rumawa. Mercury ce duniyar da tafi samun kafin jawowa na gravity daga rana.

Duniyar Mercury ta na daukan kwanaki tamanin da takwas kafin ta zagaye rana. Wato kwanaki tamanin da takwas (88 days) shine shekara daya acan. Duniyar Mercury tanada fadin (diametre) mai tsawon kilomita dubu hudu da dari takwas da tamanin (4, 880km). Wato kusan daidai fadin nahiyar kasar Amurka mai fadin kilomita dubu hudu da dari uku da goma sha uku (4, 313km). Mercury ta na kewaye rana da saurin tafiya akalla kilomita dubu dari da sittin da dari tara da talatin da uku a duk sa'a (160, 934kmph).

Tsakanin duniyar Mercury da rana akwai nisan akalla kilomita miliyan hamsin da takwas (58, 000, 000km). Duniyar Mercury babu wata wanda ya ke kewayeta. Sannan kuma satellite guda biyune su ka je duniyar Mercury, kuma su ne Mariner 10, da Messenger. Wadannan satellite guda biyun su ne su kawo bayanan da mu ke da su game da Mercury a yau. Mercury ba ta da tectonic plate kaman yanda Earth take da shi.


Kowace duniya akwai nisan da ake kira Exosphere, wanda shine karshenta. Hakama a Mercury akwaishi kuma ya kunshi sinadaran Oxygen, da Sodium, da Hydrogen, da Helium, da kuma Pottasium. Wadannan sinadaran iska mai karfice daga solar system ta ke sharosu daga doron kasa na cikin Mercury zuwa can sama har Exosphere.

Mercury kaman kowace duniya da ta ke bangaren terrestrial a solar system ita ma tanada layer guda uku kuma sune:
1. Core
2. Mantle
3. Crust

No comments

Powered by Blogger.