Bayanin kimiyya game da Moon

Wata shine wani babban abu mai girma a cikin sarari wanda ya ke zagaye wata duniya. Sannan kuma shi kansa cikinsa ya na kamada cikin duniya. Sai dai shi karamine sosai idan aka kwatanta girmansa da girman duniya. Wata shima kaman duniya a mulmule ya ke wato ya na da siffar kwallo kaman yanda kowace duniya take. A cikin solar system akwai wata sama da guda dari da hamsin wadanda su ke kewaye duniyoyin cikin solar system.

Kowace duniya akwai adadin watannin da su ke kewayeta, misali duniyar nan wato Earth akwai wata guda daya wato 'Moon' wanda shi kadaine ya ke kewayeta, Mars akwai watanni guda biyu wadanda su ke kewayeta kuma sune Phobos da Deimos, sai kuma Saturn wanda watanni samada hamsin ne su ke kewayeta. A cikin rubutun nan za mu yi bayanine game da watan da ya ke kewaye duniyar da mu ke ciki wato Earth.


Moon shine wata na biyar wajen a girma a cikin watannin da su ke cikin solar system. Watan da ya fi kowane girma a cikin solar system shine Ganymede, sai Titan, sai Callisto, sai IO, sannan kuma sai Moon.

Moon ya na da fadin kilomita dubu uku da dari hudu da saba'in da shida (3,476km) wato kusan fadin kasar China kenan wanda takeda fadin kilomita dubu uku da dari biyar da talatin (3,530km). A cikin wata akwai kura (dust), kuma akwai tsaunuka da tuddai.

Daga wata zuwa duniyan nan akwai nisan kilomita dubu dari uku da tamanin da hudu da dari hudu (3,84400km). Wato nisan tsakanin duniyan nan da wata zai dauki duniyan nan sau talatin.

Wata ya na da layer guda biyu kaman haka:
1. INNER AND OUTER CORE
2. MANTLE AND CRUST

Inner da outer core sun kunshi sinadarin iron. Mantle da crust kuma sun kunshi sinadaran Magnesium, da Oxygen, da kuma Silicon.

A ranar 20, ga wata July na 1969, kumbo mai suna APOLLO 11 ya sauka a cikin duniyar wata. Wannan kumbo kasar Amurkace ta aikashi cikin sarari musamman domin ya sauka a cikin duniyar wata - kuma ya sauka kaman yanda aka tsara.

Wata cikinsa yanada yanayi kaman na duniyan nan kaman yanda mu ka gama bayani a sama cikinsa akwai tuddai da tsaunuka. Mu na iya cewa wata da duniyar Earth dukkan su duniyoyi ne da su ke da yanayi kusan iri daya - sai dai wata dan karami ne sosai idan aka kwatanta girmansa da Earth wannan ya sa wata satellite ne ba planet ba.

Abun da ya sa aka ce wata shima duniyace, saboda ya na da yanayi irin na duniya musamman duniyoyin bangaren terrestrial wato su Mecury, da Venus, da Earth, da kuma Mars. Doron kasa na cikin duniyar nan da na wata duk kusan iri dayane. Sai dai a cikin wata akwai karancin sinadarin iskar Oxygen, ga kuma yawaitar sinadaran iska masu illa ga lafiyar dan Adam.

Tsakanin duniyar nan zuwa wata akwai gurare a sama wadanda ake kira da sunaye daban daban wanda ya danga da nisansu, misali kamansu Exoshpere, da Troposphere, da kuma Thermosphere da sauransu. Wadannan guraren za mu yi bayaninsu a takaice cikin ikon Allah.

Wadannan guraren sune:
1. Troposphere
2. Stratosphere
3. Mesosphere
4. Thermosphere
5. Exosphere

Troposphere yana sama a nisan kilomita sha daya (11km) tsakaninsa da doron kasa. Samada shekaru dari da kirkiro jirgin sama, wanda ya kawo sauki da canji ga harkokin tafiye tafiyen dan Adam da kayaiyakinsa na harkokin rayuwar yau da kullum. Jirgin sama na kasuwanci da na zirga zirgan mutane da na sauran shugabanni yana tafiyane a daidai nisan da ake kira Troposphere idan ya tashi sama. Haka kuma daidai tsayin tsaunin dayafi kowane tsauni tsayi a duniya wato Mount Everest.

Stratosphere yana sama daga nisan kilomita sha daya zuwa hamsin (11-50km). A daidai inda ake kira Stratosphere ana samun jiragen sojoji (military plane), da jirgi mara matuki na leken asiri, da balan balan (weather balloon) na auna yanayi, da kuma mutane masu yin nitso daga cikin sararin samaniya zuwa doron kasa, wadanda ake kira Sky divers, ko Highest sky divers a turance.

Mesosphere yana can a sama daga nisan kilomita hamsin zuwa tamanin (50-80km). A daidai tsakanin nisan mesosphere wasu rocket suke tsayawa sannan su fado kasa. Sai kuma satellite din dake kan rocket din ya ci gaba da tafiya shi kadai har sai ya kai nisan da ake bukata, sannan zai bude fuka fukansa - daga nan sai ya fara zagaye duniya.

Thermosphere kuma yana nan a nisan kilomita tamanin zuwa dari bakwai (80-700km). Thermosphere ana samun satellite kamansu International Space Station a wajen sannan kuma akwai tsananin zafi. Kalmar 'thermo' tana nufin zafi, ko kuma abu mai zafi. International Space Station yana sama a nisan kilomita dari hudu (400km).

Exosphere yana can sama daga nisan kilomita dari bakwai zuwa kilomita dubu goma (700-10,000km). A daidai Exosphere kuma babu komai, kawai fili ne wato vaccum space. Sai kuma iska mai karfi dake wajen. Anan nisan ana iya samun satellite masu yawa.

Hasken da muke gani na wata idan dare yayi yana zuwa daga rana ne. Idan hasken ya sauka a cikin doron kasa dake cikin wata sannan watan yayi reflect na hasken zuwa duniyan nan da muke ciki.

Za mu dakata anan dafatan ana amfanuwa da darusan kimiya da fasaha da muke rubutawa a shafinan. Mun gode sai mun sake ganinku.

No comments

Powered by Blogger.