Menene subject da object?
Subject da Object ababe ne guda biyu wadanda a duk cikakkiyar jimla ta magana sai an samesu a ciki, ko kuma dole sai an yi amfani dasu. Kowane yare bawai sai turanci kadai ba, dole ne a samu subject da object a cikin jimlar magana. Subject shine mai yin aikin, shi kuma object wanda aikin ya fada akansa, ko kuma wanda akayi aikin akansa.
Subject yana nufin mai yin wannan aikin, shi kuma object wanda aikin ya fada kan sa. Misali, idan na ce 'Na sha ruwa'. Anan ni da nasha ruwan ni ne Subject saboda ni na yi aikin. Shi kuma ruwa shine wanda aikin ya fada akansa, ko kuma shine akayi aikin a kansa. Sannan sha kuma shine aikin da nayi.
A wajen da ake amfani da object da subject suna ko wakilin suna kadai ake rubutawa. Sannan ana iya rubuta sunan mutum, ko sunan wani abu, ko kuma dai wakilin sunansa. Sunan mutum ko dabba ana iya saka su a wajen subject da object. Misali, Nura yana wasa da kwallo, ko kuma ace kwallo ta shiga raga. Anan subject da object basu da bambamci saboda anyi amfani da sunan asali.
Amma a wajen wakilin suna abun ba haka yake ba a turanci. Subject sune: shi (he); da ita (she); da ni (I); da mu (we); da kai, ko ke, ko ku (you); da ita ko shi (it) amma abu mara rai; da kuma su maza ko mata (they).
Wakilin sunan wanda aiki ya fada musu kuma wato Object sune: shi (him); da ita (her); da ni (me); da mu (us); da kai, ko ke, ko ku (you); da ita, ko shi (it) amma abu mara rai; da kuma su maza ko mata (them). He da him suna nufin shi namiji. She da her suna nufin ita mace. I da me suna nufin ni mace ko namiji. We da us suna nufin mu maza ko mata. You yana nufin kai daya, ko ke daya, ko kuma ku dayawa maza ko mata. It yana nufin shi ko ita, amma abu mara rai. Sannan they da them kuma suna nufin su dayawa maza ko mata.
Misali:
1. Saminu send a letter to his friend.
Wato: Saminu ya aikawa abokinsa wasika.
A misalin dake sama, Saminu shine wanda yayi aikin wato shine subject. Abokinsa kuma shine wanda aikin ya fada kansa wato object.
2. The driver drove his car to garage.
Wato: Wato matuki ya tuka motar sa zuwa gareji.
Matuki shine mai aikin (subject), motar kuma ita ce wanda akayi aikin akan ta.
3. Nura went metting and met his friend called Hassan.
Wato: Nura ya je taro ya hadu da abokinsa wanda ake kira Hassan.
Nura shine mai aikin abokinsa Hassan shine wanda aiki ya fada masa.
Bawai dole bane kowace jimla sai ansamu mai aiki da kuma wanda aiki ya fada masa. Akwai jimlolin da zasu bada ma'ana mai kyau wanda cikinsu zaka samu babu subject, da object. Misali, inda mu ka ce an yi ruwan sama - duk wanda ya ji wannan kalmar ya san abun da ake nufi, amma fa a cikinta babu mai aiki da wanda aikin ya fada masa. Mai aiki wato subject, da wanda aiki ya fada masa wato object dole ne a ambaci sunansu ko wakilin sunansu a cikin jimla.
4. An athlete kicks a penalty to goalkeeper.
Wato: dan wasan ya bugawa mai tsaron raga bugun penalty.
5. Policemen raid a blackmarket.
Wato: 'yan sanda sun shiga kasuwar bayan fage.
6. A politician wins the election.
Wato: dan siyasa ya yi nasarar zaben.
7. Farmer harvested his beans and maize.
Wato: manomi ya girbe wake da masararsa.
Zamu dakata da misalan anan sai mun zo da darasi na gaba, wanda a cikin sa za mu ci gaba da bayani akan sassan magana - tare da misalansu. Amma kafin sannan bari mu barku da wasu tambayoyi guda hudu wadanda zaku amsa su domin mu tabbatar da cewa ana amfanuwa da darusan koyan turanci da ake karantawa a shafin nan.
Muna so ku yi comment da mai aiki, ko kuma wanda aiki ya fada musu a ciki tambayoyin guda hudu da suke sama - domin tabbatar da cewa ana fahimta kuna ana amfanuwa da abubuwan da ake karantawa a shafin nan.
Haka kuma zaku iya tambaya akan duk abun da babu gane ba, mu kuma zamu baku amsa, idan Allah yasa mun san amsar tambayarku. Sannan daga karshe kuma muna fatan zamu sake ganinku a shafin nan. Mun gode, ahuta lafiya!

Leave a Comment