Ya ya girman duniyar Earth ya ke?
Earth ita ce duniya ta uku daga rana, kuma ta biyar wajen girma a cikin duniyoyin da suke cikin solar system gaba daya. Duniyoyin da su ka fita girma su ne Jupiter, da Saturn, da Uranus, da kuma Neptune ne. Earth ita ce duniya mafi girma a duniyoyin da suke bangaren terrestrial, tanada girma fiye da Mecury, da Venus, da kuma Mars. Amma wai shin ko ka san ya ya girmanta ya ke ne?
Kaman yanda mu ka sani duniya tanada siffar kwallo wato sphere. Sannan kuma su sphere ko kwallo sunada zagaye mai kamada zobe ko kuma round. A fagen lissafi idan ana bukatar a gano girman abun da ya ke da siffar circle ko round wato kaman zobe, ana amfani da tsayin radius na su ne.
Kafin musan menene radius, za mu fara da bayanin diameter. Diameter shine wani dogon layin wanda ya raba duk wani abun da yakeda siffar zobe, zuwa gida biyu. Misali, idan ka dauki garegare ko zobe ka rabashi daidai zuwa gida biyu, layin da ya raba tsakanin rabin da ya ke sama, da wanda ya ya ke kasa shine diameter a turance. Radius kuma shine rabin diameter, wato idan ka raba diameter zuwa gida biyu, shine zai baka radius. Misali, idan ka raba zobenka gida biyu, sai ka samu layin da ya raba su gida biyu, yanada tsayin millimetre goma sha biyar (15mm). Radius na wannan zoben shine bakwai da rabi (7.5mm). Circumference shine layin da ya kewaye zobenka gaba daya - wato kewayen zobe gaba daya shine circumference.
Idan za a gano tsayin wannan kewayen zoben ana amfani da wata formula wato C=2π. C yana nufin circumference, kuma unit nashi shine metre. π shine pi harafine daga cikin harufan Greek, kuma yana daidai da 3.1416, ko kuma 3.14 a takaice. Radius shine r, kuma unit nashi shine metre. Sannan pi (wato π) shi ba shi da unit. Misali, zobenka yana da radius 7.5mm ga yanda zakayi sai ka gano tsayin circumference na zobenka. C=2x3.14x7.5 tsayin circumference na zobenka shine 47.1mm.
Radius na duniyar Earth a daidai equator shine kilomita dubu shida da dari uku da saba'in da takwas (6, 378km) kaman yanda yazo a cibiyar zuwa sarari ta Goddard ta NASA. Kodayake Earth tanada siffar kwallo, yayin da take kewayawa radius nata yakan canza a lokacin da ta dan jirkice daga equator, to radius nata daga pole zuwa pole shine kilomita dubu shida da dari uku da hamsin da shida (6, 356km) wato banbancin kilomita ashirin da biyu kenan (22km).
Idan akayi amfani da wadannan tsayin na radius din da suke Earth, circumference na Earth a equator shine kilomita dubu arba'in da saba'in da biyar (40, 075km) haka kuma daga pole zuwa pole shine kilomita dubu arba'in da kilomita guda takwas (40, 008km).
Wannan shine abun bincike ya nuna game da saurin da duniyar Earth takeyi a shekara, da wata, ko kwanaki, da sa'o'i kaman yanda yazo a shafin space.com da fatan ana amfanuwa da rubuce rubucen da mukeyi a shafin nan. Duk wanda yake da tambaya ko kuma yin sharhi a game da darusan cikin shafin nan, yana iya ajiye comment nasa a wajen comment dake can kasa.
Daga karshe kuma muna godiya akan ziyara da kukeyi a shafin nan kullum. Da fatan zaku gaiyato 'yan uwa da abokan arziki zuwa shafin nan. Mun gode, sai mun sake ganinku.

Leave a Comment