Yanda Zaka Bude Boss A Game Din Mortal Kombat 3 Champion



Mortal Kombat wasa ne na fada a tsakanin mutane biyu wanda ya buge dan uwan sa, shike da nasara. Mun yi wasu darusa akan yanda ake buga game din SEGA a wayar Android, da kuma yanda akeyi a wayar Symbian, sannan kuma mun nuna hanya mai sauki da ake more game din mortal kombat a wayar Android - tare da yanda ake brutality da combo a game din.

A baya mun yi bayanin yanda ake kama gidan karshe a wasu gyama gyamai kaman su SONIC, da Tiny toon, ta hanyar amfani da wasu 'yan dabaru ko kuma wasu cheat da ake shigar da su a gyama gyaman. A yanzu kuma zamu nuna muku yanda ake bude Shao Khan wato boss din Mortal Kombat, tare da mataimakin sa mai suna Motaro.

Yana da kyau ku sani cewa ba'a iya bude boss da mataimakin sa a lokaci daya - saboda dukkan su, su biyun hotun nan su a waje daya suke futowa. Saboda haka sai dai ka bude daya kabar dayan a rufe, wato idan ka bude Shao Khan babu dama ka bude Motaro - hakama idan ka bude Motaro babu daman bude Shao Khan. Sannan kuma bazaiyiwu ka dauki Shao Khan ko Motaro kace zakabi layin boss dasu ba. Sai dai idan ku biyu kuke yin game din wato two player.

Shima mataimakin boss din wanda akafi sani da Motaro duk wani hani da wata doka akan boss to shima ta shafe shi, saboda shida boss din duk ba'a yi musu Finish him!. Kuma suma basa yin brutality, ko fatality, ko animality, ko babality, da sauran su, kaman yanda sauran 'yan wasan su keyi, kuma suma ake musu.

Ba sai mun tsaya mun bata lokaci akan yi muku wasu bayanai da kun riga da kun san su ba - kawai kuyi kasa ku cigaba da karatu domin koyan yanda abun yake cikin sauki. Yana da kyau ku karanta wannan tutorial sosai, saboda cheat din sai anyi sauri ko gaggawa yake aiki. Yanzu dai ga bayanin yanda ake yi yana kasa.

Ga Yanda Akeyi
1. Da farkon fari ka bude game din Mortal Kombat 3 da ke wayar ka. Yana budewa sai ka danna Start kaman yanda kake yi a farkon shiga game din, har sai ya kawo ka wajen da kake gani a jikin hoton da ka kasa.


2. Yana nuno maka wajen sai ka danna (A) da (C) sai ka danna sama. Sannan ka danna (B) sai ka sake danna sama, sannan ka sake danna (B) da (A) da kasa. Amma fa lokacin da zaka danna wadannan abubuwan ana so kayi gaggawa wajen danna su.


3. Kana gama danna wadannan abubuwan nan take zakaga wasu rubutu a jere daga can kasa sun fito sun yi sama. Idan ka lura zakaga rubutun sun kusan kai su biyar - sai kayi kasa ka shiga KILLER CODES a cikin jerin rubutun.

4. Kana shiga zakaga sunan boss din da mataimakin sa. Kaman yanda mu kayi bayani a sama sunan boss din shine Shao Khan. Shi kuma mataimakin nasa shine Motaro. A Mortal Kombat mataimakin boss ba boyaiye bane, domin shine wannan mai jikin dokin. Daga nan duk wanda kake son budewa sai ka bude shi. Misali, idan kana so ka bude boss wato Shao Khan sai kazo daidai sunan shi za ka gan shi a Disable wato akulle ko arufe. Idan zaka bude shi kawai sai ka danna baya ko gaba akan Disable din, za ka ga ya koma Enable. Kana yin haka shikenan ka bude boss.

5. Haka kuma idan kana so ka bude mataimakin boss din wato Motaro wannan mai jikin dokin. Shima sai ka zo daidai kan sunan shi za ka gan shi a Disable, kawai sai ka danna gaba ko baya za ka ga yakoma Enable, idan kayi haka shikenan ka gama komai! Sai kayi kasa ka shiga EXIT.



6. Kana yin yanda muka nuna maka a sama, kawai ka je ka fara yin game din za ka ga hoton wanda ka bude ya futo a wajen daukan mutane. Kaman yanda ake iya gani yanzu haka duk mun bude su - amma daban daban muka bude su, ba a lokaci daya muka bude su ba.



7. Daga karshe kuma wajen danna wadannan abubuwan ana danna sune da sauri kaman yanda mu kayi bayani a sama. Sannan kuma idan kayi bai yi ba, sai kayi reset na game din, sai ka sake yi, idan anan din ma bai yi ba, kayi hakuri ka sake restart na game din har sai ka samu yayi. Domin nima sai da nayi haka kusan sau biyar zuwa bakwai sannan ya dauka. Yana da kyau kayi hakuri ka sake yi sannan kuma cikin gaggawa ko sauri.

Idan za kabi layin boss, babu daman kayi amfani da boss din ko mataimakin sa, sai dai ka dauki wasu 'yan wasa na daban kaman yanda mu kayi bayani a sama.

Za mu tsaya anan ina ga dan wannan bayanin zai wadatar saboda mun nuna komai tare da bayani daidai gwargwadon hali. Da fatan wannan dan karamin tutorial din zai amfane ku wajen more gyama gyamai a cikin kwanciyar hankali.

Sannan kuma kuna iya share na wannan bayanin a Facebook ko dandalin sada zumunta na WhatsApp domin sanar da wasu abokan ku suma su zo su amfana da rubuce rubucen shafin nan. Mun gode da kawo ziyara shafin nan a huta lafiya, sai mun sake ganin ku!🎮

No comments

Powered by Blogger.