Yanda Zaka Kama Gidaje A Game Din Sonic
Munyi bayanin yanda ake kama gidan karshe a Tiny toon, sannan mu kayi bayanin yanda ake bude boss din Mortal Kombat 3, da kuma yanda ake more game din SEGA a wayar Android da kuma Symbian cikin sauki. Wannan yasa za mu cigaba da bayani, akan yanda ake kama gidaje a Sonic.
Kaman dai yanda muka sani kowane game yana da tashi wahalar kafin kaje gidan karshe. Bawai gidan karshe ba, akwai gidaje masu nisan gaske wadanda zuwan su akan sha wahala sosai. Saboda nisan su da kuma wahalar su, shiyasa zamu nuna yanda ake kama gidaje a game din Sonic.
Da ikon Allah a tutorial din nan da za mu yi, za mu nuna yanda ake kama gidaje a game din Sonic, ta hanyar amfani da wasu 'yan dabaru da kuma wasu code a cikin sauki babu wani bata lokaci. Saboda aikin babu wahala ko kadan, sai dai ana so mutum yayi da sauri.
Yana da kyau mu sani cewa hanyar nan da zamu nuna wasu code ne zamu danna. Idan mun danna su daidai, shine za mu samu dama mu fara kama gidajen da muke so. Sannan wannan hanya da zamu nuna a wannan tutorial din tana aiki ne a game din talabijin da kuma na waya, amma fa a game din Sonic kadai - kai dai cigaba da karatu kawai!
Ga Yanda Akeyi
1. Da farko, ka tabbata kana yin game din nan a wayar ka, ko kuma kana yin sa a talabijin. Abun nufi anan shine ka zamo ka iya tafiyar da game din. Abun da zakayi shine kawai ka bude game din naka wato Sonic. Kana bude shi sai ka danna Start kaman yanda kake yi ko yaushe idan zaka more game din.
2. Har sai kazo wajen da zaka daddanna wannan cheat din. Kana zuwa wajen zakaga Sonic din ya leko da kan sa, yana girgiza yatsar sa. Kana zuwa wajen kaman yanda ake iya gani a hoton da ke kasa.
3. Yana nuno maka wajen da kake gani a jikin hoton dake sama, kawai sai ka danna (A) ka rike shi kada ka daga. Daga nan sai ka fara danna sama, sai ka danna kasa, sai ka danna baya, sannan ka danna gaba, amma fa kada ka daga (A) din. Sannan sai ka danna Start.
4. Kana danna su kaman yanda muka ce kayi, nan take zasu nuno maka sunan gidajen game din gaba daya a jere daya bayan daya. Sai ka shiga gidan da kake so ka fara morewa.
5. Bari muyi misali ta hanyar kama jan gida, wato gidan nan mai suna SPRING YARD ZONE STAGE 1.
6. Kaman dai yanda kuke gani a wadannan hotunan da suke sama, muna more jan gida, wanda muka kama. Amma fa idan ba kamawa muka yi ba sai mun sha wahala sosai, kafin mu zo gidan.
Gidan da muka kama shine gida na bakwai, bayan Green hill zone 1, da 2, sai ka kashe boss na Green hill a zone 3. Daga nan zaka fara gidan wuta wanda akafi sani da Marble zone, kuma shima yana da zone 1, da 2, sannan ka kashe boss nashi a zone 3. Idan muka lissafa kenan sai ka kashe boss guda biyu, atakaice sai ka wuce gidaje shida kenan. Sannan sai kazo nan gidan wato SPRING YARD wanda muka kama yanzu.
Wannan duk ana yine a game din SEGA, ko da yake nasan wasu sunfi sanin shi da suna Sonic. Wadannan 'yan dabarun tun shekarun baya da suka wuce, nasan wasu sun san su, kuma sun haddace su, sai dai muyi tutorial din nan a matsayin tunatarwa ga wasu.
Anan ya kamata mu tsaya ina ga bayanin ya wadatar haka. Muna fatan dan karamin tutorial din nan zai yi amfani ga masu yin game domin koyan cheat a cikin sauki.
Daga karshe kuma kuna iya yin tambayoyin ku a wajen comment dake kasa akan abubuwan da baku gane ba. Zaku samu amsa idan Allah yasa mun sani. Fatan ana amfana da rubuce rubucen dake cikin shafin nan.
Kuna iya tura rubutun nan ta Facebook ko dandalin WhatsApp domin wasu abokan ku su karanta suma su amfana. Mun gode da kawo ziyara shafin nan, sai mun sake ganin ku a huta lafiya!🎮

Leave a Comment