Yanda Zaka Kama Gidan Karshe A Game Din Tiny Toon



Wasan na'ura na Tiny toon, wasa ne mai dadi ga kuma kayatarwa ga mai yin sa. A shekarun baya lokacin muna yara mun sha biyan kudi domin muyi irin wadannan gyama gyaman, ko kuma a koya mana su a shaguna da sauran guraren yin game. A yanzu kuma saboda cigaban fasahar zamani irin wadancan gyama gyaman da muke kallo a talabijin duk zaka iya samun su a cikin wayoyin hannu. Kama daga wayoyin Symbian zuwa na zamani wato Android da iPhone kai harma da wayar Java za'a iya yin su.

Kaman dai yanda muka sani a kowane game ana shan wahala kafin aje gidan karshe, ko kuma wani gida mai nisan gaske, saboda nisan gidan ko wahalar da ake yi kafin aje wannan gida. Wannan tsarin haka yake a game din Tiny toon, wato shima ana shan wahala sosai kafin aje gidan karshe. Saboda yawan gidajen sa da kuma nisan su ga kuma wahalar isa gare su.

To idan Allah yaso, a tutorial din nan zamu nuna muku yanda ake kama gidaje a game din Tiny toon, ta hanyar amfani da wasu code cikin sauki. Wannan dabara babu wahala kaman yanda muka nuna muku a yanda ake kama gidaje a game din SONIC, da kuma yanda ake bude boss din Mortal Kombat 3 cikin sauki. Ko kuma ku shiga nan domin koyan yanda ake more Mortal Kombat 3 Champion a wayar Android.

Yana da kyau mu sani cewa wannan hanyar da za mu bi wasu code ne zamu shigar kaman yanda mu kayi a baya. Sannan mu samu daman kama gidan da muke so. Kuma wadannan abubuwan da zamu nuna a tutorial din nan yana aiki a game din talabijin da kuma na wayoyin hannu. Amma fa a Tiny toon kadai ake aiki da shi domin nashi ne shi kadai.

Ga Yanda Akeyi
1. Da farko, ya zamanto daman ka kware a fannin buga game, saboda gidan karshen nan akwai wahala sosai. Abun da zakayi shine kawai ka bude game din naka kaman yanda ka saba yi.



2. Idan ka zo wajen shiga game din sai kayi kasa ka shiga PASSWORD. Kana shiga PASSWORD za su nuna maka wajen kama gidaje.


3. Yana bude maka wajen saka PASSWORD din, sai kasa wannan code din wato RQBQ HZZQ XKBQ HZZW XGDZ. Kana gama saka code din sai ka shiga END kawai.


4. Nan take za su nuno maka wajen shiga gidaje a daidai wajen shiga gidan karshe. Sai kawai ka danna Start, ko A, ko B, ko C. Amma a sani a cikin wadannan madannai guda hudu da muka ce, kawai guda daya zaka danna. Saboda duk wanda ka danna shiga gidan kawai za kayi.


5. Daga nan sai ka shiga gidan karshen, kana shiga za kaga ya kawo ka gidan karshe kaman yanda kuke iya gani a wadannan hotunan da suke kasa. Sai ku cigaba da more game naku yanda kuke so.




6. Idan kana so ka kama gidan karshe a Tiny toon hanyar da muka nuna a sama ita za ka bi daki daki, kaman yanda mu ka yi bayani. Ina ga bayanin yanda ake kama gidan karshe a game din nan ya kammala. Saboda har mun shiga gidan karshen mun fara more game din kaman yanda ake gani a hotunan da suke sama.

A sani kowane gida a game din nan code nashi daban ne, wato code din gidan daya, gidan daya kawai yake iya budewa, haka zalika code gidan biyu baya iya bude gidan uku. Amma code din da muka bayar a sama shine code na gidan karshe. Zaka iya shiga kowane gida bayan ka kama gidan karshe da code din da muka bayar a sama.

Nan shine karshen tutorial din nan sai kuma mun hadu a tutorial na gaba. Kada kumanta kuna iya tura wannan tutorial din zuwa ga abokan ku a shafukan sada zumunta da muhawara na internet domin gaiyato su zuwa shafin nan.

Fatan za ku cigaba da kasance cikin koshin lafiya, haka kuma muna fatan zaku cigaba da kasancewa tare da shafin nan a ko da yaushe domin cigaba da samun tutorial da sauran mahimman bayanai game da kimiyya da fasaha. Mungode kuhuta lafiya!🎮

No comments

Powered by Blogger.