Saukar da applcation din PixelLab

A yanzu mutum ba ya bukatar computer ko amfani da softwarer mai suna adobe, ko sauran softwares na computer domin gyaran hoto, kaman canza background, da yin rubutu mai salo daban daban na zamani, da kuma canza launin hoto da rubutu da sauran gyare gyaren hoto. Domin wayoyin zamani wato smartphone su na iyayin wadannan aiyukan da a shekarun baya sai dai a yi su a cikin computer.

Wayoyin Android su na iya dayawa daga cikin aiyukan da a can baya sai dai a yi su da computer, domin a kullum su ma ana kara musu fadin kwalkwalwa da karfin yin wasu aikace aikacen da a baya basa iya yi. Wannan application din ya na daya daga cikin applications na gaba gaba wadanda ake aiki da su a waya domin gyaran hoto.


Kaman dai yanda muka sani a baya gyaran hoto bawani bakon abu bane a computer. Amma fa sai dai a yanzu wayoyin zamani da akafi sani da smartphones su na neman kwace wa computer wannan aikin. Duk da haka dai mutane sun fi sabawa da gyaran hoto a computer saboda akwai softwares na computer masu yawa wadanda kacokan aikinsu shine gyaran hoto. Haka shima PixelLab aikinsa kenan. Amma fa sai dai shi a waya ake aiki dashi.

Shin ko ka san yanda ake saka custom font a pixellab?

PixelLab application ne wanda ake amfani da shi a wayoyin zamani ko muce smartphones. Gaba daya amfanin PixelLab a wayoyin zamani shine gyaran hoto, kaman yin rubutu, da tsara hoto tare da yin kwalliya, da saka wasu abubuwa da kuma hada logo, da banner ta kamfani na website.

PixelLab application ne mai saukin tafiyarwa akan wayoyin Android, bashi da wahala wajen aiki, kuma yana da sauri, ga kuma sauki idan ka iya aiki dashi. Yana da abubuwa daban daban kaman emoticons da backgrounds da font styles wadanda musamman kawai antanade su ne kawai domin kayatar da hoto.

A daya hannun kuma yana dauke da fonts, wato styles na rubutu daban daban samada arba'in(more than 40) kuma duk zaka iya amfani dasu. Wani abun ban sha'awa anan shine wasu font styles din na larabci ne duk dasu yake zuwa a cikin sa. Suma duk antanade su dan tsarawa da kuma kayatar da hotuna domin burge mai aiki da application din.

Shiga nan domin koyan yanda ake canza background din hoto a pixellab

Ka na iya gyara hotonka da wannan application din a smartphone naka, ta yanda idan wani ya gani zai yi tunanin da computer ka yi wannan gyaran. Wannan application din kyauta ake saukar dashi, kuma ya na budewa a wayoyi masu kananan version kama daga version 4 zuwa manyan version.

Saukar da PixelLab
1. PixelLab ga masu Android.


Amfanonin PixelLab su ne:
1. Saka backgroud.
2. Cire backgroud.
3. Yin rubutu akan hoto.
4. Yin rubutun larabci da style.
5. Hada banner da logo.
6. Hada tambarin kungiya.
7. Hada poster da hoto.
8. Rage girman hoto.
9. Kara girman hoto.
10. Juya hotuna.
11. Tsayar da hoto.
12. Saka emoticons daban daban.
13. Yin rubutu da style kala daban daban.
14. Yana kunshe da kaloli masu yawa.

Idan ka na bukatar wannan application din ka yi domin saukar dashi a wayarka ta Android, kuma a kyauta ake saukar dashi ba tare da ka biya ko sisi ba ko ka yi wata wahalaba. Kawai kai dai ka tabbata ka tanadi isasshiyar data a wayarka.

Ya kamata mu tsaya anan - sai kuma a gaba idan mun zo da tutorial akan yanda ake aiki dashi. Muna fatan wannan dan karin haske game da wannan application din yayi mana amfani wajen editing na hotuna a wayoyin mu.

Muna bukatar ku cigaba da gaiyato mana abokai da sauran jama'a domin suma suzo su bada tasu gudunmuwar ko kuma su karanta wasu bayanan domin koyan wasu abubuwa. Kuna iyayi mana gyara a duk inda kukaga munyi kuskure, hakama kuna iya baiyana mana ra'ayoyin ku a wajen comment dake kasa, Mun gode, ahuta lafiya.

No comments

Powered by Blogger.