Saukar da application din Vidmate

Vidmate application ne na Android, wanda ake amfani da shi yau da kullum wajen shiga internet domin saukar da bidiyoyi, ko kuma a kallesu kai tsaye a online. Akwai Vidmate na Android, kuma akwai na sauran wayoyi kaman iOS na kamfanin Apple. Vidmate dai application ne wanda gaba daya amfaninsa shine a saurari media file, kaman kallon bidiyo, ko sauraron audio.

Shin, ka na so ka koyi yanda ake bude blog a kyauta?.

Vidmate ana amfani da shi a saukar da bidiyoyi a shafukan internet kamansu Instagram, da YouTube, da facebook da sauransu. Hakama ana iya saukar da sautin murya wato audio daga cikin wani bidiyo a shafukan bidiyo kaman YouTube da Instagram. Wato application din nan zai ba ka dama ka dakko sautin murya kadai daga jikin wani bidiyo ba tare da shi bidiyon ka dakko shi gaba daya ba.


Idan ana maganar saukar da abubuwa a shafukan internet Vidmate ya fi KeepVid saukin aiki. Saboda shi idan ka na saukar da bidiyo a YouTube ya na saukar maka da komai na bidiyon, wato shi Vidmate ya na saukar maka bidiyon da komai na shi gaba daya. Abun da mu ke nufi shine Vidmate ya na dakko bidiyon tare da sauran file na bidiyon kaman substitle da audio. Wanda a KeepVid wani lokacin ma iya bidiyon kadai ya ke dakkowa ba a jin sautin muryar bidiyon.

Substitle shine wani rubutu wanda za ka gani ana magana ya na futowa a jikin screen ko talabijin ya yin da ake kallon bidiyo, ko shirye shirye a wata tashar satellite. Subtitle shi ya ke fassarawa mai kallo abun da ake cewa a cikin shirin da ya ke kallo. Misali idan ka na kallon fina finan India, kai ba ka jin yarensu, sai dai kaita kallo kawai. Amma za ka ga idan sun yi magana da indiyanci, sai a rubuta fassaran abun da su ke cewa da turanci. Wannan shine substitle to shima ana samun shi a cikin bidiyoyin YouTube, kuma ba shi da nauyi, sannan a KeepVid ba a iya dakkoshi.

Vidmate ana amfani da shi offline kaman yanda ake aiki da sauran media player. Wato ana iya kallon bidiyoyin da su ke cikin memory card, da kuma na kan waya a cikinsa. Haka kuma ana iya sauraron audio wadanda su ke kan memory da waya a cikin Vidmate duk a offline.

Shiga nan domin saukar da shahararren application na gyaran hoto mai suna PixelLab, da kuma sanin yanda ake aiki dashi.

A cikin Vidmate za ka iya amfani da shafukan sada zumunta kaman Facebook da Instagram ka sada zumunci da abokanka na Instagram da Facebook a kyauta kaman yanda aka saba.

Saukar da Vidmate
1. Vidmate ga masu Android

Idan ka na so ka saukar da Vidmate a wayarka, shiga daya daga link din da mu ka bayar a sama sai ka saukar da shi, sannan ka yi install din ka fara aiki da shi. Wannan application din ya na da amfani ga masu amfani da smartphone wajen sauraron audio da kallon bidiyo a wayar Android da sauran smartphone.

Bari mu tsaya a nan sai kuma mun zo da bayani akan wani application din. Mu na fata za ku ci gaba da kasancewa da shafin nan a ko da yaushe! Sai mun sake ganinku! Mun gode a huta lafiya!

No comments

Powered by Blogger.