Saukar da game din Zuma Revenge a wayarka ta Android
Wasan game din Zuma Revenge ba boyaiyen wasa bane a duniyar wasannin game. Haka kuma ba wani game bane mai wahala sosai - zuma game ne mai sauki da kuma saurin daukewa mutane kewa.
Shi ko kasan game din Fighting tiger kuwa? Kasan yanda ake more shi? Kana so ka koyi yanda zaka more shi a wayar ka ta Android cikin sauki? To maza maza shiga nan, domin koya da kuma saukar da shi a wayar ka.
Muna iya cewa Zuma wasa ne na na'ura da kusan kowa ya san shi, kuma bashi da wahala wajen koya. Wannan game din game ne mai dadin yi ga kuma saurin shiga rai, saboda yanda kamfanin sa suka tsara shi daidai da zamani, kuma a saukake.
Saukar game din a nan
1. Zuma revenge ga masu Android
2. Zuma revenge ga masu Android
3. Zuma revenge ga masu iPhone da iPad
Game din Zuma dai kyauta ake saukar dashi a waya har ma da computer. Wannan game din akwai nau'ukan shi daban daban kama daga na kananun wayoyi zuwa na manyan wayoyi. Akwai game din Zuma wanda ake morewa a computer, sannan kuma akwai na wayoyi irinsu iPhone, da Android, da Symbian da kuma na Java. Sannan dukkansu kusan tsarin game din daya ne, sai dai akwai dan banbanci kadan.
Game din nan yana da saukin koya kuma bashi da wahala domin kana iya koyan shi a cikin lokaci kadan. Haka kuma bashi da nauyi, sannan yana budewa a kowace waya cikin wayoyin iPhone, da Android. Hatta masu amfani da tsofi da kuma kananan version zasu iya more wannan game din a wayoyin su cikin sauki. Kaman wayoyi masu version 4, zuwa abun da yayi sama suna iya more wannan game din.

Yaya ake yin game din Zuma?
Game din Zuma ba ya bukatan wani dogon bayani, da wani dogon sharhi ga mai koyo a lokacin da zai fara koya. Abun da ake bukata wajen mai koyo shine kawai ka iya jera kala iri daya a kusa da kusa. Domin a cikin game din wasu kwallayene masu dauke da launuka daban daban. Wadannan launukan sune Ja (red), da Shudi (blue), da Tsanwa wato Kore (green), da Ruwan dorowa (yellow) wato Rawaya, da Ruwan hoda (violet), da sauran launuka.
Idan ka na so ka yi nasara a wasan din duk inda ka ga kwallo daya ko fiye da daya, kawai ka jefa wata kwallon mai irin wannan launin a kusa da su. Misali, ka hango wasu kwallaye biyu ko uku masu launin Ja - yanda za ka yi, shine kawai sai ka harba musu kwallo mai launi irin nasu wato Ja kenan. Nan take za ka ga sun kone, kai kuma ka samu maki. Yawan kwallayen daka kona yawan adadin makin da za ka samu. Idan kuma ka kona kwallayen gaba daya, shikenan ka wuce gidan sai su kai ka gida na gaba.
Daga tsakiya kuma akwai wani dodo wanda yake cinye wadannan kwallayen. Idan har ka bari ya fara cinye kwallayen to kai ne za ka yi game over, wato kai ne za ka fadi kenan sai ka sake yi.
Idan ka na sha'awar more game din barawon mota, wanda akafi sani da Gangster a wayarka ta Android, shiga nan.
Saukar da game din Zuma a nan
Wannan Zuman na masu amfani da wayar Android ne kadai. Saboda idan ka na bukatar saukar dashi a wayarka ta Android, kawai ka shiga nan. Sai ka saukar dashi domin more sa a wayarka. Bayan ka gama saukar da shi sai ka yi install nashi, sannan ka ci gaba da morewa!
Ka na gama install, sai ka bude shi sannan ka fara morewa. Mu na fatan za ka more game din lafiya tare da wayarka. Sai dai fa abun da za muce anan shine ana sara ana duban bakin gatari. Wato ana yin game ana tunawa da battery ka da a shanye caji gaba daya.
Nan shine karshen darasi akan game din Zuma revenge. Sai kuma wasu darusan akan wasu gyama gyaman na daban, Mun gode! ;)

Leave a Comment