Yanda ake bude domain a kyauta

Kafin muyi nisa a darasin nan idan baka iya bude email ba, ka shiga nan, sai ka koyi yanda ake budewa. A baya munyi bayanin menene domain, da kuma amfanin sa ga website - acikin bayanin mukace akwai domain na kyauta, kuma akwai na kudi. To a wannan darasin zamu nuna muku yanda ake bude domain na kyauta.

Domain na kyauta sune zakaga karshen su kaman haka .tk da .cf da .ml da .ga da .gq da dai makamantan su. Misalin domain na kyauta shine zaka ganshi kaman wannan nurablog.ga da sauransu. Amma .com da .net da .org da .gov da .ng da .edu da ire irensu su bana kyauta bane. Su kuma .com.ng da .com.in da com.bd da sauran ire irensu suma na kudi ne. Amma suna da saukin farashi ba kamansu .com, da .net ba. Saboda su wadancan masu com.ng ko com.ng da com.bd suna da alaka da sunan kasar da mutum yake. Misali com.ng na 'yan Nigeria, com.in shi kuma na 'yan India ne, com.bd kuma na 'yan bangladesh ne.

Kayan Aikin Sune:
1. Adreshin Email
2. FireFox
3. Chrome.

Wadannan browser guda biyun wato da Chrome, da FireFox amfanin su daya ne. Idan ka na da daya za ka iya yin komai da ita, ba sai ka saukar da dayan ba. Shi kuma email da shi za m uyi amfani mu yi rajistar domain din mu, wanda za mu yi amfani da shi a duk lokacin da za mu yi shiga cikin control panel na domain din mu.

Ga yanda ake budewa
Da farko, kafin mufara komai yana da kyau ka saukar da browser daya daga cikin browser biyun damuka lissafo a sama. Bayan ka saukar dasu sai kayi installing nasu ka budesu. Idan kuma kana da su kawai kabude su. Ka na budewa sai ka shiga wajen saka URL Address ka rubuta www.freenom.com sai ka taba OK ko kuma GO, sai kajira ta bude maka shafin da zaka bude free domain.


Tana tabude maka shafin Freenom daga tsakiya zakaga wani box a cikinsa an rubuta Find a new FREE domain. Sai ka shiga wannan box din ka rubuta sunan domain din da kakeso. Misali, idan inaso inbude nurablog.ga to nurablog kadai zansa banda .ga idan munje shafin gaban sai muzabi .ga din. Kaman yanda nayi kaima haka zakayi. Kana saka sunan da kakeso sai ka taba inda aka rubuta Check Availability.



Daga nan, zata kawoka wajen da zakaga an rubuta Get one of these domain. They are free! zakaga sunayen domain kaman .tk da .ml da .ga da .cf da kuma .gq sai ka dauki guda daya acikinsu. Zamu dauki mai .ga muyi misali dashi. Daga nan sunan zai koma nurablog.ga.



Ka duba kusa da domain din da zaka dauka zakaga Get it now!.


Daga nan zakaga wajen yakoma Selected. Sai kayi sama ka shiga Checkout.



Kana gama zaban domain din, bayan ka danna Checkout, zasu kawoka wajen da zaka zabi tsawon lokacin da domain din naka zaiyi yana aiki kafin yayi expire. Sai ka shiga kusa da inda aka rubuta Period, wato wajen 3 Months @ FREE, sai ka zabi tsawon lokacin da kakeso domain naka yayi yana aiki kafin yayi expire. Amma lokaci mafi tsawo shine shekara daya, babu daman da zaka zabi shekara biyu, sai dai kasa da shekara daya ko kuma watanni sha biyu. Idan ka shiga sai kazabi 12 Months @ FREE, wato shekara kenan. Amma fa idan kazabi 1 year zasuce sai kabiya kudi, 12 Months @ Free kuma babu komai kyauta yake.



Kana zaban tsawon lokacin sai ka shiga inda aka rubuta Continue.


Kana shiga Continue zasu kai ka wajen da zakasa email naka. Sai kasa email naka a inda aka rubuta Please enter your email address and Click Verify to continue to the next step. Sai kasa email naka ka taba Verify My Email Address.


Kana saka email naka nan take zasuce sun tura maka sakon verification link acikin email naka. Sai kaje ka bude sakon kafin awanni ashirin da hudu (24hours).


Daga nan sai kaje email naka kabude sakon zakaga link din acikin sakon.


Kana shiga sai ka bude sakon kayi kasa kadan zakaga wani link aciki. Sai ka shiga wannan link din da kagani. Kana shiga link zai dawo da kai cikin shafin da kake rajistar domain naka, wajen Review & Checkout.


Kana zuwa wajen sai kayi kasa ka cike wannan form din kaman haka:
First name: Nura
Last name: Mahdi
Company name: NULOAD
Address 1: Rahamawa
Zip code: 820001
City: Katsina
Country: Nigeria
State/Region: Katsina
Phone number: 08012345678
Password: ##**99
Confirm password: ##**99

Wadannan bayanan danayi amfani dasu a sama, misali ne nayi na yanda ake cike form din da bayanai na. Kaima sai kayi amfani da naka bayanan ka cike form din domin mallakar domain naka na kyauta.

Bayan kagama cikewa sai kayi tick akan inda aka rubuta I have read and agree to the Terms & Conditions. Daga nan sai ka danna Complete order.





Kana danna Complete order nan take zasu nuna maka Order confirmation naka. Sannan suce maka Thank you for your order. You will receive a confirmation email shortly. Nan take zakaga lambarka ta order a inda suka rubuta Order number is sai kayi kasa ka danna inda aka rubuta Click here to go to your client Area.


Client area shine a matsayin control panel na domain naka. Bayan kagama da matakan nan na sama zasu kawoka cikin client area naka, zakaga first name naka, daga can sama. Bayan ka kammala komai sai kadawo ka sake duba cikin email naka, zakaga wannan sakon da sukace zasu turo maka.


Yauwa, yanzu dai dukkan bayani ya kammala! Saboda haka tutorial din yazo karshe. Zamu tsaya anan saboda munyi bayanin abun gaba daya, sai kuma bayani na gaba akan yanda ake hada domain da hosting. yana da kyau musani a domain kyauta ba'a iya zaban 1 year, sai dai a zabi 12 months. Kuma ba'a zaban abun da yawuce 12months saide kasa dashi.

Muna fatan, ana amfanuwa da tutorial din da ake karantawa a shafin nan. Da fatan wannan bayanin zaiyi anfani wajen koyan yanda ake bude domain na kyauta. Mun gode ahuta lafiya!!

4 comments:

  1. Please ga email dinanan .
    manjasaminaka@gmail.com

    ReplyDelete
    Replies
    1. Kadan yimin replying idan ka gani

      Delete
    2. To akkaramakallahu, sai yanzu na samu wannan comment din, dan Allah amun afuwa

      Delete

Powered by Blogger.