Yanda Ake Dawo Da Abubuwan Da Aka Goge A Wayar Android Da Dumpster App
Dumpster application ne na Android, wanda ake amfani dashi wajen dawo da abubuwan da aka goge bisa kuskure a waya - kaman yanda akeyi a computer. Application din nan yana aiki ne kaman yanda Recycle bin yake aiki a computer. Idan ka lura duk abun da ka goge a computer zakaga yaje cikin Recycle bin ya zauna. Zakaga duk abubuwan da kagoge sun koma cikin Recycle bin sun zauna. Sannan kuma babu su a cikin memory, idan kanaso kadawo dasu, sai ka shiga Recycle bin kayi undo ko restore nasu. Wato kaje kadawo dasu yanda suke kaman ba'a taba goge su ba. Idan kuma kagoge su a cikin Recycle bin shikenan sun goge gaba daya a computer.
Dumpster kana gama install nashi a wayarka nan take zai fara aiki. Wato bayan kagama install nashi duk abun da kagoge zaije cikinsa ya zauna. Wannan zaisa kasamu kwanciyar hankali ko da kayi kuskuren goge wasu file naka da kake matukar so. Saboda zaka iya dawo dasu a duk lokacin da kaso. Inde ba ka shiga cikin Dumpster din ka goge su gaba daya ba.
Kana gama install na application din zakaga ya hada wata sabuwar folda mai suna Dumpster a kan memoryn wayarka. Abubuwan da kagoge cikin wannan foldar zasu dawo su zauna. Sannan sai ka shiga cikin application din kayi restore nasu.
A sani Dumpster yana cika, wato akwai adadin abubuwa ko nauyin da zaikai kaga idan kagoge abubuwa basa komawa cikin application din saboda babu wajen da zai ajiyesu acikinsa. Kenan duk lokacin da kayi kuskure ka goge wani file yana da kyau nan take kaje kayi restore nashi. Saboda kar application din ya cika ya dena aiki.
Bayan kagoge abubuwan ka zaka iya dawo dasu, haka kuma zaka iya gogesu gaba daya yanda baka da daman dawo dasu. Idan kagoge wani file yakoma cikin Dumpster, sai kaje cikin Dumpster din ka sake goge shi - shikenan yabar kan wayarka gaba daya.
Application Din Da Ake Bukata:
Dumpster

Ga Yanda Akeyi:
1. Da farko, ka saukar da wannan application din a link din da muka bayar a sama. Bayan ka saukar dashi sai kayi install nashi. Kana gama install nashi sai ka bude shi.

2. Bayan ka bude shi sai ka jira, har sai sun nuna maka Welcome to Dumpster!. Suna nuna maka haka sai ka taba inda aka rubuta I AGREE dake can kasa.

3. Kanayin haka zai kawo ka shafin gaba wanda shima duk kusan kalanshi daya da na farkon, anan kuma sai ka taba inda aka rubuta GO BASIC yana kasa da wajen TRY PREMIUM.

4. Kanayin yanda mukace kayi, zakaga takawo ka cikin application din.

5. Bayan kagama install na application din ka budeshi, sai kadawo ka gwada goge wani abu kagani shin application din yana aiki. Zanyi misali da wasu file da zan gogesu acikin wata folda mai suna Upload.

6. Cikin foldar akwai abubuwa guda goma sha biyu, kuma gaba dayan su zan goge, sannan daga karshe mu dawo da su yanda suke.

7. Munyi marking nasu gaba daya kaman yanda ake iya gani a jikin hoton dake kasa.

8. Bayan mun gama marking nasu, zamu gogesu gaba daya su bar kan memory card din daga baya mu dawo da su.

9. Kaman yanda ake iya gani a hoton dake kasa, mun goge abubuwan cikin foldar gaba daya. Yanzu cikin foldar babu komai, zamu shiga matakin dawo dasu.

10. Bayan mun gama goge su mataki na gaba shine na dawo da abubuwan da muka goge a farko kaman ba'a taba goge su ba. Bayan kagama goge abubuwan sai kadawo ka sake bude application din a karo na biyu. Kana bude application din zakaga duk abubuwan da ka goge a jere a cikin application din. Daga sama kusa da inda aka rubuta Dumpster akwai wani arrow karami sai ka taba kanshi.

11. Kana taba kan arrown zakaga ya nuna maka wasu foldodi, da sauran zabuka. Ka duba cikinsu sai ka taba inda aka rubuta Folders.

12. Kana tabawa zakaga application din ya nuno maka foldodin da kagoge abubuwa acikin su.

13. Daga nan sai ka taba kan foldar da kakeso kadawo da abubuwan da suke cikinta wadanda ka goge a baya, kaman yanda mukayi misali mun goge abubuwan cikin folda mai suna Upload. Idan ka taba kan wannan foldar sai ka rike har sai application din yayi marking na foldar. Kanayin marking na foldar, daga can sama ta bangaren dama, zakaga wani arrow sai ka taba kanshi.

14. Kana taba kan wancan arrown zakaga sun nuna maka cewa duk abubuwan da kagoge sun koma inda ka goge su. Wato suna nufin duk abubuwan da ka goge sun dawo!

15. Sai ka dawo cikin memoryn ka zakaga duk abubuwan da kagoge sun dawo kaman yanda suke da farko, kama ba'a taba goge su ba.

16. Idan kuma kanaso kagoge su gaba daya, daga wayarka yanda bazasu sake dawowa ba, ga yanda zakayi. Ka bude application din sai kayi marking na abubuwan da kagoge kaman zaka dawo dasu, sai ka taba alaman kwandon shara dake sama ta bangaren dama kusa da wannan karamin arrown.

17. Kana yin haka zakaga duk sun goge gaba daya daga wayar taka.

Wadannan matakan da muka nuna suke abi idan za'a dawo da abubuwan da aka goge a wayar Android. Kada a manta kaman yanda muka fada a farkon darasin nan, munce wannan application din yana cika wato akwai adadin abubuwan da yake dauka idan suka kai wannan adadi shikenan zai tsaya da aiki.
Amma shawara anan ita ce idan kagoge abu bisa kuskure kayi sauri anan take kaje kadawo dasu. Saboda kar application ya cika ya dena aiki baka sani ba. Hakama kuma ko da kagoge abu idan kanaso yabar wayarka gaba daya, sai ka shiga cikin application din ka goge shi, kaman yanda mukayi bayani a baya.
Akwai wasu application da dama da ake amfani dasu idan za'a dawo da abubuwan da aka goge a waya. Wasunsu na kyauta ne wasunsu kuma sai anbiya wani abu. Wannan application din da mukayi bayani akan sa shima, akwai bangaren da sai anbiya kudi ake iya cigaba da more shi.
Zamu dakata anan sai munzo da wani tutorial din da fatan ana amfanuwa da abubuwan da ake karantawa a shafin nan. Zaku iya sharing na wannan post din da sauran post da kuke karantawa a shafin.
Mun gode, da zuwa shafin nan!

Leave a Comment