Yanda ake hada bidiyon slideshow a wayar Android

Bayan mun rubuta tutorial akan yanda ake ragewa bidiyo nauyi, da yanda ake ciro sauti a cikin bidiyo, da yanda ake karawa bidiyo sauri da sauran tutorial. A yau mun zo da wani tutorial din akan bidiyo. Wato yanda ake hada bidiyon slideshow a wayar Android.

Slideshow shi ne bidiyon da za ka gani ana hadawa da hotunan cikin waya. Slideshow shi ne album din hoto wanda aka tarasu aka hada bidiyo da su. To a tutorial din mu na yanzu za mu nuna yanda ake hada slideshow. Domin hada slideshow ka na bukatar kayan aiki kuma ga sunan mun kawo sunansu a kasa.

Kayan aikin su ne:
1. Hotuna
2. Photo Slideshow with Music

Ga yanda ake yi
1. Kafin mu yi nisa sai a tanadi kayan aiki, kuma ga su nan mun kawo link din da za a saukar da su a sama. Ko da ya ke application guda daya ake bukata, sai kuma hotuna. Sai ka saukar da application din ka yi install dinsa, sannan ka budeshi. Ka na budeshi za ka ga CREATE SLIDESHOW WITH MUSIC, da VIEW SLIDESHOW.


2. Idan ka na so ka duba slideshow din da ka hada sai ka shiga VIEW SLIDESHOW.


Idan ka shiga za ka ga slideshow da ka hada. Idan kuma farkon bude application din ne kuma ba ka hada slideshow ko daya ba, za ka ga an rubuta Album not Created yet, sai ka dawo baya.


3. Ka na dawowa baya, sai ka shiga CREATE SLIDESHOW WITH MUSIC.


4. Ka na shiga wajen za ka ga foldodi da hotunan cikinsu. Za ka ga foldodin a bangaren hannunka na hagu, kuma su na jere daya akan daya. Hotunan kuma za ka gansu a bangaren hannunka na dama.


5. Yanda za ka hada slideshow din shine, sai ka taba foldar da hotunan su ke cikinta. Ka na taba kan foldar za ka ga maki ✔ ya baiyana akanta. Sannan daga dayan gefen wato bangaren dama za ka ga hotunan cikin foldar. Sai ka taba kan hoton da za ka sa a slideshow din za ka ga 01 ya futo a jikin hoton. Idan kuma ka kara taba kan hoton za ka ga rubutun ya koma 02. Haka za ka yi har sai ka yi marking din duk hoton da za ka hada slideshow din da shi. Sai ka duba can sama daga bangaren hannunka na dama sai ka taba inda aka rubuta DONE.


6. Ka na taba DONE din za ka ga application din ya kawoka wajen ARRANGE PHOTOS. Sai ka yi arrange din hotunan sannan ka sake taba DONE.


7. Ka na taba DONE din za ka ga application din ya kowaka PREVIEW. Wato wajen da za ka ga yanda application din ya ke tsara slideshow din. Sai ka zabi transition din da ka ke so bidiyon ya na nuna hoton. Daga kasa kuma za ka ga Shine, da Jalous, da Whole, da Separt da sauransu. Daga kasansu kuma za ka ga wajen zaban frame.


8. Idan za ka zabi frame daga can kasa za ka ga frame kuma an yi marking akan na farkon. Sai ka jawosu daga bangaren dama zuwa bangaren hagu za ka ga frame kala daban daban. Sai ka taba kan wanda ka ke so za ka ga marking ya futo a kansa.

9. Bayan ka zabi frame din daga kasan hotunan slideshow din za ka ga alamar zanen camera, da edit, da music da kuma agogon a karshe, sai ka taba agogon.


10. Ka na taba agogon za ka ga wajen Select Duration ya baiyana. Idan ka dubu za ka ga 1.0 second, da 1.5 second, da 2.0 second, har zuwa 4.0 second. Daga nan sai ka zabi tsawon lokacin da ka ke so kowane hoto zai yi lokacin da ka hada slideshow din.


11. Wajen transition din hotunan ma haka ake yi bayan ka gama tsara transition din slideshow, tare da zaban frame din bidiyon, sai ka taba DONE, wanda ya ke can sama ta bangaren hannunka na dama.


12. Ka na taba DONE din za ka ga application din ya rubuta ma ka Please wait your creation will be on process!! Sai ka jira ya gama process din.


Sannan za ka ga process din ya fara daga 1%, sai ka jira har sai ya gama, wato har sai ya kai 100%.


Application din ya na gamawa zai nuna ma ka MY STORY, kuma a wajen za ka ga slideshow din da ka gama hadawa.


13. Daga nan sai ka dawo baya ka shiga VIEW SLIDESHOW. Ka na shiga za ka samu bidiyon da ka gama hadawa.


Wadannan su ne matakan da ake bi idan za a hada slideshow a wayar Android. Ya na da kyau ka yi amfani da hotunan cikin wayarka wadanda su ke budewa daidai da screen din wayar.

Sannan kuma za a ka iya saka background music a slideshow din a lokacin da ka shiga preview sai ka shiga wajen music wanda ya ke kusa da zanen agogo.

Har ila yau ya na da kyau a sani cewa akwai wasu hanyoyin da ake bi a hada slideshow a wayar Android. Wannan hanyar da mu ka nuna dayace daga cikinsu, kuma mai sauki.

Za mu dataka a nan tun da aiki ya kammala, sannan duk mai neman karin bayani, ko kuma wanda ya ke da tambaya ya je can kasa wajen comment ya rubuta, zai samu amsa idan Allah ya so.

Da fatan ana amfanuwa da tutorial din da ake karantawa a shafin nan. Sannan mu na fatan sake ganinku tare da sauran abokanku domin su ma su zo su karanta abubuwan da ake rubutawa a shafin nan. Mun gode, sai mun sake ganinku, a huta lafiya.

No comments

Powered by Blogger.