Saukar da gyama gyaman Gangster a wayarka ta Android
More game a waya wata hanyace wanda take daukewa mutum kewa a lokacin da baya aikin komai. Yin game abu ne mai dadi, da kuma kayartawa ga mai yi. Idan ka na yin game a wayarka, zai na dauke maka kewa a lokacin da baka shiga dandalin sada zumunta na internet ba.
Shi ko ka san game din Fighting tiger kuwa? Ka san yanda ake more shi? Ka na so ka koyi yanda za ka more shi a wayarka ta Android cikin sauki? To maza maza shiga nan, domin koya da kuma saukar da shi a wayar ka.
Game din Gangster ko kuma muce game din barawon mota, kuma muna iya kiran shi a matsayin karamin game din Grand Theft Auto wato G.T.A a takaice. Game ne dake dauke da abubuwan mamaki da kuma na ban sha'awa - saboda game ne mai dadin yi, da kuma daukar hankali.
Gangster game ne da aka tsara shi daidai da zamani. Ya na dauke da kayan aiki masu yawa wadanda mai yin game din zai yi amfani dasu a cikinsa. Akwai tsararren gari mai kyau, tare da hadaddun shagu nan siyar da kaya kamar jini, da makamai idan naka sun kare. Za ka samu kudi mai yawa ta hanyar yin mission.
Akwai mission masu yawa a cikin game din, na farko farkon za ka samu su na da sauki sosai. Sai dai idan ka yi nisa ne za ka fara haduwa da masu wahalar gaske. Za ka iya samun kudi da maki a game din ta hanyar bin dokokin game din, da kuma bin mission daya bayan daya.
Ga sunan gyama gyaman a jere
Gyama gyaman su na da yawa, kuma dukkansu kamanninsu da tsarinsu iri dayane, wannan ya sa muka kawo guda biyar da su kafi shahara a duniyar game. Ga su nan a jere a kasa sai ka saukar da wanda kakeso.
1. Grand Fight Gangsters 3D
Na farko shine Grand Fight Gangsters wannan game din za ka ganshi kaman barawon mota na asali, saboda yanda aka tsara birane da garuruwan da suke cikin game din. Za ka ga motoci da mutane su na ta harkokinsu, wani ya yi gabar wani kuma ya yi yamma.
2. Real Gangster Crime 1
Na biyu kuma shine Real Gangster Crime 1, daga jin sunan na biyun nan kasan cewa za a yi gumurzu da kuma aikata lefuka a game din. Akwai mutane azzalumai a cikin wannan game din wanda za ka ga su na tafiya da makamai a hannunsu, kuma su na cutar mutane. Kai ma idan ka tsaya wasa su na iya gamawa da kai - idan kuma ka gama da su za ka iya daukan makamansu da kudin da yake jikinsu.
Shin ko ka san game din Zuma revenge? Ka san yanda ake more shi? Kaima ka na so ka koyi yanda za ka more shi a wayarka ta Android cikin sauki? To maza maza shiga nan, domin koya da kuma saukar da shi a wayarka.
3. Real Gangster Crime 2
Na ukun kuma shine Real Gangster Crime 2 wato ci gabane na Real Gangster Crime 1 shima akwai artabu, da gumurzu, da nuna jarumta, da rashin tsoro. Kwarewarka wajen iya tafiyar da game din shi zai baka daman samun kudi da kiyaye lafiyar ka a game din.
4. Gangster Town
Na hudu kuma shine Gangster Town shima dai wannan game din ba a barshi a baya ba, domin an tsara shi, da gine gine na zamani, ga motoci, da mashina, ga mutane kowa ya na harkar gabansa, sannan kuma ga shagunan da za ka yi siyaiya a cikinsu.
5. Auto Theft Gangsters
Sai na biyar din kuma wato Auto Theft Gangsters shima wannan game din kaman sauran akwai 'yan sanda da suke bada tsaro a cikin gari, da sauran gurare ka na yin laifi nan take za ka ga sun kamaka. Har-wa-yau idan ka yi mission za ka samu kudi da maki.
Shi ko ka san sabon game din guje guje, da tsallake tsallake mai suna Subway Surfers San Francisco? Ka san yanda ake more shi? Ka na so ka koyi yanda za ka more shi a wayarka ta Android cikin sauki? Yi gaggawa ka shiga nan, domin koya da kuma saukar da shi a wayarka ta Android.
Idan ka lura lokacin da kake yin daya daga cikin wadannan gyama gyaman da muka kawo a sama, za ka ga alamar taswira wanda take nuna maka hanyar da za ka bi. Duk wani mission da za ka yi a jikin taswira za ka ga sun nuna maka ga hanyar da za ka bi. Wani lokaci kuma za ka ga wata jar alama a jikin taswirar wanda take nuna maka wajen da za ka tsaya. Sannan kuma idan ka na tafiya za ka ga su na rubuta maka sauran tafiyan mita na ka karaso wajen da mission din yake.
Gaba daya gyama gyaman basu da wata wahala idan ka nutsu, kuma ka bi abun a hankali, daya bayan daya. Wani mission din lokaci za a baka wanda ake bukatan ka yi sauri, ka gama wani aiki. Wani mission din kuma za ka je ka ceto wani ko wata ko wasu daga hannun wasu 'yan ta'adda. Wannan yake nuna cewa za ka iya amfani da makami a cikin game din.
Bari mu dakata anan fatan za a more gyama gyaman lafiya, sannan kuma muna fatan ana yi, ana kula da batteryn waya. Domin idan ka biyewa wadannan gyama gyman ka na iya gamawa da cajin wayarka gaba daya.

Leave a Comment