Yanda Ake Aiki Da Xender A Wayar Android

Xender application ne na Android, wanda aka tsara shi domin ayi amfani da shi wajen musayar abubuwan da suke cikin waya. Xender application ne wanda ake amfani dashi domin turawa da kuma karban abubuwa daga wata wayar zuwa wata wayar a saukake.

Ba kaman Bluetooth ba, Xender tana tura abu da sauri. Kuma tana amfani da sadarwar wifi idan za tayi aiki.

Shiga nan domin sanin PixelLab, da kuma amfanin sa. Ko kuma ka shiga nan idan kana so, ka koyi yanda ake canza background na hoto cikin sauki a wayar ka ta Android.

Xender application ne mai sauki wajen tafiyar wa, kuma yana aiki a manya da kananun wayoyin Android. Kyauta ake saukar da Xender kuma tana da sauri wajen tura abu. Sannan lokacin da kake tura wa wani abu, ko kuma ake tura maka wani abu, ba'a so wayoyin ku suyi nisa da junan su. San samu ku ajiye wayoyin ku a jere ba tare da wata tazara mai tsawo ba.

Ga Yanda Ake Aiki Da Xender
1. Da farko, ka saukar da Xender a Playstore, ko kuma ka shiga link din nan - sai ka saukar da ita. Bayan ka gama saukar da ita, sai kayi install nata. Kana gama install nata sai ka bude ta.


2. Kana budeta za kaga ta nuno maka application da gyama gyaman da kayi install nasu a wayar ka. Sai ka duba daga kasa a tsakiya zakaga SEND, da RECEIVE. Sai ka shiga guda daya a cikin su, wanda zaka turawa abu shima sai ya shiga dayan ba wanda ka shiga ba. Idan ka shiga SEND wanda zaka turawa abu kuma sai ya shiga RECEIVE.


3. Bari muyi misali idan zaka turawa mutum wani abu a Xender. Ka shiga RECEIVE, wanda zaka tura masa abu sai ya shiga SEND.


4. Kana shiga RECEIVE zakaga wayar ka ta fara searching, wato ta fara nemo Xender wanda zaka tura masa abu. Tana cikin searching din zakaga ta nuna maka suna wancan wayar da zaka turawa abu. Sai ka taba kan sunan wayar kaman yanda ake iya gani a hoton dake kasa mun yi searching na wayar da zamu tura mata abubuwa wato Tecno H5.


5. Kana yin haka zakaga takama wancan wayar sai mai wancan wayar yayi accept ko kuma ita da kanta za tayi accept din. Daga nan zakaga kasa da sunan wayar da kakamo an rubuta Waiting for sender. Kana ganin haka sai ka taba inda aka rubuta I WANT TO SEND, zaka gan sa yana daga kasa.


6. Kana yin haka zakaga Xender ka ta nuna maka gaba daya application din da kayi install nasu a wayar ka. Kaman yanda take nuna maka farkon shigowa kafin kayi connect na Xender ka da Xender wata waya.


7. Zamu tura Opera Mini zuwa Tecno H5 da muka yi searching nata a farko. Kai ma sai ka taba kan hoton abun da kake so ka tura zakaga Xender tayi marking nashi. Sai kazo kasa ka taba inda aka rubuta SEND.


8. Kana taba SEND nan take zakaga abun da ka tura ya tafi.


Haka ake amfani da Xender kaman yanda mu kayi bayani a sama. Wannan hanya da muka nuna itace ake bi idan za ayi aiki da wannan application din. Xender tana da sauki da dadin tafiyarwa a wayoyin Android.

Idan akwai inda baku gane ba kuna iya tambaya a wajen comment dake can kasa. Fatan ana amfanuwa da rubuce rubucen da muke wallafawa a shafin nan.

Muna godiya akan ziyara da kuke kawowa shafin nan ba dare ba rana!

No comments

Powered by Blogger.