Menene international space station?
International space station ko kuma ISS a takaice. ISS tashace a acikin sararin samaniya wanda kasashen duniya da su ka ci gaba a fannin fasaha da kere kere su ka hadu su ka su ka ginata. Tashar ISS ita ce abu ma fi girma, kuma ma fi nauyi wanda dan Adam ya kera, sannan ya harba cikin sarari, ya ke aiki a cikin sararin samaniya. ISS ta na nisan kilomita dari hudu (400km) tsakaninta da doron kasa. Saboda haka ta na low earth orbit, ko kuma LEO a takaice.
ISS tashace wanda aka ginata, kuma aka harbata cikin sarari saboda binciken kimiyya. Akwai dakin binciken kimiyya (laboratory) a cikinta, wanda mutane shida su ke aiki a cikinsa.
A ranar 20 ga watan Nuwamba na shekarar alif da dari tara da casa'in da takwas (20th November, 1998) aka harba tasahar ISS cikin sarari wato yau sama da shekaru ashirin ta na aiki a cikin sararin samaniya. Sannan kuma ana tsammanin za ta kara shekaru kusan goma a nan gaba ta na aiki, wato za ta kai shekarar dubu biyu da talatin (2030) ta na aiki a cikin sarari.
Kafin tashar ISS akwai tashar sarari, wato ba tashar ISS bace tashar sarari ta farko. Kafin a ginata taraiyar Soviet karkashin jagorancin kasar Russia sun kera tashar sarari mai suna Mir. Bayan shekaru kadan ta na aiki tashar Mir ta kama da wuta, sannan ta fado cikin teku. Tashar Mir ta fara aiki a shekarar 1986, kuma a lokacin da ta ke aiki Mir ta na daukan mutune ukune kadai, kafin ta samu matsalar gobara ta fado a 2001. Toyohiro Akiyama dan Jaridane, dan kasar Japan a shekarar 1990 ya kai ziyara Mir. Bayan nanne masu sha'awar yawon bude ido zuwa sarari su ka fara ziyartar Mir.
Skylab shine dakin binciken kimiyya na farko wanda kasar America ta kera, sannan ta harbashi cikin sarari a 1973. Skylab daga jin sunansa za ka iya gano abun da sunansa ya ke nufi, wato dakin binciken da ya ke cikin sarari. Skylab ya samu goyon baya tare da taimakon kudi da kayan aiki daga gwamnatin America, da sauran cibiyoyin zuwa sararin na duniya.
Lokaci zuwa lokaci wasu ma'aikatan ana canzasu, domin samun hutu. Sannan kuma ma'aikatan da su ke cikin ISS su na bincike ana aika musu ruwa da abinci da iskar numfashi (oxygen) daga kasashen Russia da America, saboda su ne jagororin wannan tafiyar. Wani lokacin kuma ruwan recycling nashi ake, wato idan su ka sha ruwan su ka yi fitsarinsa sai a yi amfani da wasu sinadarai a tace shi, sai su sake amfani da shi.
Tashar ISS ta na da wasu hannaye wadannan hannayen su na da yawa, kuma kowane hannu amfaninsa daban ne da dan uwansa. Misali akwai hannun da aikinsa kawai idan an harbo mutum daga duniyar nan ya na karasowa kusa da tashar ISS din nan take wannan hannun zai kamo kumbon da mutum ya ke ciki ya kai shi wajen da ya kamata ya tsaya.
Tashar ISS ta na samun wutar lantarki daga hasken rana (solar), kuma cikinta akwai batura masu yawa, masu karfi sosai, wadanda lokacin da ISS ta ke kewaye duniya idan duniya ta rufe mata hasken rana nan take za su fara aiki. Saboda rashin wuta zai sa ta fado, idan ta fado kuma an yi babbar asara. Saboda an kashe makudan kudi wato miliyan daloli aka kashe wajen ginata.
Tashar ISS aikin manyan hukumomin zuwa sarari na duniyane, wato NASA (ta America), da Roscosmos (ta Russia), da JAXA (ta Japan), da ESA (European Space Agency), da CSA (ta Canada) su ne su ka hadu su ka kerata. Ga sunan kasashen daya bayan daya America (US), da Canada, da Japan, da hukumar zuwa sarari ta taraiyar turai (European Space Agency) wacce take da wakilcin kasashe kaman haka Burtaniya (UK), da France, da Germany, da Belgium, da Italy, da Holland (ko Netherlands), da Denmark, da Norway, da Spain, da Switzerland, da kuma Sweden da sauransu.
Tashar ISS ana amfani da ita ne domin bincike kimiyya musamman abun da ya shafi sarari, da taurari, da duniyoyi, da yanayi da sauransu. A America tashar ISS ana samun sadarwa da ita a Mission Control da ya ke Houston, da Texas, da New Mexico da antenna mai tsayin kafa sittin (60-foot antenna). Sauran kasashen ma su na da makamancin wannan tsarin domin samun sadarwa da wakilansu da su ke cikin ISS su na aikin bincike.
Tashar ISS ta na zagaye duniya gaba daya a cikin minti casa'in da uku (93minutes) a takaice. Sannan ta na gudun kilomita bakwai da digo sittin da shida duk second daya (7.66km/s), wato daidai da gudun kilomita dubu ashirin da bakwai da dari shida duk awa (27,600kmph). ISS ta na da tsayin mita saba'in da biyu da digo takwas (72.8m), da kuma fadin mita dari da takwas da digo biyar (108.5m).
Da fatan ana amfanuwa da darusan da mu ke wallafawa a shafin nan. Duk mai tambaya ya na da daman yinta akan abun da ya shige masa hudu, mu kuma idan Allah ya sa mun sani za mu ba shi amsa.
Mu na godiya akan ci gaba da kasancewa da shafin nan da ku ke yi. Fatan za ku gaiyato mana abokanku su ma su zo su amfana da abubuwan da mu ke wallafawa a shafin nan. Mun gode, a huta lafiya sai mun sake ganin ku.

Leave a Comment