Yanda ake canza salon rubutu a WordPress




Salon rubutu ya na daya daga cikin hanyoyin da zai WordPress ya na daukan hankalin masu ziyara.

Kafin mu canza salon rubutun ga salon da mu ke aiki da shi.


Ga yanda ake canza salon rubuta

1. Da farko ka je ka yi install din plugin mai suna Easy Google gonts. Plugin din cikinsa akwai salon rubutu kusan dari shida (600 fonts).

2. Bayan ka gama install din sa sai ka dawo dashboard ka taba alaman Menu.


3. Ka na taba Menu, za ka ga zabukan cikin dashboard sun baiyana sai ka yi kasa ka taba Appearance.


4. Ka na taba Appearance din za ka ga Themes, da Customize, da Widgets, da Menus, da Header, da kuma Background sun baiyana a karkashinsa, sai ka shiga Customize.


5. Ka na shiga Customize, sai ka yi kasa, ka shiga Google Fonts.


6. Ka na shiga Google Fonts din za ka ga Basic settings, da Advance settings, da kuma Debugging. Sai ka shiga Basic settings.


7. Ka na shiga Basic settings za ka ga Base Topography, da Heading, da kuma Buttons and Inputs, kuma kowanne daga cikinsu an zabi Default font a cikinsa.




8. Daga nan sai ka shiga Basic Topography.


9. Ka na shiga cikinsa za ka ga Default font.


10. Sai ka yi kasa za ka samu System fonts, kaman su Arial, da Calibri da kuma Consolas.


12. Sai ka sake yin za ka ga wasu Google fonts din.


13. A nan kasan za ka ga fonts kaman su ABeeZee, da Abel, da Abhaya Libre, sai ka yi kasa za ka ga sauran font din. Za mu yi misali da font mai suna Charm.


14. Idan za ka seta font din a matsayin wanda za ka yi aiki da shi, kawai ka taba kan font din.


15. Ka na taba kan font din za ka ga an dawo da kai baya. Daga nan sai ka yi sama daga bangaren hannunka na dama ka taba Publish.


Ka na taba Publish sai ka dan jira har sai Publish din ya canza ya koma Published.


16. Ka na yin haka sai ka shiga Preview ka ga yanda font din ya ke.


17. Idan kuma ka na so ka sake canza font din sai ka dawo wajen font din kaman yanda mu ka yi bayani a sama, za ka ga Charm a wajen maimakon Default font.


18. Daga nan sai ka shiga wajen font din ka yi kasa za ka ga wasu font din. Za mu seta Modern Antiqua, sai ka taba kan font din.


19. Daga nan sai ka sake taba Publish, kaman yanda ka yi da farko.


Sai ka jira har sai Publish din ya koma Published.


20. Daga nan sai ka dawo ka sake duba salon rubutun za ka ga ya canza.


wadannan matakan ake bi idan za a canza salon rubutu a WordPress.

No comments

Powered by Blogger.