Yanda ake canza site icon a WordPress

Ga yanda ake yi

1. Da farko ka je ka shiga dashboard na WordPress dinka. Ka na shiga dashboard din sai ka duba can sama daga bangaren hannunka na hagu ka taba alamar Menu.


2. Ka na taba wajen sai za ka ga zabukan cikin dashboard din sun baiyana, sai ka yi kasa ka taba Appearance.


3. Ka na taba Appearance din za ka ga ya nuna Themes, da Customize, da Widgets, da Header, da Background a karkashinsa, sai ka shiga Customize.


4. Ka na shiga Customize din sai ka yi kasa ka sake shiga Site Identity.


5. Ka na shiga Site Identify, sai ka yi can kasa za ka ga Site Icon, sai ka duba kasa da shi kadan sannan ka shiga inda aka rubuta Select Image.


6. Ka na shiga Select Image za ka ga WordPress din ya kawoka cikin Media Library, sai ka taba Upload Files.


7. Ka na taba wajen Upload Files, za ka ga an kawoka wajen upload, sai ka taba Select Files. Sannan kuma kusa da wajen za ka ga an rubuta Maximum upload size: 10MB suggested image dimensions: 512 by 512 pixels.


8. Daga nan sai ka je ka zabo hoton da ka ke so ka daura a matsayin icon na site din ka. Ka na zabo hoton sai ka daurashi.


9. Ka na zabo hoton sai ka jira ya gama upload. Ya na gama upload za ka ga marking ya futo akan icon din. Daga nan sai ka taba Select, wanda ya ke kasa kadan daga bangaren dama.


10. Ka na yin haka za ka ga an dawo da kai baya za ka ga hoton a wajen Crop Image, sai ka yi crop, idan da bukatar yin sa, idan kuma babu bukatar yin sa sai ka shiga Skip.


11. Daga nan za a kawoka wajen Preview na icon din. Idan hoton bai yi ma ka kyau ba, ko kuma ka na so ka ciresa, sai ka taba Remove. Idan kuma za ka canza hoton sai ka shiga Change image.


12. Idan kuma hoton ya yi kyau ya na burgeka, sai ka yi sama, ka taba Publish.


13. Ka na gama publish din hoton sai ka je ka duba icon din za ka ga ya hau icon din blog din ka.


No comments

Powered by Blogger.