Yanda ake seta dark mode a WhatsApp

Dark mode tsarine da mutane su ka rungumi amfani da shi a wayoyinsu a yau. Kasancewa ka na amfani da waya a cikin dare idan screen din ta farine ko kuma ya na da haske ya na iya saka ka ji idonka ba ya son ganin screen din.

Dark mode zai kare idonka daga samun matsalar ido, ko ganin farin haske.

Saukar da WhatsApp a nan
1. WhatsApp ga masu Android
2. WhatsApp ga masu iPhone da iPad

Ga yanda ake setawa

1. Da farko, ka saukar da WhatsApp a Play store ko App store a link din da mu ka bayar a sama. Bayan ka saukar sai ka budeshi, ka sa lambar wayarka da sunanka, sai ka budeshi. Idan kuma ka na da shi a wayarka sai ka bude shi, ka na bude shi, sai ka duba daga can sama ta bangaren dama za ka ga wasu digo guda uku, sai ka tabasu.


2. Ka na tabasu za ka ga wasu zabuka sun baiyana. Zabukan su ne New group, da New broadcast, da WhatsApp Web, da Starred message, da kuma Settings a karshe. Sai ka shiga Settings din.


3. Ka na shiga Settings din za ka ga Account, da Chats, da Notifications, da Data storage usage, da Help da kuma Invite a friend. Sai ka shiga Chats.


4. Ka na shiga Chats, za ka ga Theme, da Wallpaper, da Chat settings, kawai sai ka shiga Theme.


5. Ka na shiga Theme din, za ka ga an zabi Light.


6. Daga nan sai ka cire tick din da ya ke kan Light ka canza shi zuwa kan Dark, sannan ka taba OK.


7. Ka na zaban Dark din za ka ga kalan cikin WhatsApp din ya canza daga haske zuwa mai duhu.


Wadannan matakan su ne matakan da ake bi domin seta dark mode a WhatsApp. Ba wai sai a WhatsApp kadai ake yin aikin da dark mode ba, ana iya da dark mode a sauran application kaman Facebook lite, da Twitter, da WhatsApp, da Instagram sai dai mu na iya cewa matakan da ake bi sun dan banbanta. Daga karshe kuma duk mai tambaya zai iya rubutawa a wajen comment wanda ya ke can kasa.

Za mu dakata anan da fatan ana amfanuwa da tutorial din da ake karantawa a shafin nan. Mu na godiya akan kawo ziyara shafin nan da ku ke yi ba dare ba rana. Sannan mu na fatan za mu sake ganinku a shafin nan

No comments

Powered by Blogger.