Menene adjective?
Koyan turanci kaman kowane yare ya na bukatar fahimtar nahawunsa daki-daki, kaman yanda mu ka yi. A baya mun yi bayanin noun, da pronoun, yanzu kuma za mu ci gaba da bayani akan adjective, wanda dayane daga cikin sassan magana guda takwas na nahawun turanci.
Ma'ana: Nura (matashi ne mai kirki).
2. Muhammad is (strong) boy.
Ma'ana: Muhammadu kakkarfan yaro ne.
3. Fatima was a (beautiful) girl.
Ma'ana: Fatima kyakkyawar yarinya ce.
4. Aliyu is a Nigerian.
Ma'ana: Aliyu (dan Nigeria) ne.
2. Adjective of quantity
3. Possessive adjective
4. Demonstrative adjective
5. Proper adjective
6. Predicate adjective
7. Attribute adjective
Ma'ana: Hafsa (kyakkyawar) mata ce.
6. Abubakar is a kind man.
Ma'ana: Abubakar (mutumin kirki) ne.
7. This is a (big) house.
Ma'ana: Wannan gidan (babba) ne.
Ma'ana: Hafsa ta na da wayoyi guda (guda).
9. (Few) cars were packed.
Ma'ana: An yi parking din motoci (kadan).
10. Muhammad wrote (many) sentences.
Ma'ana: Muhammadu ya rubuta jimloli (da yawa).
Ma'ana: Wannan wayar(ka) ce.
12. (His) father has beaten him.
Ma'ana: Baban(sa) ya bugeshi.
13. (My) house is so small.
Ma'ana: Gida(na) dan karamine.
Ma'ana: (Wannan) yaron dan baiwane.
15. (That) book is mine.
Ma'ana: (Wancan) littafina ne.
16. (Those) iPhones are costly.
Ma'ana: (Wadancan) wayoyin iPhone din ma su tsada ne.
18. British (burtaniya) - Britain (dan burtaniya)
19. Canada (kanada) - Canadian (dan kanada)
20. Nigeria (najeriya) - Nigerian (dan najeriya).
21. Pakistan (fakistan) - Pakistani (dan fakistan).
Ba wai sai mutum ne kadai ya ke daukan wannan sunan ba, hatta kamfanoni ko wani abu da ya ke da asali a wancan garuruwa ko kasashe. Misali, American company employed employees, ma'ana kamfanin amurka ya dauki ma'aikata.
Ma'ana: Malamin (dogo) ne.
23. This guy is (handsome).
Ma'ana: Wannan matashin (mutumin kirki) ne.
24. My wives are (beautiful).
Ma'ana: Matana (kyawawa)ne.
Ma'ana: (Dan kirkin) ya karaso.
26. My (beautiful) wives visited her.
Ma'ana: (Kyawawan) matana sun ziyarceta.
27. The (tall) man is sitting.
Ma'ana: (Dogon) mutumin ya na zaune.
Wadannan su ne adjective da misalansu, sannan ku na iya rubuto ma na na ku misalan a wajen comment da ya ke can kasa. Za mu dakata a nan da fatan a na amfanuwa da darusan da mu ke rubutawa a shafin nan. Idan kuma akwai mai tambaya sai ya yi kasa wajen comment ya rubuta ta za mu amsa, idan Allah ya sa mun sani.
Domin ci gaba da samun darusan koyan turanci a ci gaba da kasancewa da shafin nan. Ku na iya gaiyato ma na 'yan uwa da abokan arziki zuwa shafin nan domin su ma su amfani. Mun gode, sai mun sake ganinku.
Menene adjective?
Adjective ko kuma mu ce baiyanau a takaice. Adjective shine ya ke baiyana suna, ko wakilin suna ta hanyar maye gurbinsu a cikin jimla. Misali, babba (big), ko karami (small), ko mai karfi ko kakkarfa (stronger), ko lusari (coward), ko mai kirki (kind) da sauran su.Misali:
1. Nura is a (kind) guy.Ma'ana: Nura (matashi ne mai kirki).
2. Muhammad is (strong) boy.
Ma'ana: Muhammadu kakkarfan yaro ne.
3. Fatima was a (beautiful) girl.
Ma'ana: Fatima kyakkyawar yarinya ce.
4. Aliyu is a Nigerian.
Ma'ana: Aliyu (dan Nigeria) ne.
Ire-iren adjective
1. Adjective of quality2. Adjective of quantity
3. Possessive adjective
4. Demonstrative adjective
5. Proper adjective
6. Predicate adjective
7. Attribute adjective
1. Adjective of quality
Adjective of quality shine ya ke baiyana karkon mutum ko wani abu.Misali:
5. Hafsa is a (beautiful) woman.Ma'ana: Hafsa (kyakkyawar) mata ce.
6. Abubakar is a kind man.
Ma'ana: Abubakar (mutumin kirki) ne.
7. This is a (big) house.
Ma'ana: Wannan gidan (babba) ne.
2. Adjective of quantity
Adjective of quantity shine ya ke baiyana adadin yawan abu a cikin jimla.Misali:
8. Hafsa has (three) phones.Ma'ana: Hafsa ta na da wayoyi guda (guda).
9. (Few) cars were packed.
Ma'ana: An yi parking din motoci (kadan).
10. Muhammad wrote (many) sentences.
Ma'ana: Muhammadu ya rubuta jimloli (da yawa).
3. Possessive adjective
Possessive adjective kaman possessive pronoun ya ke domin ya na amfani da wakilin suna na mallaka.Misali:
11. This is (your) phone.Ma'ana: Wannan wayar(ka) ce.
12. (His) father has beaten him.
Ma'ana: Baban(sa) ya bugeshi.
13. (My) house is so small.
Ma'ana: Gida(na) dan karamine.
4. Demonstrative adjective
Demonstrative adjective shima kaman demonstrative pronoun ya ke, shima amfaninsa shine nuna wani ko wani abu a cikin jimla. Kuma ana amfani da wadannan kalmomin this, da that, da those, da these, da here, da there da sauransu.Misali:
14. (This) boy is intelligent.Ma'ana: (Wannan) yaron dan baiwane.
15. (That) book is mine.
Ma'ana: (Wancan) littafina ne.
16. (Those) iPhones are costly.
Ma'ana: (Wadancan) wayoyin iPhone din ma su tsada ne.
5. Proper adjective
Proper adjective su ne kalmomin da ake amfani da su domin baiyana sunan wani ko wani abu daga asalinsa, ko daga inda ya samo asali.Misali:
17. America (amurka) - American (ba amurke)18. British (burtaniya) - Britain (dan burtaniya)
19. Canada (kanada) - Canadian (dan kanada)
20. Nigeria (najeriya) - Nigerian (dan najeriya).
21. Pakistan (fakistan) - Pakistani (dan fakistan).
Ba wai sai mutum ne kadai ya ke daukan wannan sunan ba, hatta kamfanoni ko wani abu da ya ke da asali a wancan garuruwa ko kasashe. Misali, American company employed employees, ma'ana kamfanin amurka ya dauki ma'aikata.
6. Predicate adjective
Predicate adjective kalmomine da su ke zuwa a bayan suna ko wakilin sunan da su ka maye gurbinsa.Misali:
22. The teacher is (tall).Ma'ana: Malamin (dogo) ne.
23. This guy is (handsome).
Ma'ana: Wannan matashin (mutumin kirki) ne.
24. My wives are (beautiful).
Ma'ana: Matana (kyawawa)ne.
7. Attribute adjective
Attribute adjective kalmomine da su ke zuwa kafin suna ko wakilin sunan da su ka maye gurbinsa.Misali:
25. The (handsome) guy arrives.Ma'ana: (Dan kirkin) ya karaso.
26. My (beautiful) wives visited her.
Ma'ana: (Kyawawan) matana sun ziyarceta.
27. The (tall) man is sitting.
Ma'ana: (Dogon) mutumin ya na zaune.
Wadannan su ne adjective da misalansu, sannan ku na iya rubuto ma na na ku misalan a wajen comment da ya ke can kasa. Za mu dakata a nan da fatan a na amfanuwa da darusan da mu ke rubutawa a shafin nan. Idan kuma akwai mai tambaya sai ya yi kasa wajen comment ya rubuta ta za mu amsa, idan Allah ya sa mun sani.
Domin ci gaba da samun darusan koyan turanci a ci gaba da kasancewa da shafin nan. Ku na iya gaiyato ma na 'yan uwa da abokan arziki zuwa shafin nan domin su ma su amfani. Mun gode, sai mun sake ganinku.
Leave a Comment