Menene antonyms?

Kalmomi a kowane yare su kan zo da kishiyoyinsu, wato kalmomin da su ke kalubalantar wasu kalmomin. Misali, idan ka ce dogo, kishiyarsa ita ce gajere, ko gundu. Kaman kowane yare turanci ma ya na da irin wadannan kalmomi.

Menene antonyms?

Antonyms kalmomine da su ke kishiyantar wasu kalmomi a turance. Wadannan kalmomin sun hada siffa, ko aiki. Misali, mai aiki da ma ra aiki, ko farin mutum da bakin mutum.

Ire-iren antonyms

1. Graded antonyms
2. Relational antonyms
3. Complementary antonyms

1. Graded antonyms

Graded antonyms su ne kalmomin da su ke da kishiyoyi ko ma su kalubalantarsu sama da daya ko biyu.

Misali:

1. Happy - Sad
2. Health - sick
3. Smart - stupid
4. Small - Big

Abun da ya kamata a fahimta a nan shine wadannan kalmomin akwai wasu kalmomin da su kishiyancesu banda wadanda mu ka rubuta. Kaman wajen Happy mu na amfani da angry, ko unhappy, ko kuma fury - sai wajen Health mu na iya amfani da illness, wajen Smart mu na iya amfani da dumb, ko fool - hakama wajen Small mu na iya amfani da huge, ko bulky da sauransu.

2. Relational antonyms

Relational antonyms kalmomi wadanda su ke da kishiyoyinsu guda daya tak. Wato su ba kaman graded antonyms su ke ba, sannan kuma kusan a na iya cewa su na da alaka.

Misali:

5. Front - back
6. Husband - wife
7. Open - close
8. Come - go
9. In - out
10. Up - down

Relational antonyms idan mu ka lura mu na iya cewa su na da akala, kuma su na kamanceceniya da complementary antonyms wanda za mu yi bayaninsa a kasa.

3. Complementary antonyms

Complementary antonyms su ma kalmomine biyu wadanda su kadai su ke kishiyantar juna, wato idan aka sa wadanda ba su ba ne a wajen to ma'anar ba za ta yi yanda ake so ba.

Misali:

11. Alive - dead
12. Daughter - son
13. Father - mother
14. True - false
15. Male - female

Ga yanda ake aiki da su

16. Musa is (happy) today.
Ma'ana: Musa yau ya na (farin ciki).

17. Ibrahim is (sad) today.
Ma'ana: Ibrahim ba ya (farin ciki) yau.

18. Nura (opens) the door.
Ma'ana: Nura (ya bude) kofar.

19. Muhammadu (closed) the door.
Ma'ana: Muhammadu (ya rufe) kofar.

Wadannan su ne antonyms da misalansu, sannan ku na iya rubuto ma na na ku misalan a wajen comment da ya ke can kasa. Za mu dakata a nan da fatan a na amfanuwa da darusan da mu ke rubutawa a shafin nan. Idan kuma akwai mai tambaya sai ya yi kasa wajen comment ya rubuta ta za mu amsa, idan Allah ya sa mun sani.

Domin ci gaba da samun darusan koyan turanci a ci gaba da kasancewa da shafin nan. Ku na iya gaiyato ma na 'yan uwa da abokan arziki zuwa shafin nan domin su ma su amfani. Mun gode, sai mun sake ganinku.

No comments

Powered by Blogger.