Menene conjunction?

Koyan nahawun turanci (English grammar) ya na bukatar sanin ka'idojinsa, ko dokokinsa kaman kowane. Daya daga cikin wadanda ka'idojin shine sassan magana (part of speech) wanda mu ka yi bayanin wasu daga cikinsu, kamansu noun, da pronoun, da verb, da preposition. Yanzu kuma za mu ci gaba da bayani akan conjunction, da amfaninsa a nahawun turanci.

Menene conjunction?

Conjunction wasu kalmomine da ake amfani da su domin hada kalma da kalma, ko kananin jumloli a tare. Wadanda kalmomin su ne and, da but, da when, da where, da who, da which, da while, da as, da since, da before, da after, da in order, da that, da so that, da unless, da until, da though, da although, da because, da nevertheless da makamantansu.

Misali:
1. Nura (and) Muhammad read the story.
Ma'ana: Nura (da) Muhammadu sun karanta labarin.

2. Katsina is a big city (but) lesser than Kano.
Ma'ana: Katsina babban birnine (amma) kasa da Kano.

3. They called Nura (while) he was absent.
Ma'ana: Sun kira Nura a lokacin da ba ya nan.

4. I know the boy (who) kicked the ball.
Ma'ana: Na san yaron (da) ya buga kwallon.

Ire-iren conjunction

Conjunction an rabasu gida biyu, kaman haka: Coordinating conjunction, da Subordinating conjunction.

1. Coordinating conjunction

Coordinating conjunction kalmomine da ake amfani da su domin hada kalmomi biyu, ko gajerun jumloli a jimla daya. Kalmomin da ake amfani da su su ne: and, da but, da or.

Misalan coordinating conjunction

5. Nura is a rich guy (but) Muhammad is richer than him.
Ma'ana: Nura matashine mai kudi (amma) Muhammadu ya fi shi kudi.

6. One should go between you (or) I.
Ma'ana: Tsakanin ni (da) kai dayane zai tafi.

7. Teacher (and) his students are working.
Ma'ana: Malami (da) dalibansa su na karatu.

2. Subordinating conjunction

Subordinating conjunction su ne kalmomin da ake amfani da su wajen hada gajerun jumla a cikin jumla daya. Wadanda kalmomin su ne: when, da where, da who, da which, da while, da as, da since, da before, da after, da in order, da that, da so that, da unless, da until, da though, da although, da because, da nevertheless da sauransu.

Misalan subordinating conjunction

8. I reached the market (when) it was rainy.
Ma'ana: Na karasa kasuwa (a lokacin da) ake ruwan sama.

9. I will not greet you (unless) you pay him.
Ma'ana: Ba zan gaisheka ba (har sai) ka biyashi kudinsa.

10. (Although) I am a small boy I can do the work.
Ma'ana: (Duk da cewa) ni karamin yarone zan iya yin aikin.

Wadannan su ne conjunction da misalansu, kuma ku na iya rubuta na ku misalan a wajen comment da ya ke can kasa. Idan kuma akwai mai tambaya sai shima sai ya je wajen comment ya rubuta ta za mu amsa, idan Allah ya sa mun sani.

Domin ci gaba da samun darusan koyan turanci a ci gaba da kasancewa da shafin nan. Ku na iya gaiyato ma na 'yan uwa da abokan arziki zuwa shafin nan domin su ma su amfani. Mun gode, sai mun sake ganinku.

2 comments:

Powered by Blogger.