Menene interjection?

Domin koyan nahawun turanci (English grammar) a na bukatar sanin dokokinsa kaman kowane yare a duniya. Daya daga cikin wadanda ka'idojin kuma ma fi shahara shine sassan magana (parts of speech) wadanda mu ka yi bayanin wasu daga cikinsu, kaman noun, da pronoun, da verb, da preposition, da conjunction. Sannan kuma a yanzu za mu ci gaba da bayani akan interjection, da amfaninsa wajen koyan nahawun turanci.

Menene interjection?

Interjection wasu kalmomine da ake amfani da su a cikin jimla domin a nuna damuwa, ko jin ciwo, ko jimami, ko murna ko farin ciki da makamantansu. Wadannan kalmomin yawancinsu ana kara exclamation mark wato alamun motsin rai (!) a karshensu.

Kalmomin da ake amfani da su a interjection su ne: Oh!, da Wow!, da Hurrah!, da Alas!, da Yes!, da sauransu.

Misalan interjection

1. (Oh!) I cut my palm!
Ma'ana: (Wayyo!) Na yanka tafin hannuna!.

2. (Yes!) That is what I like much!
Ma'ana: (Yauwa!) Daman irin wannan na ke so sosai.

3. (Wow!) What a delicious dinner!
Ma'ana: (Kaaai!) wannan wane irin abincin darene mai dadi!.

4. (Alas!) We fail in the match!
Ma'ana: (Kash!) ba mu yi nasara a wasan ba.

5. (Hurrah!) She has bought a Bugatti!
Ma'ana: (Tabarakallah!) ta siya motar zamani mai suna Bugatti.

Wajen da na yi amfani da Wayyo, ko Yauwa, ko Kaaai, ko Kash, da tabarakallah za ka iya amfani wasu kalmomin da ake amfani da su a yankinku wajen nuna fari, murna, damuwa, ko akasin su.

Wadannan su ne interjection da misalansu, kuma ku na iya rubuta na ku misalan a wajen comment da ya ke can kasa. Idan kuma akwai mai tambaya sai shima sai ya je wajen comment ya rubuta ta za mu amsa, idan Allah ya sa mun sani.

Domin ci gaba da samun darusan koyan turanci a ci gaba da kasancewa da shafin nan. Ku na iya gaiyato ma na 'yan uwa da abokan arziki zuwa shafin nan domin su ma su amfani. Mun gode, sai mun sake ganinku.

No comments

Powered by Blogger.