Mene ne preposition?

Ko daga jin sunan kalmar preposition ana iya fahimtar menene shi, ko kuma me ya ke nunawa a cikin jumla.

Misali:
1. Nura lives (in) Katsina.
Ma'ana: Nura ya na rayuwa (a) Katsina.

2. Students holding a meeting (at) hall.
Ma'ana: Dalibai su na taro (a) dakin taro.

3. Muhammad is sitting (on) a chair.
Ma'ana: Muhammadu ya na zaune (a kan) kujera.

Idan mu ka duba daga cikin misalai guda uku da mu ka kawo a sama za mu ga cewa da (in), da (at), da (on), su ne su ke nuna alakar da ke tsakanin aiyukan ko kuma sunaye da aiyukan da su ka gina jumlar, saboda haka su ne preposition.

Menene preposition?

Preposition ya na nufin manuni, kuma wasu kalmomine da su ke baiyana inda abu ya ke, ko su ke hada alakar suna da suna (noun), ko aiki da aiki (verb), ko kuma aiki da suna a cikin jimla.

Kalmomin da ake aiki da su a preposition su ne: on, da in, da at, da to, da under, da behind, da above, da below, da sauransu.

Misalan preposition

4. Pen on the book.
Ma'ana: Biro (a kan) littafi.

5. The man is walking under the bridge.
Ma'ana: Mutumin ya na tafiya (a karkashin) gada.

6. Boiled water in the bucket.
Ma'ana: Tafasashshen ruwa (a cikin) bokiti.

7. We study (at) government school.
Ma'ana: Mu na karatu (a) makarantar gwamnati.

Wannan shine bayanin preposition, tare da misalansa. Sannan ku ma ku na iya rubuta na ku misalan a wajen comment da ya ke can kasa. Idan kuma akwai mai tambaya shima sai ya je wajen comment ya rubuta ta za mu amsa, idan Allah ya sa mun sani.

Domin ci gaba da samun darusan koyan turanci a ci gaba da kasancewa da shafin nan. Ku na iya gaiyato ma na 'yan uwa da abokan arziki zuwa shafin nan domin su ma su amfani. Mun gode, sai mun sake ganinku.

1 comment:

  1. Muna godiya Allah saka da alkairi wannan page din yana da matukar amfani

    ReplyDelete

Powered by Blogger.