Menene simple present tense?

Bayan mun gama bayanin verb, mun yi misali lokutan aiki mabanbanta guda uku, wato present tense, da future tense, da kuma past tense. Kuma mun ce kowane daya daga cikinsu an kasashi gida hudu. Amma a wancan darasin mun yi bayanin tushe uku wadanda a cikinsu aka kirkiro sauran taran wanda ya sa adadinsu ya zama goma sha biyu.

Wadannan lokutan su ne simple present tense, da present continues tense, da present perfect tense, da present perfect continues tense. Sai past tense, da past perfect tense, da past perfect continues tense, sai kuma future tense, da future continues tense, da future perfect tense, da kuma future perfect continues.

To a cikin darasin nan za mu yi bayani game da simple present tense, sai kuma a cikin darusa na gaba ma su zuwa mu ci gaba da bayanin sauran tenses din.

1. Menene simple present tense?

Simple present tense ya na nufin aiki na al'ada, wato aiki na yau da gobe, a takaice ya na nufin aikin da ya ke maimaituwa lokaci lokaci. Kaman aikin da ake yi a kullum, ko kowace shekara, ko kowane wata, ko kowane sati, ko kowane second ko minti.

Simple present tense shine aikin da ya ke maimaituwa. Misali, kaman zuwa makaranta kullum, cin abinci ko shan ruwa, ko yin ibada a kullum ko duk karshen sati.

Ka'idojin amfani da simple present tense

1. Simple present tense ba saka helping verb (am, is, are) a cikinsa.

2. Kuma ba a kara (ing) a karshe kalma.

3. Sannan ana canza aiki daga daya zuwa mai yawa ta hanyar kara harufan s, ko es, ko kuma ies a karshen kalma, amma fa a sunan mutum daya banda (I), ko sunan abu guda daya ko kuma (he, she, it).

4. Amma a wakilan suna kaman you, da we, da they, da I, ko sunan mutane da yawa ana rubuta asalin kalmar ba tare da an canzata daga daya zuwa mai yawa ba.

5. Kuma daga karshen jimla ana amfani da wasu kalmomi da su ke yin karin haske game da lokacin da aikin ya ke faruwa. Wadansu daga cikin kalmomin su ne every day, da every week, da every month, da every year, da always, da sometimes, da anytime, da always, da daily, da weekly, da monthly, da yearly, da regularly, da occasionally, da often, da kuma rarely da sauransu.

Misali:

1. Nura (chats) on his phone every night.
Ma'ana: Nura ya (kan yi chatting) a wayarsa kowane dare.

2. Hafsa (goes) to school every day except weekend.
Ma'ana: Hafsa ta (kan je) makaranta kullum, banda karshen sati.

3. Muhammad (visits) Katsina every month.
Ma'ana: Muhammadu ya (kan ziyarci) Katsina kowane wata.

4. Policemen (raid) the house of the man regularly.
Ma'ana: Jami'an 'yan sanda su (kan farmaki) gidan mutumin kai-a-kai.

5. Real Madrid, Barcelona, Bayern Munich and Juventus (play) UEFA Champions League every year.
Ma'ana: Real Madrid, Barcelona, Bayern Munich da Juventus su (kan buga) gasar cin kofin zakarun turai kowace shekara.

6. The trap (catches) the targeted one always.
Ma'ana: Tarkon ya (kan kama) abun harinsa kullum.

7. Nigeria (holds) national election every four years.
Ma'ana: Kasar najeriya ta (kan yi zaben) kasa duk bayan shekaru hudu.

8. The train (stops) at the station rarely.
Ma'ana: Jirgin kasan ya (kan tsaya) a tasha ba ko da yaushe ba.

9. The farmer (farms) weed in the farm.
Ma'ana: Manomin ya (kan nome) ciyawa a gona.

10. We (brush) every day.
Ma'ana: Mu (kan wanke) bakin mu kullum.

Wannan shine verb da misalansa, sannan ku na iya rubuto na ku misalan a wajen comment da ya ke can kasa, domin wasu su gani su amfana.

Za mu dakata a nan da fatan a na amfanuwa da darusan da mu ke rubutawa a shafin nan. Idan kuma akwai mai tambaya sai ya yi kasa wajen comment ya rubuta ta za mu amsa, idan Allah ya sa mun sani.

Domin ci gaba da samun darusan koyan turanci a ci gaba da kasancewa da shafin nan. Ku na iya gaiyato ma na 'yan uwa da abokan arziki zuwa shafin nan domin su ma su amfani. Mun gode, sai mun sake ganinku.

No comments

Powered by Blogger.