Menene present continuous tense?

Bayan kammala bayanin sassan magana, mun gabatar da bayanin simple present tense, daya daga lokuta a nahawun turanci. Bayani na gaba shine wannan wanda za mu yi game da present continuous tense, wato wanda ya ke nuna cewa aikin yanzu ake yin sa, ko kuma dai aikin da ba a gama ba. Misali, Nura ya na rubuta posting a shafin arewanote yanzu haka, kenan kalmar yanzu haka ta kara nuna ma na cewa aikin yanzu haka Nura ya na kan aiwatar da shi.

Menene present continuous tense?

A darasin da ya gabata mun yi bayanin aikin da ake yi kullum ko kuma duk bayan wani lokaci. Present continuous dayane daga cikin tense na turanci wanda ya ke nuna cewa aikin da ake magana a kansa yanzu aikin ya ke tafiya. Kaman yanda mu ka bayar da misali a sama cewa Nura ya na rubuta posting a shafin arewanote yanzu haka. Wani misalin kuma shine kai da ka ke karanta wannan posting din yanzu haka shima present continuous tense ne, saboda yanzu ka ke karantawa.

Misali:

1. They are eating.
Ma'ana: Su na cin abinci.

2. Fatima is going to house.
Ma'ana: Fatima ta na tafiya gida.

3. Nura is listening tafseer right now.
Ma'ana: Nura ya na sauraron tafsiri yanzu haka.

4. The air is blowing.
Ma'ana: Iskar ta na kadawa.

5. You are reading this post now.
Ma'ana: Ku na karanta posting din nan yanzu haka .

Yanda ake aiki da present continuous tense

1. Karshen kalmar aiki a na kara (ing). Misali, kalmar (go) idan aka kara (ing), za ta koma (going).

2. (a) Waikilin sunan I a na rubuta am a tsakaninsa da aiki (verb), wato sai ya koma I am, ga wadanda su ka kware su kan cire harafin 'a', su rubutashi kaman haka I'm kuma duk ma'anarsu. Misali, I am playing, ko I'm playing.

(b) Wakilan sunan he, da she, da kuma it kuma a na rubuta is a tsakanin su da aikin. Kaman haka he is ko she is ko kuma it is, su din ma a na cire harafin 'i' a rubutasu kaman haka he's, ko she's ko kuma it's. Misali, he is writing, ko he's writing.

(c) Wakilan sunan you, da we, da they kuma are ake rubutawa a tsakaninsu da aiki, kaman haka we are, ko they are, ko you are. Sannan su din ma harafin 'a' din farkon are ake cirewa a bar re, sai a hada shi da wakilin suna we're ko they're ko you're. Misali, we are reading, ko we're reading.

Ga sauran misalan:

6. I'm going to school.
Ma'ana: Ina tafiya makaranta.

7. It's blazing.
Ma'ana: Wuta na tana ci.

8. You're typing on your phone.
Ma'ana: Kana rubutu a wayarka.

9. We're working in the house.
Ma'ana: Muna aiki a cikin gidan.

10. Nura and Muhammad are travelling to Kano.
Ma'ana: Muhammadu da Nura su na tafiya zuwa Kano.

Wannan shine bayanin present continuous tense, tare da misalansa. Sannan ku na iya rubuto mana na ku misalan a wajen comment da ya ke can kasa. Sannan kuma idan akwai mai tambaya sai ya yi kasa wajen comment ya rubuta za mu amsa, idan Allah ya sa mun sani.

Domin ci gaba da samun darusan koyan turanci kaman wannan sai a ci gaba da kasancewa da shafin nan. Kuma ku na iya gaiyato ma na 'yan uwa da abokan arziki zuwa shafin nan domin su ma su amfana. Mun gode, sai mun sake ganinku.

No comments

Powered by Blogger.