Menene present perfect tense?
Bayan kammala bayanin simple present tense, da present continuous tense za mu ci gaba da bayani akan present perfect tense wanda shine cikon na uku daga cikin rassan present tense guda uku na nahawun turanci. Idan ba ka karanta wadancan darusan ba ya na da kyau, ka koma ka duba.
Idan mu ka duba misalin cewa "Yanzu Nura ya gama yin rubutun nan" za mu ga cewa Nura ya gama yin rubutun nan yanzu ba da jimawa ba a wani fannin ana ce masa past tense, amma kasantuwar ya na da alaka da lokacin da ake ciki sai ya zama present perfect tense, wato aikin da aka gama yi yanzu, ba jimawa.
(b) Wakilan sunan mutum daya ko "he", ko "she", ko "it" ana amfani da "has" a tsakaninsu da aikin.
(c) Wakilan sunan "I" da "you" da "we" da "they" ana amfani da "have" a matsayin helping verb.
2. Kalmar aikin ana amfani da past perfect a maimakon past tense. Misali, ba a cewa "I have went", sai dai a ce "I have gone". Sai dai wasu kalmomin past tense din su da past perfect din su duk dayane, kaman "killed" da "killed", wasu kuma na su dabanne kaman "spoke" da "spoken".
Ma'ana: Na ziyarce su yanzun nan.
2. You have bought the phone.
Ma'ana: Kin siya wayar yanzu.
3. We have sold the food.
Ma'ana: Mun siyar da abincin.
4. He has left few minutes ago.
Ma'ana: Ya bar nan mintuna kadan da su ka wuce.
5. She has killed the snake.
Ma'ana: Ta kashe macijin.
6. The ball has hit the wall.
Ma'ana: Kwallon ta bugin bangon.
7. The team have won the trophy.
Ma'ana: Kungiyar ta yi nasarar lashe kofin gasar.
8. The ship has arrived the shore now.
Ma'ana: Jirgin ruwan ya iso bakin gaaba yanzun nan.
Wannan shine bayanin present perfect tense, kuma da misalansa. Sannan ku na iya rubuto mana na ku misalan a wajen comment da ya ke can kasa. Sannan kuma idan akwai mai tambaya sai ya yi kasa wajen comment ya rubuta za mu amsa, idan Allah ya sa mun sani.
Domin ci gaba da samun darusan koyan turanci kaman wannan sai a ci gaba da kasancewa da shafin nan. Kuma ku na iya gaiyato ma na 'yan uwa da abokan arziki zuwa shafin nan domin su ma su amfana. Mun gode, sai mun sake ganinku
Menene present perfect tense?
Present perfect tense ya na nuna cewa wannan aikin yanzu-yanzu a ka kammala shi. A wata fassarar kuma a na iya cewa aikine da aka kammala ya wuce amma ya na da alaka da yanzu. Misali, Yanzu Nura ya gama yin rubutun nan.Idan mu ka duba misalin cewa "Yanzu Nura ya gama yin rubutun nan" za mu ga cewa Nura ya gama yin rubutun nan yanzu ba da jimawa ba a wani fannin ana ce masa past tense, amma kasantuwar ya na da alaka da lokacin da ake ciki sai ya zama present perfect tense, wato aikin da aka gama yi yanzu, ba jimawa.
Ga yanda ake aiki da present perfect tense
1. (a) Tsakanin suna ko wakilin sunan mai yin aikin da kalmar aikin ana rubuta "has" ko "have". Idan mutum dayane ya yi wannan aikin ana amfani da "has", da kuma mutane biyune ko sama da haka su ka yi aikin ana amfani da "have" ne. Amma da "I" da "you" ko da mutum dayane ya yi aikin ba a rubuta "has" a tsakanin sunan sa da aikin sai dai a rubuta "have".(b) Wakilan sunan mutum daya ko "he", ko "she", ko "it" ana amfani da "has" a tsakaninsu da aikin.
(c) Wakilan sunan "I" da "you" da "we" da "they" ana amfani da "have" a matsayin helping verb.
2. Kalmar aikin ana amfani da past perfect a maimakon past tense. Misali, ba a cewa "I have went", sai dai a ce "I have gone". Sai dai wasu kalmomin past tense din su da past perfect din su duk dayane, kaman "killed" da "killed", wasu kuma na su dabanne kaman "spoke" da "spoken".
Misali:
1. I have visited them.Ma'ana: Na ziyarce su yanzun nan.
2. You have bought the phone.
Ma'ana: Kin siya wayar yanzu.
3. We have sold the food.
Ma'ana: Mun siyar da abincin.
4. He has left few minutes ago.
Ma'ana: Ya bar nan mintuna kadan da su ka wuce.
5. She has killed the snake.
Ma'ana: Ta kashe macijin.
6. The ball has hit the wall.
Ma'ana: Kwallon ta bugin bangon.
7. The team have won the trophy.
Ma'ana: Kungiyar ta yi nasarar lashe kofin gasar.
8. The ship has arrived the shore now.
Ma'ana: Jirgin ruwan ya iso bakin gaaba yanzun nan.
Wannan shine bayanin present perfect tense, kuma da misalansa. Sannan ku na iya rubuto mana na ku misalan a wajen comment da ya ke can kasa. Sannan kuma idan akwai mai tambaya sai ya yi kasa wajen comment ya rubuta za mu amsa, idan Allah ya sa mun sani.
Domin ci gaba da samun darusan koyan turanci kaman wannan sai a ci gaba da kasancewa da shafin nan. Kuma ku na iya gaiyato ma na 'yan uwa da abokan arziki zuwa shafin nan domin su ma su amfana. Mun gode, sai mun sake ganinku

Leave a Comment