Mu koyi lissafi (mathematics)

Kaman dai yanda mu ka yi bayani a bayanan gabatarwa, mun ce shafin nan shafine abokin mai karatu wato shafine na kimiyya da fasaha, shi ya sa mu ke ta kokarin kawo bayanai masu alaka da kimiyya ko fasahar zamani. Kaman yanda kowa ya sani ilimin lissafi, ilimine mai matukar mahimmaci ga dalibai, domin ya na da amfani sosai, wasu ma su ka ce shine tushen ilimin na'ura mai kwakwalwa (computer).

Ko da tarihin fasahar zamani ka duba za ka ga cewa wanda ya fara kirkiro computer, shine dan burtaniya (British) mai suna Charles Babbage a shekarar 1886. Kuma ya kirkirotane domin ayi amfani da ita wajen lissafi, wancan na'urar ana kiranta analytical machine. Ba wai nan kadai ba Apollo 11 wato kumbo na farko da ya fara sauka a duniyar wata (moon), kafin a aikashi duniyar wata sai da aka yi amfani da ilimin lissafi da na kimiyyar physics.

Isaac Newton da ya gano ka'idojin motsawa (laws of motion) ya yi amfani da lissafi wajen baiyanasu, da aikinsu. Hakama Galilei Galileo da ya gano kinematics ya yi amfani da lissafi wajen kawo wadannan formula guda uku ko biyar din nan a physics. James Clark Maxwell ya yi amfani da ilimin lissafi wajen tattaro ka'idojin tsohuwar physics ta electromagnetism wato Classical electromagnetism.

Ba a nan kadai ba, hatta yanda satellite su ke aiki an yi amfani da ilimin lissafi, domin GPS Satellite, da International space station, da Geostationary satellite, da kuma satellite na farko wato Sputnik 1 satellite da sauran satellite su na aiki bisa tsarin aiki da aka gano a lissafi da kimiyyar physics.

Gaskiyane, ilimin lissafi ya na da rikitarwa, da kuma wahalarwa musamman ga dalibai da kuma wadanda ba su san ka'idojinsa ba. Kowace darasi a lissafi ya na bukatar nutsuwa da kuma kiyaye dokoki, da ka'idoji, da sharudan da aka shimfida domin koyan wannan darasin. To da ikon Allah a shafin nan za mu kawo wasu ko kuma sanannun dokokin lissafin da mu ka sani.

Kawai kai dai ci gaba da kasancewa da shafin Arewanote. Sannan kai ma ka na iya bayar da gudunmuwarka ta hanyar gaiyato ma na 'yan uwa da abokan arziki zuwa shafin nan. Bayan wannan kuma ku na iya aikomana na ku bayanin da ku ke da shi wanda ku ke ga ya kamata a wallafashi, domin mabiya shafin nan su amfana.

Da ilimin lissafi ake amfani wajen lissafi a banki, da ilimin lissafi ake amfani wajen lissafin kwanan wata (date), da shekaru, da ilimin lissafi ake amfani wajen lissafo nisan dake tsakanin garuruwa (distance), da ilimin lissafi ake amfani wajen gano sauri ko gudun abun hawa (speed), da ilimin lissafi ake amfani wajen daura mutum akan adadin magungunan da zai sha idan ba shi da lafiya, da sauran su.

Za mu dakata a nan sai mun zo da darasi na gaba wanda a cikinsa za mu fara bayanin yanda ake lissafi daki-daki. Jawabin nan ya na matsayin gabatarwa game da amfanin ilimin lissafi ga rayuwar dan Adam ta yau da kullum. Kar a manta a ci gaba da kasancewa da shafin nan tare da gaiyato 'yan uwa da abokan arziki su zo, su amfana.

Mun gode, sai mun sake ganinku, a huta lafiya.

No comments

Powered by Blogger.